Yadda amarya zatayi a daren farko

Yadda amarya zatayi a daren farko

Jawabinmu na wannan rana, ya ta'allaƙa ne kacokan kan yadda amarya zatayi a daren farko musamman budurwa, da abinda ya kamata kiyi bayan ganin jini a daren farko.

Yadda amarya zatayi a daren farko

Wacece Amarya? Amarya ita ce wacce bata laifi koda kuwa ta kashe ɗan masu gida, kirarin nata kenan. Amarya dai ita ce macen da aka ɗaurawa aure aka kuma sha shagulgulan taron bikin ta kafin aka miƙa ta ɗakin mijinta ana taya ta da fatan alheri. A cikin wannan rubutun, idan kin kasance ɗaya daga cikin matan da take shirin zama amarya watau bi ma'ana taron bikin ki yana kan gaɓa, ko kuma an fara bikin ki ko kuma za'a saka ki a lalle, kai idan ma lissafin naki ya kasance da ɗan nisa watau kina cikin irin matan nan da aka kawowa kuɗin aure ne ko kuma an saka miki rana, to dukan ku wannan rubutun don ku aka yi shi, a saboda haka sai ku gazaryo ku bani aron hankulanku ku karanta ku fahimtu kuma kuyi amfani da abinda kuka karanta domin ƙaruwar ku. 

Wannan rubutun kacokan zai yi duba ne akan yadda amarya zata yi a daren farkon ta, sai dai kuma kafin nan ina kira ga amare ko masu shirin zama amare da cewa duk wani shirin da zaku yi, ba fa zai fara bane a wannan daren, idan har shirin ki zai fara ne a daren amarcin naki to tabbas ki rubuta ki ajiye, ni nace miki kin faɗi. Hausawa suna cewa ba a fafe gora ranar tafiya haka kuma bature yake cewa Rome wasn't build in day. Watau dai anan ana nufin ko wane mataki na rayuwa ba faraɗ ɗaya yake kasancewa ba, komai ana bin sa ne daki daki.

To kamar haka ne ga amarya ko kuma wacce ta ɗaura ɗamarar zama amarya. Shirin ki na amarcin daren farko a tsari ya kamata ya fara ne wata biyu ko ɗaya ko kuma satuttuka kafin a fara shagalin bikin ki. 

Menene ya kamace ki a wannan lokacin ? 

Ko ban fito ɓaro ɓaro na bayyana ba, ai amsar a bayyane take, ko kuwa ? 

To amma dai domin kauda kokwanto abin daya kamaci duk wata mace mai shiri ko niyya ko kuma ɗaura ɗamarar zama amarya shine gyaran jiki na amare. Shi kuwa wannan gyaran jikin da za kiyi zai fara ne dayi miki magungunan sanyi na mata ciki da waje domin ba sai na fito na faɗa ba, ba kuma sai na tsaya ɓata lokaci domin yin bayani anan ba, na irin illar da sanyi yake da ita a jikin mata musamman yara ƴan mata watau budurwoyi kenan. Idan kika je gyara kika yi sake kika ƙi maida hankali akan maganin sanyi, ki ka tsaya ana ta murje miki fata ana yi miki su alawa da dilka to wannan ki sani bafa dabara bace. Abu na farko shine maganin sanyi. Domin idan aka magance sanyin dake jikin ki to ki sani wannan shine jigon nasararki da kuma samun martabarki ta ƴa mace a wurin angon ki. 

Yana daga cikin illolin sanyi a jikin mace; ya hana mace juriya ko jin daɗin jima'i kai a taƙaice ma idan sanyi ya kama gabanki to zaki riƙa jin zafi da raɗaɗin azaba ne yayin da ango yake tarawa dake, idan kika kasa jurewa kuma, wanda dama baza ki jure ɗin ba, to ki sani shi fa ango ba uzuri zai yi miki ba, domin kuwa a wurinsa kin faɗi kuma wannan daren daya jima yana burin samun sa a tare dake kin kawo masa babban naƙasu. Saboda haka maganin kar a fara shine kar a soma. Yake mai shirin zama amarya, kafin gyaran jiki, maganin sanyi ya zama shine na farko a lissafin ki ko kuma agendar ki. Su waɗannan matan da zasu yi miki gyaran jikin nan na amarci sune dai waɗanda zasu yi miki amfani da magunguna daban daban na magance duk wani sanyi dake jikin ki ciki da waje, watau in and out kenan. Saboda haka gare ki kuma gare su. 

A cikin abubuwan da aka sani kuma ingantattu na maganin sanyi, misalin su sun haɗar da; man zaitun, tafarnuwa, zuma, albabunaj, bagaruwa, kanunfari, da wasu saiwoyin bishiyu da sauran ababen da ban ambata ba. 

Gareki amarya, bayan kin tabbatar da anyi miki gyara irin na kawar da sanyi daga jikin ki ciki da waje, daga nan kuma sai a bawa gyaran jiki himma, ayi miki gyaran jiki sadidan. Hausawa a wata faɗar su suna cewa; idan kana da kyau to ka ƙara da wanka,to haka yake a gurin ki amarya. Idan ya kasance ke ɗin irin waɗannan tsala tsalan ƴan matan ne masu shegen kyau, to fa kar ki sake kice ko kuma kiyi tunanin ai ni ina da kyau gyaran me zanyi. Da kin fara irin wannan tunanin to kiyi maza ki tuge shi daga cikin zuciyarki, domin idan kika bari irin wannan tunanin yayi miki tasiri to ina mai tabbatar miki sunan ki sorry. 

Ya kamata mata ku san wani abu; shi fa namiji da kuke gani, idan yana soyayya da yarinya yana kuma zuwa wurin ta zance to anan kyanta zai riƙa ruɗar sa har ma ya riƙa ganin babu wata mace data kama ƙafar ta a kyawu, to amma fa mafi akasari idan ya mallake ta ma'ana idan ya aure ta ta shigo yana ganin ta kullum to fa wannan kyan da yake gani ba zai kai na farkon nan da yake ruɗa shi ba, kuma dama wannan halayya ce ko ɗabi'a ta ɗan adam watau human being, sau tari bama daraja abin da muke dashi sosai mun fi hango abin da bamu dashi da idon buri, a saboda haka idan baka gyara sai ayi bake. 

Bayan amarya tayi amfani da magungunan sanyi ta kuma yi duka gyare gyaren da zata yi, to kuma akwai wasu muhimman abubuwa da zan lissafo sannan nayi fashin baƙi a kansu kamar haka;

-Cire kunya da tunani ko fassarar da ango zai miki 

-Shawarwarin ƙawaye da ƴanuwa

-Nazari dangane da koyon wasannin soyayya dana kwanciyar aure

-Cire kunya da tunani ko fassarar da ango zai miki 

Gare ki amarya, bayan an ƙalƙale miki jiki dasu dilka da alawa da su humra dangin ƙamshi da sauran ababen gyaran jiki dana ƙaro ni'ima kamar su gumba da zumar mata da irin kazar nan da akewa mata haɗi su riƙa ci har kuga idan ta zauna a wuri ta tashi tana yin naso saboda tsabar ni'ima lol.. To daga nan sai tunanin ki ya koma kan yadda zaki tafiyar da angon ki a daren ku na farko. Ina kira ga matan hausawa waɗanda tuni aka barsu a baya saboda rashin wayewa sakamakon gidadanci da suke yiwa kallon kunya. Yake bahaushiyar amarya ki sani, idan aka ce miki yau wannan mijinki ne to fa zancen kunya ya kare, eh, yes dole akwai irin nauyi da rashin sabo amma wannan bashi zai hana ki runtse ido ki farantawa sahibinki rai ba, matuƙar kina son ki bashi first impression mai kyau. 

Abu na biyu kuma bayan kunya da yake yiwa amaren hausawa naƙasu shine tsoron kar aga sun zaƙe a shimfiɗa, ango yayi musu kallon ƴan iska. To ki sani, ko da baki yi rawar kai a shimfiɗa ba, indai har zaki saki jikinki ki, ki kuma sakarwa angon ki ragamar ki to kuwa zaki faranta masa rai. Dole ne tilas idan har kina son daren ki na farko tare da ango ya zama abin kwatance to lallai sai kin sakar masa jiki ko ɗan yaya ne, kar ki barshi ki zama kamar gunki sai dai ya juya ki can ya juyo ki nan, misali kamar irin su sumba watau kiss da sauran wasannin soyayya idan mijinki yazo miki dasu kiyi ƙoƙari ki rika mayar da martani ko yaya ne, shi ɗa namiji yana son haka, kuma hakan zai gigita miki shi ya kuma taimaka miki ainun wurin kore tunanin wasu matan a zuciyar sa kamar yadda kike fata, idan kuwa haka ne to dole ne ki himma tu. 

-Shawarwarin kawaye da yanuwa 

Nasan da yawa yawan amare idan aka zo wannan gaɓar sukan riƙa jin tsoro da faɗuwar gaba wannan kam dole ne musamman ma ga amaryar da bata da buɗewar idanu, to amma kuma a yayin da amarya zata tsinci kanta a wannan halin na zulumi da fargabar daren farko, a ɗaya hannun kuma dole akwai ƙawaye na jikinta da sauran ƴan uwa da zasu riƙa bata shawara musamman akan abinda yake kusanto ta na keɓewa da ango watau daren farkon nan. Anan ina kira ga amarya lallai ta maida hankali ta ji, ta fahimtu, ta riƙe, ta kuma yi amfani da abinda ƙawaye da ƴan uwanta suke bata shawara a game da wannan daren domin nasan a irin wannan maganganun da shawarwarin da zasu bata, zasu fito mata ne a mutane su bayyana mata yadda abin yake ɓaro ɓaro saboda su ɗin ƙawaye ne da abokan wasa babu wani nauyi ko kunya a tsakanin su. Wannan aikin dama na ƙawaye ne da abokan wasa, iyayen ki da sauran manya sai dai suyi miki nasiha, faɗa da jan kunne akan haƙuri da biyayya da bin mijinki sau da ƙafa. 

-Nazari dangane da koyon wasannin soyayya dana kwanciyar aure

Domin kau da irin wannan matsalar ta rashin sanin yadda zaki yi idan ango yazo miki da wasanni na soyayya dole ne ki naƙalci bin shawarwarin ƙawaye da ƴan uwa kamar yadda na ambata miki a sama, haka kuma ki jiɓanci karatun articles dake ɗauke da bayanai kamar dai wannan da kika tsinci kanki kina mai karantawa a yanzu domin samun damar gane kalolin wasa irin na soyayya watau romance da salo salo na saduwa da kuma yadda zaki gyara kanki idan mai aukuwa ta auku, watau bayan ango yasha romon amarci kenan ko kuma nace bayan ango ya kai ga saduwa dake, domin kuwa ba kowane ango bane mai tarairaya da kuma ƙoƙarin gyara amaryarsa da kan sa bayan ya sadu da ita, duk da hakan abu ne mai kyau ace ango shi zai yiwa amaryarsa komai bayan ƙura ta lafa, to amma dole ki koyi yadda zaki yi idan har angon naki baya daga cikin jerin mazajen da suke ɗaukan amaryarsa cak "in a bridal style".. su shiga bayi da ita ba. 

Idan har amarya zata maida hankali tabi wannan taswirar ko nace blue print to tabbas abubuwa zasu zo mata da sauƙi kuma hakan zai taimaka mata matuƙa wurin tafiyar da rayuwar aurenta bayan wannan daren farkon.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post