Gajerun labaran ban dariya

Tatsuniya mai ban dariya musha dariya

Kunsan yan magana sunce taɓa kiɗi taɓa karatu, to yau idan mai duka ya yarje, mun kawo gajerun labaran ban dariya, tatsuniyar ban dariya daga littafin musha dariya.

Tatsuniya mai ban dariya musha dariya

LABARIN FARISA

Farisa ya kasance wani buzu mai rayuwa a daji, a rayuwar Farisa babu abinda yake so da ƙauna irin tocilan da rediyo. Farisa yana da wata tsohuwar tocilan daya gada a wurin kakansa sai dai kuma bashi da rediyo. Ana haka wata rana sai Farisa ya samu aikin gadi a birni. 

Koda Farisa ya karɓi albashinsa na farko daga wannan aikin gadin da yake yi sai ya bazama kasuwa ya sayo sabuwar rediyo ya dawo gida. Daga zuwan sa gida sai ya roƙi uwar ɗakin sa yace a taimaka a saka masa rediyon sa a cikin firinji, koda matar gidan taji haka sai tayi mamaki, sannan ta nisa tace;  to kai malam Farisa me zakayi da rediyo a cikin firinji?. Cike da murna Farisa yace;
Ai hajiya anjima zan sha KUL MUZIK! wai yana nufin zai sha cool music.

LABARIN ABU AMIR DA KYAKKYAWAR ƳAR SA

A cikin ƙarni na goma sha takwas anyi wani mutum mai suna Abu Amir. Abu Amir dai mutum ne mai tarin ilimi da kuma kaifin kwakwalwa wanda saboda tsabar kwanyarsa harta sarkin garin da manyan attajirai sun san dashi. Sai dai kuma babbar matsalar abu amir ita ce shi dai mutum ne mai tsananin muni sosai wanda a dalilin haka matan garin duka suka ƙi auren sa. Yana da muni sosai saboda gashi baƙi wuluk da ƙaton hanci da jajayen idanu. Da wannan matsalar ta ishi abu amir sai ya yanke shawarar cewa zai je can ƙauye ya samu wata kyakkyawar mace ya aura idan yaso duk lokacin data tashi haihuwa sai ta haifa masa ƴaƴa masu kyau. A cewar abu amir, ƴaƴansa zasu yi gadon kyawun matar da zai aura sannan kuma zasu yi gadon tarin ilimin sa. 

Da wannan shawarar abu amir yaje can ƙauye ya samo wata kyakkyawar mace fara tas ya auro amma kuma jahilace ta gaske babu karatu. Bayan wani lokaci sai ta samu ciki wanda hakan yasa abu amir farin ciki dan yasan matarsa zata haifa masa kyawawan yara kamar ta. Bayan wata tara sai matar abu amir ta haifi yarinya mace, sai dai kuma me? Wannan yarinyar da aka haifawa abu amir sai ya zamana tama fishi baƙi da munin fuska, a yayin data girma kuwa sai tama fi uwarta jahilci!.. 

LABARIN ZABO DA ZOMO

Wata rana da rana tsaka malam zabo yana cikin tafiya a hanyar sa ta komawa gida daga kasuwa tun daga nesa ya hango malam zomo yana tahowa. Koda suka zo kusa da juna sai malam zabo ya kalli malam zomo ya kuma kalli manyan dogwayen kunnuwan sa, sannan ya nisa yace; 

"Malam zomo nan kuka "kunno" kenan..? 

Ko da malam zomo yaji haka yasan malam zomo ba'a yake masa watau kunnowa da yayi amfani da ita yana nufi kunnuwan sa kenan. Sai mal zomo ya kaɗa kai ya kalli korar nan da take kan malam zabo sannan ya nisa yace;

"Malam  zabo kenan, ai "koran" nan ma, nan muka yo.. 

Koda malam zabo yaji martanin malam zomo shima sai ya fahimci lallai malam zomo yana nufin korar nan ta kansa kenan. Daga nan kowa ya kama gaban sa zuwa inda ya nufa.

MATI A KASUWA 

A ƙarni na goma sha takwas anyi wani bazazzagi mai suna MATI. 
Mati bai taɓa sanya ƙafa ya fita daga cikin garin Zaria ba a shekarun sa arba'in da takwas a duniya. Kwatsam wata ranar laraba, tabawa ranar sa'a kenan, sai wani razdan yace da maigari a haɗa masa maza majiya ƙarfi da zaije Kano dasu cin kasuwa. Ko da maigari ya saka yaransa akan a haɗo masa mazan da razdan zai tafi Kano dasu domin ɗebo masa kaya sai aka haɗa har da mati a wannan tafiyar kasancewarsa sungumemen ƙato majiyi ƙarfi. 

Tunda aka ɗauki hanya aka fara tafiya mati ya saki baki sai dalalar da yawu yake har aka zo babbar kasuwar kayan abinci a cikin garin kanon dabo. To mati dai a ƴar makarantar da yayi ta yaƙi da jahilci yasan wata kalmar turanci guda ɗaya rak wai ita 
''for''..  Saboda haka koda mati yaga a jikin buhunhuna ana rubuta 
"FOR SALE" sai abin yake bashi mamaki. A tunanin mati lallai haƙiƙa ko wanene wannan mutumin mai suna sale yana da arziki tunda duk buhunhunan kayan abincin dake wannan babbar kasuwar mallakin sale ne, kai hatta buhunhunan razdan da suka ɗauko aka jera a mota duka sale ne ya bashi. 

TILO ƊAN FULANI 

Tilo wani matashin bafulatani ne da baya samun ishasshen barci duk daren duniya a sakamakon cizon da sauro yake masa. Ana nan sai tilo wata rana ya shiga birni. A cikin birni bayan ya gama abinda ya kaishi yana shirin dawowa karkara a tashar mota sai yaga wata mata tana talla tana cewa azo a sayi gidan sauro. 

Koda tilo yaji haka sai ya garzaya wurin matar nan ya tambaye ta mai ake yi da gidan sauro, matar nan ta faɗawa tilo cewar idan ya ɗaura gidan sauro to shikenan ya huta da sauro da kuma cizon sa. Cikin farin ciki tilo ya saya gidan sauro ya hawo mota ya koma gida. Koda dare yayi sai tilo ya samu wuri ya ɗaura gidan sauro shi kuwa ya koma gefe yayi shimfiɗa ya kwanta, barci yayi gaba dashi. 

Can cikin baccin sai tilo yaji sauraye suna cizon sa, sai tilo yayi tsaki yace; haba saulo ga gidan ki can na ɗaura miki kinzo kina damuna.

WANENE ZAI SAKAWA KYANWA ƘARARRAWA? 

A cikin ƙarni na goma sha huɗu a wani gari da ake kira shuwarin anyi wasu al'umma ta ɓeraye masu yawa. Wannan al'umma ta ɓeraye tana da tsohon tarihi a wannan garin na shuwarin, al'ummarsu ta haɗa da kakannin kakannin su, kakannin su, iyayen su tare da ƴaƴa da jikokin su. Haka suka kafa daular su a wannan garin a can bayan garin, haka kuma suke shiga cikin wannan garin musamman idan dare yayi su riƙa damun mutanen garin nan da ɓarna da halin su na ɓeraye watau sata. Kuma idan ido na ganin ido ne wannan samari ko matasan ɓerayen cikinsu sukan haɗa zuga su shiga cikin garin suna sace sace saboda mutanen garin da dama a wannan lokacin sun tafi gona. 

A sakamakon irin wannan ɓarnar da al'ummar ɓerayen nan suke damun mutanen garin shuwarin da ita, sai ya zamana mutanen shuwarin sun shiga damuwa sosai saboda babu dama su ajiye wani kaya na amfani ba tare da ɓerayen nan sun sace ko sun lalata ba. Idan kaya ne na tufafi haka ɓerayen nan zasu yayyaga shi, idan kayan abinci ne haka ɓerayen nan zasu ci iya cinsu sannan su saci na sata domin kaiwa ƴan uwansu na bayan gari dake can sansaninsu. Kai a taƙaice duk wani abu da mutanen garin shuwarin zasu ajiye to fa ɓerayen garin nan zasu kai gare shi. Haka kuma ɓerayen da suke shigowa cikin garin nan na shuwarin suna da ɗan banzan yawa kuma sun san duk wata mafaka, gashi basa faɗawa tarko saboda suna da dabaru kala kala. 

Mutanen garin shuwarin a ƙoƙarin su na kawo ƙarshen matsalar ɓerayen nan da sace sacen da suke musu, sai suka haɗa taron gangami a fadar maigarin shuwarin domin dai asan hanya ko kuma hanyoyin da za'a bi a shawo ko kuma a kawo ƙarshen ɓerayen nan saboda kowa matsalar ta shafe shi a garin. Babu wanda ɓerayen nan basa yiwa ta'adi a cikin mutanen garin nan. Da aka zauna aka fara gabatar da taro kowa yana kawo irin nasa shawarwarin, wasu sunce tarkuna za'a haɗa a kuma naɗa su da yawa a cikin kowane gida dake garin sai dai kuma da yawa daga cikin mutanen garin ba suyi na'am da wannan shawarar ba, a cewar su ai an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa. 
A cewar mutanen garin ai an jima ana haɗa tarkuna a kuma naɗa su amma kuma cikin dare haka ɓerayen nan zasu shigo musu gidaje suyi ta'adi yadda suke so kuma su fita ba tare da ɓera ko da ɗaya bane ya samu shiga ɗaya daga cikin ɗaruruwan tarkunan da aka naɗa ba. Saboda haka dai gaskiya azo da wata shawarar. 

Ganin cewa mafi yawa ko rinjaye na mutane basu amince da maganar kafa tarkuna ba, sai mai gari yace a sake kawo wata shawarar. Jin haka ne yasa wasu fusatattun manoma waɗanda ɓerayen nan suka shigar musu rumbun su kuma suka yi musu mugun ta'adi kusan mako ɗaya daya gabata suka kawo shawarar ai kawai a tafi bayan gari a nemi sansanin ɓerayen nan a kona su gaba ɗaya. Mutanen gari da suka sake jin haka sai suka ce ai ko anje ba za'a taɓa samun su ba saboda suna da ramuka da yawa a saboda haka suna da hanyoyi da yawa da zasu ɓulle, a yayin da duk aka nemi kai musu farmaƙi. Koda mai gari yaga wannan shawarar ma ba'a karɓe ta ba, sai ya kalli taron jama'ar nan yace; ko da akwai wani mai shawara? 

Daga can baya wani tsohon mutum tukuf mai farin gemu ne ya tashi yace yana da shawara, koda mai gari ya tambaye shi mecece shawarar sa, sai wannan dattijon mutumin yace kyanwa za'a samo a sake ta a bayan gari kusa da sansanin ɓerayen nan, sannan kuma a samu wanda zasu riƙa kai mata abinci can inda take. 
A cewar wannan dattijon indai ɓera ɗaya ya fito yaga kyanwar nan to shikenan sun dena fitowa daga ramukan nan nasu sai dai yunwa ta kashe su a ciki. Jin wannan shawarar ta dattijon nan sai mutanen garin aka ɗau sowa ana murna aka kuma yi na'am da shawarar tasa. Daga nan kuma mai gari yasa aka tashi aka tafi wani garin aka samo wata ƙatuwar kyanwa aka zo aka sake ta a bayan garin nan inda ɓerayen nan suke. 

Koda ɓerayen nan suka ga kyanwa sai suka dena fitowa gaba ɗaya kuma ga yunwa tana addabar su domin wasu ɓerayen har sun fara mutuwa. Wannan ne ya tashi hankalin al'ummar ɓerayen nan sosai har suka haɗa taro domin asan yadda za'a yi da kyanwar nan da ta hana su fitowa. Wani tsohon ɓera ne ya kawo shawarar cewa a samu ƙararrawa a saka a wuyan kyanwar nan yayin da take bacci idan yaso duk lokacin da zasu fita idan kyanwar tayi motsi zasu ji, za kuma su gane inda take domin guje mata. Da jin wannan shawarar sai taron ɓerayen nan ya ɓarke da murna aka shiga kaɗe kaɗe da bushe bushe na murnar samun nasara tunda dai sunyi maganin matsalar kyanwar nan. Ana tsaka da wannan murnar ne sai shugaban ɓeraye yaga wannan tsohon ɓeran mai yawan hazaƙa da hangen nesa baya murna, saboda haka yace a dakata, sai kowa yayi shiru akayi tsit. Sai shugaban ɓeraye ya tambayi wannan dattijon ɓeran mai yasa baya murna? 

Dattijon ɓeran nan sai daya kalli taron ɓerayen nan ƴan uwansa ɗaya bayan ɗaya sannan ya nisa yace; 
A CIKIN WANNAN TARON WANENE ZAI JE YA SAKAWA KYANWA ƘARARRAWA A YAYIN DA TAKE BACCI..? 

Daga wannan tambayar ne wannan babban taron ya tashi ba tare da an samu amsar tambayar ba.

{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post