Gyaran fuska da manja da haske

Gyaran fuska

Barka hajiya da shigowa wannan gida managarki ta kowane fanni, yau zanyi rubutu ne dangane da gyaran fuska da manja gamida bayanin gyaran fuska da kurkur, ban tsaya nan ba akwai jawabin yadda ake gyaran fuska da zuma ko da tumatir harma da gyaran fuska da kwai.

Gyaran fuska da manja,zuma,kurkur, tumatir,kwai

Yaku nisa'u yaku mataye,  ina kira gareku da jan hankali a game da gyaran fuska wanda ya wajaba a gare ku. Fuskarku duk da ta kasance ba ita ce mafi martabar abinda kuka mallaka a jikinku ba, amma dai akwai wani abu da bature yake kira 'first impression'. Wani namijin fa kallon fuskarki kawai zai yi daga nan kuma sai labari domin kin gama tafiya dashi, to amma kuma idan fuskar taki bata samun gyara fa ? Idan fuskar taki bata samun kulawa fa ? Matuƙar ba zaki tsaya ki bawa fuskarki lokacin ki ba, matuƙar ba zaki jiɓanci gyaran fuskar ki da kula da ita ba to fa ba zaki samu yadda kike so ba a duk lokacin da kikai duba izuwa mirror watau madubi. 

Akwai matsalolin da suka shafi fuska, irin matsaloli na yau da kullum kamar irin su pimples watau ƙurajen fuska, da sun burn da oily face watau fuska mai maiƙo. Waɗannan duka matsaloli ne waɗanda suke natural ma'ana sun samu ne natural waɗanda dama can akwai su a rayuwa. To banda su kuma akwai matsaloli waɗanda mu da kanmu muke janyowa kanmu su, ire iren matsalolin nan sun haɗa da amfani da mayuka waɗanda basu dace da fuskar mu ba. Ba wai ina maganar mayukan bleaching bane. 

A wannan jawabin nawa ba'a ma kai nan ba. Shi bleaching yama fi ƙarfin na kira shi da matsala domin kuwa shi ganganci ne saboda duk mai yin bleaching ai tasan cewa akwai adverse effects da zasu biyo bayan daɗewa da za tayi tana amfani da mayukan bleaching amma a hakan zaku ga masu yi sun cigaba da amfani da irin waɗannan mayukan. To koma dai wane irin matsalolin fuska kike fama dasu wannan rubutun zai yi bayani a taƙaice kan matsalar ƙurajen fuska watau pimples da sauran matsaloli kafin mu garzaya kan gyaran ita kanta fuskar.

Kurajen fuska;

Kasancewar ƙuraje daga cikin ababe masu ɓata fuska, ya sa yake da kyau mu riƙa kula da fatar fuskarmu.
Daga cikin abubuwan dake janyo ƙurajen fuska sun haɗar da:
yawan cin abu mai maiƙo kamar butter watau blue band ko cin gyaɗa, da amfani da mayukan da basu dace da fatar fuskar ba, kwayoyin cuta watau germs da kuma shiga rana sosai, da aiki a cikin zafi.

Sau tari mutane da dama su kan kashe kuɗaɗen su suyi ta sayen creams da sauran magunguna da fatan zasu magance musu ƙurajen fuskar su amma zaku ga abu ne mawuyaci a samu biyan buƙata. 

Ana iya magance ƙurajen fuska ta waɗannan hanyoyin da zan yi bayani
anan gaba kaɗan.

Ga mata masu fama da baƙin fuska watau dark marks ko kuma irin na gefen fuskar nan to irin wannan cikin biyu ɗaya ne, ko dai ana shafa cream ana shiga rana ko ana shafawa lokacin da ake zafi ko kuma shafawa a shiga aikin abinci ko kuma a shafa man da yayiwa fatarki ƙarfi.

Yadda za'a magance wannan tabon za a samu madara ta ruwa sai a sata a fridge ta yi sanyi so sai sai a goga a wannan tabon dake fuskar ya yi kamar minti ashirin ko fiye da haka sai  ki wanke. Sannan idan gari da zafi sai a samu ruwan sanyi a samu yar audiga a tsoma a ruwan sanyi sai a ɗora a kan tabon sai a barshi ya yi kamar minti biyar haka sai a cire audugar a shafa mai idan aka yi wannan kamar sau uku haka za'a fara ganin canji. 

Yadda ake gyaran fuska da manja:

Manja watau palm oil, man da ake samar dashi daga kwakwar manja dankare yake da sinadaran da suke tallafawa fatar jikin ɗan adam. Shi yasa sau tari zaku ga idan mutum yana borin jini ko kuma yana jin ƙaiƙayin jiki akan shafa manja a fatar jikin. Kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci zaku ga an samu relief. Hakan yana samuwa ne saboda akwai sinadaran da suke kwantarwa haɗe da buɗe jijiyoyin jinin jikinmu a maimakon takurewa da suke yi. Watau abin da ake kira vasodilation kenan a ɓangaren harkar lafiya. Domin haka manja yana taka muhimmiyar rawa wurin gyaran fatar jiki in general bama ta fuska ba. 

Bugu da ƙari, baya ga ɓoye shekaru da hana tsufa da manja ke yi, yana tausasa fatar jikin ɗan adam yana kuma cire maiƙon jikinsa. Hakan yasa ake ake amfani da shi wurin yin sabulai da mayuka. Man ja na magance ƙaiƙayin jiki kuma kamar yadda nayi bayani a sama. 

Idan aka samu manja mai kyau wanda ba ayi wa mix da gasara ba, sai a jiɓanci shafa shi a fuska da sassafe sai kuma da dare. A duk lokacin da aka shafa shi sai a barshi na tsawon minti talatin zuwa awa ɗaya, indai ana yin wannan to za'a ga canji na ban mamaki. 

Yadda ake gyaran fuska da kurkur:

Kurkum na ɗauke da sinadarai da dama kamar su vitamin b6 da vitamin c da sauransu. Haka kuma yana rike fata da kara mata inganci. Gyaran fuska da kurkum yana ƙarawa fuska laushi, santsi da kuma haske. 

Za'a samu garin kurkum da zuma a kwaɓa a kuma haɗa da ruwan lemon tsami a kwaɓa sosai. Wannan kwaɓin za'a rika shafawa a fuska kamar na tsawon mintuna goma sha biyar sannan a wanke da ruwan dumi. Za'a iya yin wannan sau ɗaya ko biyu a sati. Amfani da wannan haɗin ya kan hana fesowar ƙuraje haka kuma yana saka laushi da santsi da kuma hasken fata. 

Yadda ake gyaran fuska da zuma: 

Za'a samu zuma mai kyau a goga da auduga a fuska, a bar ta zuwa wasu mintuna sai a wanke. Za'a iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen su fita.

Yadda ake gyaran fuska da tumatir:

Za'a samu tumatir da kokuma a niƙa sai a tace a saka a firij ya yi ƙanƙara sai a ringa shafa kankarar a kan tabon kullum. Hikimar anan ita ce koda ƙanƙarar ta ruwa ce zalla zata taimaka wurin sakar da fuska saboda ita fatar fuskar mutum sam bata son abu mai zafi ko kuma abu mai ƙarfi.

Baƙin tabo a fata yawanci yana samuwa ne daga kuraje da pimples.  Tumatir idan aka jibanci goge fuska da shi yana iya taimakawa wajen kawar da su.

A haɗa ruwan tumatir cokali biyu da sukari cokali ɗaya sai a shafa a fuska na tsawon mintuna 25-30.  Bayan haka, a yi amfani da ruwa mai ɗan ɗumi don ɗauraye shi.

Idan fatar jikin ku na da ƙuraje, za ku jiɓanci shafa tumatur yau da kullum   Tumatir ya ƙunshi sinadaran vit A, C da K waɗanda ke taimakawa fata don kiyaye matakin PH na yau da kullun kuma yana haifar da tsabta mai zurfi ga fata.

Za'a iya haɗa ruwan tumatir tare da ganyen na'a na'a watau mint ko man itacen shayi.  A riƙa shafawa a fuska sau biyu ko uku a sati. 

Yana hana yamutsewar fata wato wrinkles. Haka kuma tumatir yana taimakawa wajan samar da sinadarin collagen tare da samar da sinadarin furotin (protein) wanda ke ba wa fatar fuska ƙarin inganci da tsari mai kyau.

Ga kuma wata hanyar:

A samu cokali biyu na ruwan tumatir tare da Multani mitti don samun kyakkyawan sakamakon da ake so.

Wannan haɗin yana hana fata mai maiko wato oily skin. 
Idan fatar fuska tana saurin yin  maiko to amfani da tumatir a fuskarkar yana taimakawa kwarai da gaske. Hakan yana faruwa ne saboda tumatur yana taimakawa wajen kiyaye matakin PH na fata da kuma samar da ruwa.

Yadda ake amfani da;

A haɗa ruwan tumatir tare da aloe vera don samun cikakken sakamakon da ake so.

Yana kare fata daga ƙunar rana wato sun burn. Zafin rana na iya yin illa ga fata, sau da yawa takan yi duhu da kuma cire mata abubuwan gina ta.

Ga wata hanyar:

A haɗa ruwan tumatir da butter ko madara.  A shafa a fuska na tsawon mintuna 15, sannan a wanke da ruwan ɗumi.

A lura cewa bai kamata a yi amfani da wannan haɗin a kowace rana ba saboda yana iya haifar da saluɓewar fata.  Sau ɗaya ko sau biyu a sati ma ya wadatar.

Yadda ake gyaran fuska da kwai:

Babban abinda ke maganin ƙurajen fuska kamar kwai. 
Ƙurajen fuska ko pimples a turance
wasu ƙuraje ne da suka fi fitowa a fuska musamman idan ana amfani da mayuka iri-iri ba tare da kula da man da ya dace da fatar fuskar ba.
Matsalar ƙurajen fuska tafi shafar mata musamman matasa. Da yake mata sun fi maza yin shafe shafe kuma ban da haka, a bisa tsarin halittar jiki ma, mata sunfi maza samun ƙurajen fuska. Maza ma suna samun irin matsalar sai dai bata kai ta mata ba. 

Da farko dai za'a samu kwai a fasa kwan a cire kwanduwar watau egg yolk. Daga nan sai a kaɗa farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa. A shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan ƙurajen. A rufe fuskar musamman daga kan hanci har zuwa kumatu da ƴar ’tissue paper’.
Idan ya bushe sai a wanke fuskar.
Sannan sai a shafa kwanduwar a kwan a fuska na tsawon mintuna goma sha biyar. Sai a wanke fuskar.

Amfani wannan hanyar dana misalta a sama yana kashe ƙurajen fuska ya kuma bada kariya daga ƙuraje.

Yana ƙara hasken fuska
Yana rage maiƙon fuska

Ga wata hanyar kuma;

Za'a samu kwanukan sha guda biyu, ɗaya za'a zuba ruwan kwai bayan an cire kwanduwar ɗaya kuma za'a zuba ruwan zafi. A kaɗa farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa, daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma kan ƙurajen, sai a samu ’tissue’ kaɗan a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu, kada a yi magana sosai bayan an gama manna ’tissue’ domin yin hakan zai iya buɗe fuskar, wannan zai iya ɓata aikin da aka yi domin ana sanya tissue ɗin ne don ta matse fuskar. 

Bayan haɗin ya bushe, sai a wanke fuskar, sannan sai a shafa kwanduwar a fuskar har kamar tsawon minti sha biyar sannan a wanke. A nan za a ga abin mamaki, a jarraba a ga banbanci domin wannan ba ƙaramin maganin gyaran fuska bane da kuma matsalar ƙuraje.  Wannan haɗin yana kawar da baƙin tabo wato black head. 

{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post