Yadda ake gwajin ciki da gishiri

Yadda ake gwajin ciki da gishiri:

Yau kuma ga wata sabuwa domin mata, wato yadda ake gwajin ciki da gishiri, munyi bincike domin samo gaskiyar batu na yadda ake gwajin ciki ta amfani da gishiri. Kuma ga abinda muka samu.

Yadda ake gwajin ciki da gishiri

A cikin wannan rubutun zanyi cikakken bayani kan yadda ake gwajin samfuri watau sample na fitsarin mai ciki watau juna biyu ko kuma wacce ake zargi ko tsammanin akwai juna biyun watau ciki a tattare da ita. Rubutun zaiyi bayani daki daki kan yadda za'a gabatar da wannan gwajin tare da haka kuma, wannan rubutun zai yi bayani akan ingancin wannan gwajin da kuma matsayin sa a wurin masana da kuma manazarta. A tare da haka, duka dai idan makaranta suna tare dani zamu yi duba zuwa ga wasu hanyoyin gwaje gwaje da kuma abinda ake gani a cikin samfurin fitsarin mai juna biyu har akai ga yanke hukuncin cewa tana da juna biyun ko bata da shi. 

Gwajin ciki watau juna biyu wani abu ne da aka jima ana yi a yayin da ake tsammanin mace tana da shigar ciki a jikinta. Sau tari idan mutane suka ji an ambaci kalmar gwajin ciki to mafi akasari tunanin su yana tafiya ga asibiti ne, wanda kuma shi gwajin ciki ba lallai sai a asibiti kaɗai ake iya yin sa ba. Akwai hanyoyi da yawa da ake bi wajen yin gwajin ciki watau juna biyu ba tare da an dangana da asibiti ba. Daga cikin irin waɗannan hanyoyin akwai gwaji da gishiri. Gwajin ciki da gishiri hanya ce wacce ake yin gwajin juna biyu a gargajiyan ce kuma ba tare da ɓata lokaci ba. 

Ga takamaiman yadda ake gwajin ciki da gishiri (Juna biyu):

Da farko dai za'a fara tanadar kwano ko kuma nace kwanuka guda biyu masu tsafta sai ƙaramin cokali watau tea spoon suma guda biyu. Idan aka samu waɗannan kwanuka guda biyu za'a zuba sample na fitsarin mai cikin nan a kwano ɗaya, ɗayan kwanon kuma wani fitsarin daban wanda ba nata ba. Daga nan sai a samu gishiri ƙaramin cokali guda biyu duk a zuba a cikin kwanukan fitsarin nan guda biyu. Bayan an zuba ƙaramin cokali gishiri biyu a cikin kwanukan fitsarin nan sai a jira na wasu mintuna ba masu yawa ba. 

Bayan wasu mintuna kaɗan za'a iya duba cikin kwanukan fitsarin nan guda biyu domin lura da irin canje canjen da aka samu. Idan aka ga fitsarin matar da ake tsammanin tana da juna biyu watau ciki, yayi kala kamar kalolin gajimare watau rainbow to wannan matar tana ɗauke da juna biyu, illa iyaka dai baza a iya cewa ga iya tsawon satittika ko watannin cikin nata ba kamar yadda likita yake bayyanawa. Ɗayan kwanon kuwa za'a ga babu wani canji a cikinsa duk kuwa da cewar an zuba masa gishiri kamar yadda aka zubawa na mai cikin nan. Wanda hakan ne yake tabbatar da cewar akwai ciki a jikinta. Kar a manta cewa idan za'a yi wannan gwajin to mafi kyautuwa shine ayi shi da safe. 

Yadda ake yin gwajin chlorine da fitsari:

Za'a ɗauki sample watau samfurin fitsari a zuba a cikin kofi ko wata container haka. Daga nana kuma sai a mayar da samfurin fitsarin cikin kananan kofuna biyu masu ɗauke da sinadarin bleach watau bleaching agent. Za'a bar wannan haɗin watau mixture na sample ɗin fitsari da kuma bleach na tsawon mintuna a ƙalla talatin. Bayan nan kuma sai a samu 30 ml watau mil talatin kenan na hodar chlorine watau ma'ana chlorine powder a saka a cikin kofin. 

Bayan an gama duka wannan za'a rufe kofin a sake bashi tsawon mintuna sha biyar zuwa ashirin watau fifteen to twenty minutes kenan. Sannan sai a buɗe domin duba sakamako. 

Wannan hanyar ta gwajin samfurin fitsarin mai juna biyu da chlorine ta samu shaidar inganci da kaso saba'in cikin ɗari watau 70% out of 100 kenan. Ita ma kuma dai wannan hanyar bata da wata kwakkwarar shaida a wurin manazarta ko masana ilimin kimiyya na amfanin ta wurin gwajin ciki, sai dai kuma duk da haka mutane da dama suna amfani da ita sosai har ila yau domin tabbatar da ciki a jikin mace. 

Menene siffar fitsarin mai ciki? 

Kamar dai yadda fitsari yake ko kuma yadda aka san kalar fitsari watau kalar rawaya kuma mai haske, watau mai ɗauke da sinadarin alkaline ba tare da wani canji ba, haka kalar fitsarin mai ciki yake watau juna biyu. 

Ta yaya za a iya canza siffar fitsari mai ciki da gishiri?

Ƙarin gishiri a cikin fitsarin mai ciki wata hanya ce da mutane da dama suke yinta na tsawon lokaci, ma'ana an jima ana amfani da ita domin gano ko akwai ciki a jikin mace. Koda yake babu wata kwakkwarar hujja ko kuma shaida a kimiyance ta cewa ana gane ko kuma shaida tabbatuwar ciki ta hanyar gwajin fitsari da gishiri amma dai mutane sun jima suna yi haka kuma suna samun sakamakon da suke bukƙatar samu. Kamar yadda aka bayyana siffar fitsarin mai ciki a sama watau kalar sifar yadda kowane fitsari yake kenan kalar rawaya. To idan fitsarin na mai ciki ne, ƙarin gishiri ko da rabin karamin cokali ne watau tea spoon zai sa wannan kalar rawayar ta baje ya dawo clear ko kuma ya haɗa gajimare watau rainbow. Waɗannan sune observation ɗin da ake samu na canje canje a fitsarin wacce ake tsammanin akwai ciki a jikinta. Canji na uku wanda shi ba'a cika samu ba shine bayan wasu mintuna da ƙarin gishiri a cikin fitsarin za'a ga fitsarin yana takurewa watau abinda a kimiyance da kuma turanci ake kira da precipitation. 

Wace Hanya Ce Mafi Sauri Don Gano Juna Biyu? 

Gwajin Ciki wanda ake gudanarwa a gida shine hanya mafi sauri don gano juna biyu. Za'a sanya sample watau samfuri kenan na fitsari a jikin gwajin daga nan sai a jira wasu ƴan mintuna don samun ko kuma ganin sakamakon. Shi dai wannan abin gwajin a cikin kantin magani ko pharmacy ake samun sa watau inda ake siyarwa. A irin wannan gwajin da ake gudanarwa akwai sakamakon mai kyau wanda ba'a samun kuskure a cikinsa. Sakamakon gwajin fitsarin mai juna biyu yana bayyana kasancewar sinadaran hormone ne idan har akwai juna biyun da ake son tabbatarwa. 

Gwajin jini domin tabbatar da sinadaran hormone irin na masu juna biyu: 

Shi dai wannan hanyar gwajin a cikinsa ana daukar samfurin jinin mace ne wanda da shine za'a gabatar da bincike a ciki lab watau ɗakin gwaje gwaje ko bincike kenan a kimiyance. A cikin wannan gwajin da za'a yi ne za'a duba kasantuwar sinadaran hormonal na estrogen da progestereone da kuma adadin su a cikin samfurin jinin domin tabbatar da kasantuwar juna biyu. 

Scanning ɗin mahaifa domin neman ɗan tayi. 

A wannan hanyar kuma ana ɗaukan hoton mahaifa ne watau scanning domin gano foetus watau ɗan tayi. Wannan hanyar ta tabbatar da cikin tana daga cikin hanyoyi mafiya inganci da har yanzu ake amfani dasu a fagen kimiyya da fasaha. 

Danganawa da asibiti. 

Kai ziyara zuwa asibiti domin ganawa da likita tabbatacciyar hanya ce wacce take tattare dabin hanyoyi da suka dace musamman idan ciki watau juna biyu yazo tare da matsaloli watau complications a tare da uwar watau mai cikin ko juna biyun ko kuma shi kansa cikin da yake jikinta. A wannan hanyar ta danganawa da likita, a cikinta ake samun shawarwari dangane da duk matsalolin da zasu iya tasowa da kuma shawarwari da duk dokokin da mace mai ciki ya kamata tabi domin kula da lafiyar abin dake cikinta. 

A dai dai wane lokaci ne alamun ciki suke iya bayyana a cikin fitsari. 

Idan sinadaran juna biyu suka bayyana a cikin fitsari

Da zarar an samu kyankyasar kwai a mahaifa watau ma'ana idan maniyyin namiji ya haɗu da kwan mace kenan, to daga wannan haɗuwar ne sinadarin ciki mai suna beta HCG zai bayyana kansa a cikin jini da kuma fitsarin mai juna biyu. Shi dai wannan sinadarin na beta HCG yana bayyana kansa ne da wuri a cikin samfurin jini da fitsarin mace mai juna biyu akalla cikin kwanaki goman farko na samuwar ciki. 

Haka kuma a yayin da sinadaran juna biyu watau estrogen da progestereone suka bayyana a cikin jini da fitsarin mace watau ma'ana idan aka yi gwajin asibiti aka gansu to babu makawa mace na dauke da juna biyu. 

Waɗanne alamomi ke nuna akwai yiwuwar ciki kafin akai ga yin gwajin ciki koda gwajin na gida ne ? 

Ɓatan wata ko kuma ɗaukewar jinin al'adar mace. 

Ita dai wannan hanyar an tabbatar da ita a matsayin al'amar farko wacce idan ta faru watau idan a lissafin mace na zuwan jinini al'adar ta yayi amma kuma jinin bai zo ba, to tun anan ake ɗaura alamun tambaya da tsammanin tana dauke da juna biyu. 

Zubar jini ko ɗigar jini

Wannan ma dai wata hanya mai nuna alamun yiwuwar shigar ciki a jikin mace a yayin data lura da zubar jini mai yawa daga farjin ta ko kuma digar sa a lokacin daya kamata ace jinin al'adar ta yazo. Shi dai wannan jinin da zai riƙa ɗiga ko zuba yana da haske a launinsa domin bai cika duhu ba. 

Kumburin ciki

Wasu matan da zarar sun samu juna biyu watau shigar ciki to sam ba'a ɗaukan lokaci cikin nasu yake fara dagawa yana girma. A sakamakon saurin girman da cikin nasu zaiyi hakan zai zama wata alama da za'a iya gane a gane cewar suna da ciki. 

Sauri ko kuma yawan gajiya

Idan ya zamana mace tana saurin gajiya ko ku ma jin kasala kuma ba tare da tayi aikin komai ba, shima wani abin dubawa ne ko kuma alamar kasantuwar juna biyu a jikinta. Akwai yawan jin juwa ko jiri watau dizziness a tattare da mace idan tana jin wannan kasalar ko kuma gajiyar. Haka kuma mace zata riƙa jin tashin zuciya watau kumallo ko amai duk dai a cikin alamun juna biyu dake tattare da ita a, wannan lokacin. 

Yaushe ne ake samun kuskure a cikin gwajin ciki na gida? 

Idan akayi gwajin ciki da wuri

Gudanar da gwajin ciki watau juna biyu a fitsarin mace cikin gaggawa ba tare da wasu daga cikin alamomin da na gama bayyanawa a sama ba sun nuna kansu hakan kuskure ne, kuma a dalilin haka ne ba za'a samu irin sakamakon da ake so ba. Idan har ana son samun cikakken sakamako koda ace bayan alamomi sun nuna kansu ne, to bayan gwajin da za'a yi na cikin gida akwai bukatar a dangana da asibiti domin a sadu da likita bokan turai!


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post