Shigar ciki na sati daya

Shigar ciki a satin farko

Kowace mace akwai haƙƙin sanin alamomi na shigar ciki na sati daya a jikinta ko alamomin cikin sati daya. Yana da kyau hakan kuma yana da muhimmanci mace ta san irin alamomin da idan ta gansu zata iya farga ta kuma yi zargi ko tunanin ciki ya shige ta ba don komai ba kuwa sai don kula da lafiyar ta da kuma abin da yake cikin nata. 

Shigar ciki na sati daya

Samuwar ciki a jikin mace ba ƙaramin al'amari bane sannan kuma ba abu bane wanda za'a yi wasarere dashi aƙi bashi muhimmanci da duk wata kulawa data dace saboda ko ba komai wannan cikin na jikin mace shine tushen rayuwa. Kowa da kowa a cikin mu ta wannan hanyar aka samar dashi watau tsakanin jinsin mace da namiji bayan an sadu mace ta ɗauki ciki ta rene shi wata tara kafin ta haife shi kuma, saboda haka duba da irin tarin ɗawainiyar da take ƙunshe da wannan babban al'amari ya kamata ace kowace mace tasan alamomi na shigar ciki a jikinta. 

A bincike kala kala da aka saba gudanarwa an riga an san cewa alamomi na shigar ciki a satin farko ba kowace mace bace take ganin su amma kuma dai binciken ya nuna cewa akasarin mata sukan ga alamomi na satin farko bayan ciki ya shige su. Su dai waɗannan alamomin mafi akasarin su shine; ciwon nono, ciwon ciki mai tsanani da sauran rashin lafiya. Waɗannan suna yawaita ne a cikin kwanaki biyar zuwa shida, kunga kenan waɗannan zasu zama sune alamomin shigar ciki na satin farko. 

Masana da manazarta sun sha yin bayani musamman ga mata akan cewa idan mace tana da yawan lissafi da kuma mai da hankali akan zuwan jinin al'adarta da kuma ɗaukewarsa to ba zata sha wahala wurin gane shigar ciki a jikinta ba. Sai dai, kuma duk da haka akwai wasu dalilan da ka iya sawa jini al'adar mace ya ɗauke ko da babu shigar ciki a jikinta. Kamar misali wasu larurorin rashin lafiya ko kuma amfani da wasu kwayoyin na bature da kuma wasu dalilan duk suna iya janyo ɗaukewar jinin al'adar mace na wani lokaci. 

Har ila yau dai, ɗaukewar jini na haila daga lokacin da ya saba zuwar wa mace, shine babbar alamar shigar ciki a jikinta amma dai kamar yadda na bayyana a sama wasu dalilan kan janyo ɗaukewar jini na wani ɗan lokaci. Amma kuma idan mace musamman ta san babu wani dalilin da zai iya janyo ɗaukewar jininta to babu tantama shigar ciki ne kawai zai sa jinin nata ya ɗauke. 

Wasu alamomin da za'a iya gane akwai shigar ciki a cikin sati daya kacal sun hada da;

Ciwon ciki mai tsanani

Canji a nono; kamar ciwon nono ko kuma kumburinsa, mace dai za taji nononta ya canza ba kamar yadda ta saba jin sa ba

Tashin zuciya da jin alamun hararwa watau amai ko kuma nausea a turance 

Yawan sha ruwa. Koda mace ta kasance irin mai shan ruwa ce sosai amma za taga shan ruwan nata ya tsananta sosai

Baya ga yawan shan ruwa kuma akwai yawan fitsari. Shima mace za taga tana yawan sintirin zuwa toilet yin fitsari

Ciwon kai; Mace zata rika fama da ciwon kai mai damu kuma akai akai duka a cikin wannan dan tsukukun na kwanaki biyar zuwa shida na farkon shigar ciki

Kumburin ciki da yin gyatsa sosai 

Kasala mai tsanani watau fatigue. Mace zata riƙa jin gajiya sosai ba tare da tayi wani aiki ba. 

Yawan bacci. Duk inda mace ta zauna Sai kuga ta sheme ta fara bacci mai nauyi. 

Waɗannan a taƙaice kenan duk alamomi ne dake iya nuna akwai yiwuwar shigar ciki a jikin mace a cikin sati daya kacal. 

Note (abin lura) :

Duka waɗannan alamomi dana lissafo a sama ba lallai bane mace ta gansu duka, haka kuma mace zata iya samun shigar ciki amma kuma ba tare da ko alama daya a cikin jerin waɗannan alamomi sun nuna a jikinta ba. Saboda kamar yadda wasu matan suke da laulayin ciki to kuma haka ake samun wasu matan da sam sam basu da laulayin ciki. Mace mai laulayin ciki itace wacce za tafi nuna waɗannan alamomin dana lissafo a sama. Idan har mace ta kasance mai mugun laulayin cikin to zata iya nuna duka waɗancan alamomin na shigar ciki a sati ɗaya. Wacce kuwa bata da laulayin ciki zai yiwu taƙi nuna ko alama ɗaya. 


Alamomin yadda ake gane shigar ciki na sati daya:

Ɗigar tabon jini (blood spotting) 

Ita wannan alamar tana daga cikin manyan alamomi na shigar ciki a sati daya to amma sakamakon cewa ba shigar ciki bane kadai ke kawo ɗigar jini daga farji ba, shi yasa masa da yawa basa farga ko kuma gane wannan babbar alamar. Misali, wasu matan da yawa sukan fara al'adar sune da wannan digar jikin, a saboda hakane idan suka ga digar jini daga farjin su sai su yanke hukuncin cewa na al'adar su ne. 

Haka kuma, shi wannan zubar ko ɗigar jinin daga farjin mace mafi akasari yana zuwa ne tare da ciwon mara wanda kuma hakan ne ke ƙara sawa mace tayi tunanin cewa al'adar ta ce take shirin zuwa saboda dama digar jinin al'adar ta yana zuwa ne tare da ciwon mara da kuma ciwon ciki. 

Gajiya (fatigue) 

Gajiya watau kasala a wurin mace mai shigar ciki ba wani sabon abu bane ba. A yayin da duk mace take jin alamomi kamar su jiri, canjin nono, canje canje a abincin da zata ci. To ita wannan gajiyar tana daga cikin alamomin da idan aka lura dasu za'a fi saurin fahimtar mai yiwuwa akwai shigar ciki a jikin mace. Gajiya irin ta mace mai ciki tana tattare ne da yawan kwanciya, kuma da zarar ta kwanta sai bacci. Kuma yawanci duk baccin da mai ɗauke da cikin nan zata yi to za'a ga cewa bacci ne mai nauyi. Koda sau goma mace zata kwanta a dan wuni daya to kuwa bacci mai nauyi zai kwashe ta. To irin wannan baccin akai akai alama ce ta akwai ciki a tattare da mace. Kuma a cikin satin farko wannan baccin da kuma gajiyar suna tsananta ne ga mace watau alamar wani bakon al'amari a tattare da ita yana faruwa. Sannan kuma bayan wannan tarin baccin da mai shigar cikin nan za ta riƙa yi akwai kuma gajiya sosai watau fatigue a tattare da ita, zai zamana idan ta tashi a gajiye take haka kuma zata wuni a gajiye ta kuma kwana a gajiye ba tare data yi aikin komai ba. Duk waɗannan alamomi ne na shigar ciki a satin farko. 

Canji a mama

Canji a maman mace mai shigar ciki shima yana daya daga cikin alamun samuwar ciki a satin ɗaya. Kamar dai wasu da yawa daga cikin alamomin da muke tattaunawa a cikin wannan rubutun, shima canjin mama a wurin mace mai shigar ciki yakan faru da macen da al'adar ta ke shirin zuwa. Sakamakon haka ne mata da yawa basa ganewa canjin da suka ji ko kuma suka samu a mama su na shigar ciki ne, musamman ma ga macen data ɗauki cikin farko kunga kenan bata da experience bata saba ba. Alamun canjin mama dai a sati ɗaya na shigar ciki za'a ji mama yaya nauyi sosai ba kamar yadda yake ba. Mama zai ƙara girma ya cika kuma za'a ga kan mama watau nipples sun ƙara baƙi watau sunyi duhu kenanan kuma zasu ƙara girma. 

Ciwon safiya (Morning sickness) 

Ciwon safiya watau morning sickness a turance kenan, za'a iya cewa yana daga cikin alamomin ciki na farko farko wanda idan aka lura dasu za'a yi saurin gane shigar ciki a jikin mace. Shi dai wannan ciwon na safiya watau morning sickness yawancin sa zazzaɓi ne da juwa watau jiri ko kuma dizziness a turance. Shi dai wannan ciwon na safiya idan mace tana yinsa za'a ga ta wuni kalau tana harkokinta haka kuma zata kwanta lafiya lau amma fa da zarar ta farka da safe zata tashi ne cikin mawuyacin hali na ciwo wanda ya haɗar da kumallo watau amai da zazzaɓi mai tsananin gaske da sauran lalurori irin wanda morning sickness yake kawo su. Duk wannan yana faruwa ne sakamakon jikin mai shigar cikin wanda yake sakin sinadarai watau hormones kamar su estrogen da kuma progesterone, waɗanda su kuma dama waɗannan sinadaran na pregnancy né wadanda ake kiransu da pregnancy hormones a turance. Watau ma'ana sinadarai ne na mai juna biyu. 

Ciwon kai

Ciwon kai yana daga cikin alamomi na farko farko wanda ba lallai mace don taji ciwon kai ta gane cewa akwai shigar ciki a jikinta ba. Tunda dama shi asali ciwon kai kamar alama ce mai nuna wa mutum cewa akwai wata matsala a jikinsa amma shi ciwon kai akan karan kansa na rashin lafiya bane. Shi dai zai zama kamar wata manuniya kawai. 

Canje-canjen abinci

Shima wannan wata babbar alama ce daga cikin alamomin dake nuni da cewa mace ta samu shigar ciki tun a satin farko. Idan ita macen ko kuma na kusa da ita misali mijinta suka ga tsirfarta tayi yawa a wurin abinda take son ci ko yaushe to ya kamata su rankaya zuwa asibiti domin yin gwaji. Idan haka kawai mace taga lokaci ɗaya ta canza tana yawan jin sha'awar kayan cima wanda bata marmari a da can, to hakan wata alama ce mai zaman kanta. 

Jin ƙamshi ko wari

Wannan alama ta jin ƙamshi ko wari sosai da sosai ba ita kadai bace alama irin ta ba. Da yake mace mai shigar juna biyu watau ciki tana samun sabbin canje canje ne a jikinta to hakan le sakawa jin ƙamshi ko wari ya tsananta a wurinta koda kuwa kamshin ko kuma warin basu wani taka kara sun karya ba. Wani lokacin ma za kuga mace tafi son yaji wari akan kamshi. Misali kamar mace ta rika son  jin warin kwata ko na toilet duka wannan na cikin canje canjen da jikinta ya samu a sakamakon shigar ciki. 

Yawaitar yin fitsari

Yawan fitsari akai akai kuma kwatsam lokaci daya kenan shima wata alama ce dake nuna shigar ciki a sati daya. Koda dai ba kowace mace bace za taji ta kuma gane ba, amma dai a sakamakon yawan jin fitsarin, ya kamata mace ace ta hasaso wani abu sabo a game da ita. 

A ƙarshe ina sake jan hankali ga makaranta cewa duka alamomin nan da aka tattauna a cikin wannan rubutun na lallai mace ta gansu ko ta jisu ba saboda duka wadannan abubuwan suna bambamta ne daga wannan macen zuwa wata macen. 


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post