Alamomin shigar ciki a satin farko

Alamomin shigar ciki a satin farko.

Barka hajiya ko uwargida da shigowa wannan babban shafi na hausawa, a yau zaki san alamomin shigar ciki a satin farko tareda ni mawallafin wannan shafi mai albarka.

Alamomin shigar ciki a satin farko

Menene Ɗaukar ciki?

Ɗaukar ciki ko muce samun juna biyu, yana nufin mahaifiya ko uwa ta ɗauki cikin halittar jariri ko jaririya a cikin mahaifarta inda zata cigaba da zama dashi a cikinta har yakai ranar da zata sauke shi. Hakan yanada matuƙar wahala, amma idan kika jure sannan kika jajirce to komai zai zo cikin sauƙi da yardar ubangiji maɗaukaki.

juna biyu yakan ɗauki kimanin aƙalla makonni arba’in (40) cif ko sama da haka koma ƙasa da hakan a wasu matayen, kamar yadda kika a lokacin da kika yi jinin al'adarki ta ƙarshe.

Menene alamomin shigar ciki a satin farko ?

Alamomin shigar ciki ko juna biyu a makon ga mace musamman amarya sun haɗa da kowane canji da zata iya fuskanta wanda ke nuni da cewa eh lallai tana ɗauke da juna biyu a tareda ita.

Mafiya yawan alamomin farko da ake gane cewa mahaifiya tana dauke da juna biyu, sun haɗa da:

1. Ɓatan wata

2. Canjin yanayin mama

3. Yawan kasala da gajiya

4. Yawan jin jiri

5. Yawaita yin fitsari

6. Yawan yin mafarki mara kyau

7. yawan samun tashin zuciya

8. Ciwon jiki

9. Canjin dandanon abinci.

10. Yawan samun ciwon jiki

Bayanin waɗannan alamomi na shigar ciki a satin farko:

Ɓatan wata: Bincike ya tabbatar da cewa a mafiya yawancin lokuta idan kina ɗauke da juna biyu, to alama ta farko da mace zata iya gane hakan shine ɓatan wata wato rashin zuwan jinin al'ada kamar yadda kika saba duk bayan wasu kwanaki, amma kuma wasu lokutan ba shigar ciki ne ke hana zuwan jinin al'ada ba a'a wata ƙila baki da lafiya ne.

Canjin yanayin nono: Zaki iya fuskantar yanayin mamanki ya canja kodai kiga yayi kumburi ko kuma ya dinga yi miki yawan ciwo, kai tsaye zamu cewa kina ɗauke da juna biyu matsawar lafiyarki ƙalau. Amma kiyi sani cewa ba dole bane sai kinyi ciwon nono sannan kike ɗauke da juna biyu.

Yawan kasala ko gajiya: Hakanan kawai zaki ji wata kasala ta rufe ki kuma keba aikin fari bare na baƙi, harma kiji kina neman kasa yin tafiya to wannan ma alama ce daga alamomin shigar ciki a satin farko.

Jirin kai: Duk lokacin da kika fuskanci cewa kina yawan samun jiri a kanki wato kiji kawai sai kiji kanki na neman cakewa kamar kinsha wani abu mai bugarwa, to gaskiya akwai alamar tambaya a kanki kuma yanda kyau ki ziyarci asibiti domin yin gwajin juna biyu a tareda ke.

Yawan Fitsari: haka zalika ta ɓangaren yawan fitsari abun haka yake, idan kina ɗauke da sabon ciki zaki dinga yawan fitsari akai akai wanda biki saba yin irinsa ba, to wannan yana daya daga cikin manyan alamomin shigar ciki a satin farko. 

Yawan munanan mafarkai: Wasu matan da zarar ciki ya shigesu to suna yawan fama da yin mafarkai bartakai marasa kyau, to kema ina tunanin hakan zata iya samunki a matsayinki na amarya, wato kinga ke nafi shigar farko ne kuma hakan zai iya samunki.

Duk lokacin da kika ga kina yawan mafarkai bartakai marasa dadi to ki soma bincike akan lafiyarki.

Yawan samun tashin Zuciya: idan zuciyarki tana yawan tashi wanda hakan bai saba kasancewa dake ba, akwai alamun kina ɗauke da ciki. Duk da hakan ba wata hujja wacce zaku dogara da ita tunda tashin zuciya hakanan ma yana iya faruwa, amma bincike ya samar da cewa yawan jin tashin zuciyar mace musamman sabuwar amarya to akwai yiwuwar samun ciki a tare da ita.

Ciwon ciki: yawan samun ciwon ciki ga mace musamman mai sabon aure yanada alaƙa da juna biyu, domin wasu matan idan aka samu ajiya a tareda suna yawan yin ciwon ciki. Wanda hakan zai iya hana cin abinci harma da abin sha sai kuma a koma kayan kwaɗai.

Canjin ɗandano: Da yawa daga cikin mataye sukan fuskanci rashin jindaɗin ɗandanon abinci ko kuma abin sha lokacin da suka samu juna biyu, hakan kuma yana samo asali ne daga yawan tashin zuciya da kuke fuskanta.

Mura: yawan yin mura akai-akai yana daga cikin alamomin shigar ciki a satin farko ga amarya, ta ɓangaren wasu matan daga samun ciki sai matan su soma yin mura. Hanci yakan iya toshewa, wasu ma hada yawan yin tari. idan kin tabbatar da cewa biki saba yin haka ba to akwai alamu na juna biyu a tareda ke.

Kowanne ɗaya daga cikin abubuwan da muka gabatar a sama, babu shakka sukan iya zama wata alama ta mace mai juna biyu, sai dai kuma a wani lokacin sukan iya kasancewa ba haka ba ko akasin hakan saboda wasu dalilai na bincike da kimiyya koma muce na bambance-bambancen halitta dake ƙunshe a jikin kowane ɗan adam.

Domin tabbatar da cewa kina ɗauke da juna biyu ko ciki musamman a satin farko?

Idan kin tabbatar kina fuskantar wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama to babu ko tantama zai iya kasancewa kina ɗauke da juna biyu. Amma kuma ta yaya zaki kara tabbatar da cewar tsammaninki gaskiya. Domin tabbatar da cewar juna biyu ne a zahiri to kina buƙatar gwajin kwararren likita, domin ganin likita shine kaɗai hanyar tabbatar da samuwar juna biyu.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post