Alamun ciki a watan farko

Yau a wannan rana mun zauna gamida yin bincike akan alamun ciki a watan farko. bincikon namu bai tsaya nan ba, harda shawarwari izuwa ga mai juna biyu domin inganta lafiyarta data jaririnta.

Alamun ciki a watan farko

Yanada matuƙar muhimmanci kowacce mace tasan alamomin dake nuna shigar juna biyu a tareda ita, sannan kuma ta fahimci idan taji ko taga waɗannan alamu ko canje-canje dake nuna tana dauke da juna biyu.

Kafin nayi nisa, zan so masu karatu ku sani cewa mun tsintsinto wasu daga cikin bayanan nan ne ta cikin jawabin da doctor Ibrahim Y. Yusuf yayi, yayinda wasu jawaban kuma mun samo sune daga mujallun lafiya harma da shafikan lafiya a yanar gizo.

Tun kafin kije asibiti, ayi miki test wato gwaji domin tabbatar kina dauke da ciki ko akasin haka, to kema yana da kyau kisan alamun shigar ciki a watan farko musamman idan kinyi sabon aure, daga fahimtar waɗannan alamomi zaki gane kina dauke da juna biyu, ta yadda zaki je da ƙwarin gwiwa domin ganin likita.

Shin mahaifiya zata iya gane tana ɗauke da juna biyu tun kafin zuwa Asibiti?

Kwarai uwa zata iya ganewa, amma kamar yadda Doctor ya bayyana, yace bafa kowacce mace ce tasan cewar batan wata shine babban abinda ke kawo juna biyu ba

Ƙwayoyin cuttukan iri daban-daban dake shiga mahaifa suma sukan kawo batan wata, [wato rashin ganin jinin al’ada], ko kuma ɓatan lissafin wata.

Wasu daga abubuwan daka iya kawo rashin ganin jinin al’ada sune kamar;

(1). Yawan yawo

(2). Shayarwa

(3). Rashin samun isasshen hutu [sakamakon yin wasanni masu wahala]

(4). Yawan damuwa

(5). Sha magunguna barkatai walau na gargajiya ko na Bature.

Abubuwan nan guda biyar dana jero, su ne wadanda doctor ya tabbatar sukan haifar da matsalar ɓatan wata.

Kuma baya ga su kamar yadda mu ka ambata a baya cewa, shigar kwayoyin cuttuka cikin mahaifa suma suna iya haifar da ɓatan wata.

Yanzu kuma zamu gangara kai tsaye kan maƙasudin wannan rubutu namu, wato alamun ciki a watan farko har zuwa tsufan ciki.

Bayanin alamun ciki a watan farko;

Yayinda aka samu shigar juna biyu a watan farko mafi akasarin mata basa ganewa ko ganin wata alama dake nuna kai tsaye juna biyu ya shiga jikinsu. Amma duk da hakan wasu matayen na iya ganin wasu alamun dake nuna shigar juna biyun da wuri musamman a makon farko, kamar su:

Zubar da jini: Wani samfurin fitar da jini ne dake faruwa kwanaki goma 10 zuwa 14 bayan mace ta ɗauki sabon ciki. Kuma hakan yana faruwa ne bayan ƙwayar halittar maniyyi [da za'a halitta] ta manne da ƙofar mahaifa.

Kumburin mama: Mace zata ji mamanta yana yi mata zafi koma ya kumbura sakamakon rashin samun motsawar jini yadda ya kamata a jikinta, hakan kuma na samo bayan shigar juna biyu.

Kasala: Koda yaushe zaki dinga jin wata sabuwar kasala na rufe ki, kuma kin tabbatar da cewa ba haka jikinki yake ba a baya.

Yawan fushi: Hakanan kawai zaki ji kina saurin yin fushi da mutane, ko kiji gaba ɗaya haƙurinki ya ragu abu kaɗan sai ki hau masifa, duka yana daga cikin alamun ciki a satin watan farko. 

Kamshi ko wari: Ya danganta wasu matan idan suka samu juna biyu sukan buƙaci ƙamshi da yawa koda yaushe, amma ta banganen wasu matan kuwa wari suke buƙata, wasu ma suna son zarnin fitsari.

Indai kinji wasu daga cikin abubuwan da muka ambata a sama na alamun ciki a satin watan farko, to yana da kyau kije asibiti domin ayi miki test na ciki domin tabbatar da samuwar cikin ko akasin haka.

Waɗannan sune alamun ciki a watan farko da amarya ko uwargida zata iya fuskanta;

Alamomin da uwargida ko amarya dake dauke da juna biyu da yakai kwanaki talatin ko watan farko zata iya fuskanta suna da dama amma ga wasu daga ciki kamar haka;

Amai (vomiting) wani lokacin da tashin zuciya musamman da safe [kuma shi irin wannan amai na masu juna biyu kan iya zuwa ba tareda anci komai ba]

Jin jiri (dizziness) yayinda kika zo tashi tsaye sai ki dinga jin kamar zaki faɗi ko kuma ki dinga fuskantar saurin gajiya in kinyi wani ɗan ƙaramin aiki.

Zubar da yawu: Wannan dama kamar an saba dashi, domin duk wata mace mai dauke da juna biyu tana iya zubar da yawu akai-akai sakamakon tashin zuciya da rashin jindadi baki. 

Rashin son kamshi: akwai matan da basa son ƙamshi amma wasu suna so lokacin da suke ɗauke da cikin, ya danganta da matar dake da juna biyun, rashin son ƙamshi ko sonsa yana ɗaya daga cikin alamun ciki a watan farko.

Zazzabi: Shima yin zazzaɓi ba wajibi bane ga mace mai ciki a watan farko amma mafi akasarin mata masu juna biyu a wannan kwanaki talatin suna samun yawan zazzaɓi harma da mura.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post