Hanyoyin samun ciki da wuri

Hanyoyin samun ciki da wuri

Koda yaushe yanada kyau ma'aurata su san hanyoyin samun ciki da wuri, domin hakan zai bayar da damar a samu haihuwa cikin sauri, karku fara tarazar haihuwa kafin ku haihu saboda hakan nada matuƙar hatsari, wannan rubutu na ƙunshe da lokacin da mace tafi daukan ciki, harda da yadda za'a samu saurin daukar ciki.

Hanyoyin samun ciki da wuri

Akwai hanyoyin samun ciki da wuri ko muce dabaru sosai na kimiyya, wanda inhar aka gwada amfani dasu ko aka daukesu aka yi aiki dasu da yardar Allah za'a dace cikin ƙankanin lokaci wanda a wannan gabar ta wannan rubutu zamu yi bayanin hanyoyin.

Menene juna biyu:

Juna biyu dai wanda muka fi sani da ciki shine, halittar abinda babu shi bayan yan kwanaki da curewar maniyyi mace da namiji, inda daga karshe yake komawa izuwa ɗan-tayi. Lokacin da uwa da samu ajiyar wannan ɗan-tayi a mahaifarta shine ake cewa juna biyu.

Wasu daga cikin alamomin ciki:

1. Rashin ganin jinin al'ada

2. Yawan ciwon baya

3. Tashin zuciya

4. Sauyawar mama

5. Yawan yin fitsari akai akai

6. Jin amai da yawan yin amai

7. Rashin son cin abinci

8. Yawan son shan kayan kwaɗai

9. Yawan ciwon jiki

10. Yawan jin gajiya da kasala.

Mun sani cewa samun ya'ya yanada daɗi a rayuwa, amma kuma samun aihuwa sannan a zauna cikin ƙoshin lafiya dangane da uwa yafi komai daɗi, ki fara tambayar kanki, shin kin shirya ɗaukar kuma zaki iya ?. Idan amsar eh ce wato kin shirya, to abinda zai rage miki kawai shine jira da kuma dauriya.

Waɗannan sune hanyoyin samun ciki da wuri da binciken mu ya samar daga kafa sahihiya.

(1). Ki ziyarci asibiti ki gana da likita domin yayi miki duba izuwa ga sinadarai masu kawo samuwar ciki da kuma isasshen folic acid, wanda yanada tasiri matuƙa domin yana kare duk wani cuta ko lahani da zai hana mace ta ɗauki juna biyu. folic acid yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka zama mataki na farko na daukar ciki ko rashin daukar, saboda haka yanada muhimmanaci ayi bincike akan sinadarin folic acid a jikin mace.

(2). Sanin lokacin jinin al'ada, shima wannan yana taka muhimmiyar rawa ta ɓangaren hanyoyin samun ciki da wuri, domin lokaci ne mafi dacewa daya kamata ayi saduwar aure, saboda lokaci ne da ake samun juna biyu da wuri, wannan yana kyau domin mace tasan lokacin da take jinin al'ada. sannan akwai hanyoyi masu yawan gaske wanda matar aure zata auna ta gane lokacin da take al'ada ko kuma lokacin da al'adan nata ke tsayawa. Sanin lokacin da kike yin al'ada zai taimaka ba kaɗan ba wajen samun ciki da wuri, saboda haka iyaye ya kamata kafin a yiwa yarinya aure to a nuna mata hanyar da zata kula da jininta.

(3). Ki kasance mai zama akan gado bayan an kammala saduwa, shima wannan wata hanya ce dake taimakawa sosai wajen samun ciki da wuri, kuma ana bukatar bayan mata da namiji sun gama saduwa to idan so samun ne anaso su bada ratar kamar mintuna 15 zuwa 20 domin hakan zai bawa maniyyi ya sauka inda ake buƙata wato ya ƙarasa sauka zuwa mahaifa.

(4). Idan kai namiji ne to kada ka kasance mai yawan kwanciyar aure, saboda yawan saduwa akai akai, ba shine zai sa mace ta dauki ciki da wuri ba, abinda ake bukata shine koda yaushe shine a riƙa samun tazara koda na kwana 1 ko 2 saboda wasu lokutan maniyyi yakan kai kwana aƙalla 5 bayan fitansa daga jiki.

(5). Ma’aurata wato mata da miji duka biyu anaso su kasance masu rage saka damuwa a ransu kowannen su ya cire damuwa da tunani, saboda hakan yakan yi tasiri sosai wajen samun juna biyu, saboda haka a lokacin da kuke saduwa domin samun albarkar juna biyu to kuyi ƙoƙari ku cire duk wata damuwa a ranku domin hakan shine yafi.

(6). Koda yaushe anason kasantuwar lafiya a tattare da ma'aurata, ana buƙatar daga kai har izuwa matarka ku kasance masu isasshen lafiya kuma ku dinga motsa jiki kada ku dinga zama haka kawai babu exercise wato motsa jiki.

(7). Koda kin kasance mace mai yin shaye-shaye to ya kamata ki daina har sai lokacin da burinki ya cika wato ma har sai ranar da kika yaye jaririnki, saboda shan miyagun na daya daga cikin hanyoyin hana samun ciki da wuri.

(8). Ki daina sha ko amfani da duk wani abin sha soft drinks wanda ke dauke da caffeine, wato wani sinadari me hana bacci yana kuma ƙarin kuzari misali kamar a sabon abin sha mai suna (V-COOL) ko a PASSION me karfin doki, to duk wadannan ya kamata a gujesu.

(9). Ki rage yawan wahalar da kanki matukar kinason samun ciki da wuri tofa saikin rage yawan aikace-aikace a gida.

(10). Ki tabbatar kina yawan ganin likita akai akai saboda hakan zai bada damar sanin halin da kike ciki da kuma matakin daya kamata ki ɗauka. 


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post