Alamomin ciki a bayan mahaifa

Alamomin ciki a bayan mahaifa post

A wannan rubutun mai taken alamomin ciki a bayan mahaifa harma da alamomin cikin ya mace yana ƙunshe a ciki, Hmm nasan daga jin sunan zai sa wasu da yawa daga jikin makaranta su fara zancen zuci da kuma tunanin shin dama ana samun ciki a bayan mahaifa ? Kwarai kuwa ana samu. Sai dai kafin na kai ga bayyana irin alamomin da idan aka gani za'a fara zargin yiwuwar ciki a bayan ko wajen mahaifa akwai buƙatar nayi waiwaye domin fayyace muku menene shi kansa ciki a bayan mahaifa, tare da haka kuma ta yaya ake samun sa ma'ana ta yaya yake kasancewa watau dai menene ke faruwa har ake samun cikin a baya ko wajen mahaifa ba tare da cikin ya shiga cikin mahaifa ba kamar dai yadda aka sani kuma kamar yadda aka saba. 

Alamomin ciki a bayan mahaifa

Idan kuma kuna tare dani har zuwa ƙarshen rubutun nan zamu tattauna hanyoyin yadda ake bi ake gane shin mace na ɗauke da ciki a waje ko kuma bayan mahaifar ta sannan kuma wane hanyoyin ake bi domin magance matsalar ciki a wajen ko kuma bayan mahaifa. Duka wannan abubuwan zamu tattauna tare daku idan har kuka bani aron hankulanku kacokan kuma kuka bini har ƙarshen wannan rubutun. 

Yadda ake samun ciki a bayan mahaifa.

Shi dai ectopic pregnancy watau ciki a bayan mahaifa, yana samuwa ne sakamakon kyankyashasshen kwai (fertilised egg) ma'ana kwan daya haɗu da maniyyin namiji ya dasa kansa a wani waje saɓanin inda ya saba zama watau cikin mahaifar mace. Bayan kwan ya samu waje ya zauna zai cigaba da girma kamar yadda ciki yake girma a cikin mahaifa. Shi dai ectopic pregnancy watau ciki a bayan mahaifa yana da haɗari idan yaci gaba da girma a haka ba tare da an gano an kuma magance matsalar ba. 

A ƙasashen duniya waɗanda suka cigaba, watau developed countries ana samun masu ciki a bayan mahaifa da kaso ɗaya tal a cikin ɗari yayin da kuma ake samun masu ciki a bayan mahaifa da kaso biyar cikin ɗari a ƙasashen dake tasowa, wannan ya samo asali ne daga yanayin kula da kiwon lafiya watau health management system wanda yake akwai bambanci sosai a tsakani. 

Me ke kawo faruwar sa ko kuma haddasa shi ? 

Izuwa yanzu babu wani cikakken bayani ko kuma sahihiyar amsar data nuna dalilin samuwar ciki a bayan mahaifa, amma dai a bincike tare da hasashen da manazarta suka yi, suke kuma kanyi, sunyi lissafin abubuwa da dama waɗanda acewarsu, sune abubuwan da idan akwai su ko kuma idan abubuwan suna  kasancewa to mace zata iya samun ciki a bayan mahaifar ta, watau dai suna nufin kamar abubuwan da ake kira da clinical risk factors kenan. Waɗannan abubuwan sun haɗar da;

Cutar sanyin mara

Macen data samu miscarriage watau zubewar ciki a baya

Macen data taɓa samun ciki a bayan mahaifarta 

Macen data samu ciki bayan tana da shekaru da yawa misali (45 years) 

Cututtukan infections 

Mace da take zuƙar taba sigari 

Cututtukan infections a gaban mace

Cikin da aka samar dashi ta hanyoyin zamani, misali; surrogacy

Amfani da robar mahaifa

Cutar fibroids

Cutar kansar mahaifa 

Macen da namiji yake saduwa da ita tun tana ƙaramar yarinya

Macen da take kwanciya da maza da yawa 

Mace mai matsala a mahaifar ta

Mace data samu matsalar toshewar fallopian tube watau bututun fallopian. 

Jerin alamomin cikin da yake a bayan mahaifa:

Alamomi watau symptoms na ciki a bayan mahaifa mafi akasari guda uku ne kwarara. Kuma su waɗannan alamomin suna faruwa ne a jere da juna kamar haka;

1- Rashin ganin jinin al'ada

Kamar dai yadda ake samun alamomin shigar ciki koda kuwa a cikin mahaifa ne, wanda a cikin alamomin sa akwai ɓatan wata watau rashin ganin al'ada to a wannan halin ma na samun ciki a bayan mahaifa ko kuma a wajen mahaifa shima akwai ɗaukewar jinin al'ada. 

2- Ciwon mara mai tsananin gaske

Wannan alamar ta ciwon mara, masu ciki wanda bashi da matsalar nan watau cikin da yake cikin mahaifa kenan, suma sukan samu ciwon mara amma bambamcin shine su masu ciki a bayan mahaifa nasu ciwon marar yana tsananta ne da yawa sannan kuma ɓarin da yafi ciwo to wannan yana nuna alamun cewa anan ne cikin ya kwanta.

3- Zubar jini daga farjin mace

Shi dai wannan zubar jinin yana da wahalar gane matsayin sa a wurin Mace, domin mata da yawa sukan yi tunanin zubar wannan jinin na al'ada ne, to amma kuma shi wannan jinin bai kai yawan jinin al'ada ba. 

Tare da haka kuma, bayan ganin waɗannan manyan alamomi guda uku, mace kan iya fuskantar wasu ƙananan alamomin kamar su zazzaɓi, amai da gudawa, rashin ƙarfin jiki, jiri, ciwo yayin da take fitsari  da makamantansu. 

Yadda ake gane kasantuwar ciki a bayan mahaifa ta zamani a asibiti;

A lokacin wannan rubutun, a yanzu haka kenan halin da ake ciki a ƙasashen ƙetare inda aka cigaba watau developed countries da kuma ƙasashe masu tasowa watau developing countries, ana bincike a kuma gane cikin da aka samu a bayan mahaifa ta hanyar yin gwaje gwaje watau tests kamar guda biyu zuwa uku. Waɗannan gwaje gwajen da akeyi sun haɗar da;

Gwajin ciki (Pregnancy Test)

Wannan gwaji ana yin sa ne dama don a sani a kuma tabbatar da mace tana da ciki ko kuma bata da shi. 

Akwai hoto na ultrasound da ake kira Transvaginal Scan (TVS): Shi dai wannan hoton na musamman ne wanda yake nuna abinda yake cikin mahaifar mace mai ciki. Bayan an tabbatar mace tana da ciki a wancan gwajin ciki da akayi mata, to idan aka samu shi wannan hoton bai nuna komai a cikin mahaifar wannan mai cikin ba to kuwa tabbas wannan cikin na jikinta baya cikin mahaifa kenan don haka yana bayan mahaifarta. 

To daga wannan gaɓar ne masana a kiwon lafiya zasu fara bincike akan inda wannan cikin yake duk da dai ire iren binciken da aka gabatar akan mata masu ciki a bayan mahaifa sun nuna wuraren da cikin yafi zama wurare ne guda uku kamar haka;

-Bututun fallopian (fallopian tube) 

-Cikin kogon peritoneum a dai dai kan bakin mahaifa

-Cikin ovary

-Gwajin gane adadin sinadarin beta-hCG a cikin jinin mace

Shi dai wannan gwajin ba dole sai an aiwatar dashi ba. Illa iyaka dai shine yawan wannan sinadarin na beta hcg a cikin jini yana nuna cewar mace na ɗauke da juna biyu idan kuma yawan sa ya ƙetare har ya kai wani range ɗin daban watau wani adadi to hakan yana ƙara tabbatar da cewa akwai ciki a wajen mahaifar mace. 

Yadda ake maganin juna biyu a bayan mahaifa:

Yadda za'a magance wannan matsalar ta zaman ciki a bayan mahaifa ya danganta ne da lokacin da aka gane akwai shi. Idan lokaci bai ƙure ba, ma'ana idan anyi saurin ganewa za'a iya tarar matsalar a gyara ta. Idan kuma cikin yayi girma har ya kai ga fashewa to fa dole sai an haɗa da tiyata an cire shi saboda ba zai ɗore ba a sannan, domin kuwa ita mai cikin zata shiga wani matsanancin hali ne a lokacin wanda idan ba'a bata taimakon gaggawa ba zata iya rasa rayuwar tama gaba ɗaya. 

Idan ta yiwu an gane ciki a bayan mahaifa da wuri kamar yadda na ambata a sama to gyaran da za'a iya yiwa cikin da yake wajen mahaifar shine; za'a riƙa monitoring ɗinsa ne ana kuma fatan ya koma cikin mahaifa. Idan kuwa ya cigaba da girma a haka to babu wani zaɓi kuma sai dai a lalata shi ta hanyar yin allura cikin ya zuɓe. 

Ga wasu jerin tambayoyi da mata waɗanda suka taɓa samun irin wannan matsalar suke yawan yiwa malaman asibiti:

1. Shin irin wannan cikin zai sake faruwa dani kuwa?

Wannan ita ce tambayar farko a cikin jerin gwanon tambayoyi da irin waɗannan matan sukeyi. Kuma dama na ambata tun a farkon wannan rubutun cewa masana da manazarta sun lissafa matar data taɓa samun ciki a bayan mahaifa cikin clinical risk factors na wannan matsalar, watau cikin abubuwa ko kuma dalilai da zasu sa a samu wannan matsalar ta ciki a bayan mahaifa. 

2. Babu matsala idan na ƙara ɗaukar ciki ? 

A nazarin manazarta da na masana dai kawo yanzu babu wata hujja ko dalilin da zai sa macen data samu matsalar ciki a bayan mahaifa ta shiga wani haɗarin bayan samuwar wani cikin. Sai dan idan ya kasance an bata wasu magunguna a wancan matsalar, domin kuwa a cikin magunguna da ake bawa mata da suka samu irin wannan matsalar akwai  magani wanda yake da lahani sosai ga ɗan tayi watau foetus. 

3. Shin akwai wasu hanyoyi da zan bi domin kariya daga faɗawa wannan matsalar ?

Babu wata hanya da ake bi ko wani magani da likita zai iya bayarwa wanda za'a sha domin kariya daga samun ciki a bayan mahaifa. Sai dai fatan a samu ciki a cikin mahaifa kawai. Kuma ayi fatan kada yazo da wasu complications ɗin watau wasu mishkilolin ko matsalolin na daban kuma. 

Sannan baya ga haka, kamar yadda nayi bayanin akan abubuwa ko kuma dalilan da manazarta da masana suka zayyano a matsayin clinical risk factors watau waɗannan abubuwan da idan suka faru ko kuma idan akwai su to zata iya fuskantar wannan matsalar ta samun ciki a baya ko kuma wajen mahaifa a maimakon cikin kogon mahaifarta kamar yadda ya kamata. 

To su waɗannan abubuwan ya kamata mata su duba suyi nazarin su su kuma nisanta dasu ko ba don komai ba domin tsira da rai da kuma lafiyar si da kuma tseratar da rai da lafiyar abin da yake cikinsu idan har sun daura damarar daukan ciki. 

Kamar dai misalin cututtukan Infection wadanda likitoci suka lissafo cikin abubuwan dake taimakawa wurin samuwar wannan matsalar. Kunga kenan ya kamata mata su tashi tsaye tsayin daka domin yaƙar cutar infection haka kuma ga mata masu tarawa da maza da yawa suma ya kamata su guji wannan mummunar dabi'ar ta yin alakar saduwa da maza da yawa. Haka kuma da mata masu fama da matsalar karin nan watau fibroid suma sai su dage domin neman magani saboda shima an lissafo shi cikin clinical risk factors na abubuwan da zasu iya janyo samuwar ciki a baya ko kuma wajen mahaifa. 


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post