Maganin farin jinin samari

Maganin farin jinin samari

Wannan jawabi yana ƙunshe da da bayanin maganin farin jinin samari, kama daga addu'ar farin jinin samari, maganin farin jini da tumfafiya, lakanin farin jini, wuridin farin jini da dai sauransu, kuma mun samo sune daga kafa sahihiya.

Maganin farin jinin samari

Kamar yadda tittle ɗin wannan rubutun yake, wasu mutanen ko kuma makarantan zasu yi mamakin cewa dama mata suna neman ko kuma zasu iya neman magani ko laƙani ko dai wani taimako na farin jini domin samun samari? Kwarai kuwa mataye da yawa, mata da dama suna nan suna neman ire iren waɗannan laƙanan ko magungunan. Haka kuma ga waɗanda zasu yi mamakin kasancewar hakan, to hakan fa ba wani abun mamaki bane musamman idan akayi duba ko la'akari da irin yanayin rayuwar da ake ciki. Kafin na kai ga lissafo dalilan da yasa mata zasu nemi irin wannan taimakon na farin jinin ɗa namiji zan fara kawo muku misali guda ɗaya tal. 

Misali, mace ce ta taso tare da ƙawayenta tun na yarinta. Ƙawayenta a gida ko a makaranta har suka girma suka kai minzalin aure. Sai duka ƙawayenta suka samu mazajen aure kuma suka yi auren har aka samu ƙaruwa watau ƴaƴa, ita kuma tana gida har wannan lokacin. Ku faɗa min don me ba zata riƙa samun damuwa ba? Wannan misalin na mace ɗaya ne kawai to mata nawa ne suka fuskanci irin wannan jarrabawar? Haka kuma mata nawa ne zawarawa waɗanda anyi auren amma kuma an sake su, auren ya mutu, wasu kuma mazajen sun mutu saboda haka babu auren. Duk ku lissafa irin waɗannan instances ɗin zaku ga cewa lallai dole mace marar aure a wannan zamanin taso yin aure, kuma kar ku manta wannan misalin dalili dɗya ne tal na bayar. 

A wannan zamanin da muke ciki mun tsinci kanmu ne a cikin wani irin rikirkitaccen zamani wanda a cikinsa adadin mata sun fi adadin maza yawa a ko ina da ina a faɗin wannan duniyar da muke cikin. Ko wace nahiyar watau continent haka kuma kowace kasa idan da za'a zagaya ayi ƙidaya da kuwa za'a tabbatar da cewar mata sunfi maza yawa. Wannan yana daga cikin ƙalubalen da mata suke fuskanta na rashin samun samari bare kuma akai ga maganar aure, ba wai anan ƙasar hausa kaɗai ba, har a sauran sassa na duniya baki ɗaya. Saboda haka ba abun mamaki bane don haka yana samar da damuwa a tsakanin matayen da basu da aure da waɗanda ko samarin ma basu dasu. 

Akwai mata da yawa waɗanda ko sallama ba'a taɓa yi dasu ba irin matan nan da za kuji ana cewa ai basu da mashinshini. A tsarin shari'ar musulunci wacce ita muke bi a ƙasar hausa kasancewar mu musulmai, watau namiji yana da damar auren mace ɗai ɗai har huɗu, haka kuma ga sarakuna da manyan attajirai suna da damar haɗawa da kwarkwara watau sa ɗaka ko kuma a turance wacce ake kira da concubine, amma fa duk da haka akwai mata birjik da yawa waɗanda suna nan jingim babu mashinshini. Duba da irin waɗannan challenges watau ƙalubale da mata suke fuskanta ya zama dole hakan ya dame su. 

Idan kuma mace bata samu tsayayye ba watau saurayin da yake son ta da aure sai kuji mutane sun fara maganganu akan ta kuji ana cewa ai taƙi aure. Idan mace bata samu aure ba zaman gida ya dame ta, tayi tunanin komawa makaranta nan ma bata tsira ba domin mutanen unguwa ne zasu fara maganganun cewa taƙi aure tace sai tayi boko, irin waɗannan abubuwan dole ne su damu mataye saboda ana yin maganganun akan su tamkar sune zasu aurar da kansu. Kuma duk masu yin irin waɗannan maganganun sun sani sarai cewa mace bafa zata aurar da kanta ba amma saboda yanzu kiwon mutum ake bana dabba ba, shi yasa ake zunɗen matan da basu samu aure ba. 

To wai ma tukunna, tun yaushe son yin aure a wajen mace ya zama laifi ko rashin kunya?  Ko ɗaya babu. Wai don mace tana son samun saurayi, ko kuma tana son yin aure dai ya zama abun magana, to tabbas duk waɗanda suke ganin hakan bai dace ba, sune suke buƙatar su sake tunani, domin kuwa ga macen dake son samun saurayi tsayayye har hakan ya kai su ga yin aure ko kuma macen data haƙiƙance aure take so, indai da kyakykyawar niyya ne to tabbas lada mace mai wannan niyyar zata samu tunda dai sunna take son rayawa. 

Kafin na kai ga yin bayani akan magani, taimako ko wasu laƙanan farin jini da mata zasu iya amfani dasu domin samun samari, akwai wani babban jan hankali da zanyi. Yake mace mai son sanin maganin farin jinin samari, akwai buƙatar ki ƙudurce a zuciyar ki cewa su waɗannan magungunan, laƙanan ko kuma taimako da ake bayarwa ba sune guarantee ba, watau ma'ana ba sune ke nuna tabbas cewa idan kinyi amfani dasu zaki dace ba. Dama tun ran gini ran zane, al'amari duka kowane iri ne yana wurin Mai duka. Saboda haka kar ki manta maganin farin jini, wannan wani ƙoƙari ne kawai zaki yiwa kanki daga nan sai ki koma gefe ki cigaba da sa rai kina addu'a. 

Jerin magungunan farin jinin samari:

A cikin taimako ko laƙanai ko magunguna na irin waɗannan matsalolin, wasu daga ciki addu'o'i ne kawai, wasu kuwa ana yin rubutun sha ne, yayin da wasu kuma ake yin rubutu asha a kuma shafe jiki da ruwan rubutun. Bayan haka kuma wasu laƙanan ko taimakon akan samar dasu ne ta fuskar hatimai ko layu. Tare da haka kuma, ana amfani da ayoyi na Al-Qur'ani babban kundi wanda a cikin ire iren taimako ko laƙanin da ake bayarwa sun hadar da;

-Sirrin Alam Nashrah suratul sharhi
-Laƙanin suratul Yusuf 

Waɗannan suna daga cikin sannannun laƙanai ko taimako da ake yi domin samun farin jini na mutum ko na kasuwa ko na wurin aiki da dai sauransu. Wanda kuma a cikin wannan rubutun zanyi bayanin yadda ake amfani dasu. 

Bayan wannan kuma akwai laƙanin furen tumfafiya wanda ake amfani dashi ta siffofi da yawa domin samun farin jini. Akwai magani ko laƙanin farin jini na hatimi kamar yadda na ambata a sama, dukan su zanyi bayanin su kamar haka;

Laƙanin furen tumfafiya:

Idan kina neman farin jini to ki riƙe wannan sirrikan na tumfafiya kamar haka;

-Ki yawaita cin furen tumfafiya yana kawo farin jini ainun. Garin furen tumfafiya idan ana zubawa a ruwa ana wanke fuska dashi  duk inda kika shiga a riƙa son ki, zaki tsaya a ran mutane musamman samari kamar yadda kike fata. 

-A zuba garin furen tumfafiya a cikin abinci a ci yana kawo farin jini sosai ba da wasa ba, ki riƙe wannan. Sanya furen tumfafiya a aljihu zai sanya ki ki zamo mai farin jini sosai. 

-Ana haɗa furen tumfafiya da furen bishiyar zaitun sai a zuba a man shafawa a riƙa shafawa a jiki wannan ba ƙaramin haɗi bane na sirrin farin jini, ina faɗa maki, idan har kika yi wannan haɗin kika kuma yi amfani dashi da kanki zaki zo kina nema na domin miƙo saƙon godiyarki, amma kar ki damu ke dai kawai do as you are told. 

Maganin farin jini na laƙanin suratul yusuf:

Ga kuma wani babban sirri ko kuma nace maganin farin jini mashahuri wanda shima idan ki kai amfani dashi zaki sha ruwan mamaki. Shi dai wannan sirrin tested and trusted ne musamman akan irin matan nan da basu da samari da kuma waɗanda suka jima babu aure, da yawa yawan su bayan an basu sirrin sunje sun gwada yanzu sai dai labari kamar yadda bature mai jan kunne yake cewa; the rest is history.. To don haka ki karkaɗe kunnuwan ki kuma ki buɗe idanunki ki karanta abinda na rubuta na kuma kawo miki domin amfanin ki. Shi dai wannan sirrin farin jini ne na laƙanin suratul Yusuf sura mai albarka sura ta goma sha biyu a cikin babban kundi watau littafi mai tsarki kenan Al-Qur'anil Kareem. 

Ga yadda sirrin ko kuma nace lakanin yake;

Za'a rubuta suratul yusuf kafa tara (9) duk bayan aya ɗaya sai a rubuta (AZZAUJU). Da haka da haka za ayi ta rubutawa har sai an rubuta ƙafa tara ɗinnan. Za kuma a wanke asha da ruwan zam zam da kuma zuma fara.

Sirrin suratul sharhi alal nashrah kenan, da kuma hatimin ta.

A wannan sirrin za'a nemi hatimin dana ambata a sama ƙafa ɗaya sannan a rubuta suratul sharhi watau alam nashrah kafa bakwai (7) asha na tsawon kwana bakwai watau sati ɗaya kenan, one week inji turawan yamma. Idan kika aikata wannan matuƙar dai farin jini kike nema to ba keba sai dai kuma ki bawa wata labari,saboda tsananin ƙarfi da tasirin wannan sirrin ko laƙanin don haka ki kiyaye shi kuma ki jiɓanci amfani dashi.

Haka kuma ana rubuta alam nashrah idan aka rubuta ayar farko sai a tsaya a tsakanin aya sai kuma a rubuta "malikinnas" sai kuma a tafi aya ta biyu haka za'a riƙa yi har ƙarshen surar. Kuma haka za'a ta rubutawa har ƙafa tara. Daga nan sai a wanke a samu zuma mai kyau a zuba a shanye. Za'a yi wannan ne na tsawon kwana uku (3) 

Laƙanin farin jini na hatimi:

Akwai wani laƙanin farin jini na samari yaku mata wanda idan kuka dace kuka yi amfani to fa kakarku watau grandma, ta yanke saƙa daga wannan ranar da aka aikata shi. Shi dai wannan sirrin ko kuma laƙanin na wani hatimi ne mai ɗauke da haruffan larabci na ba, da dalun, da wawun da kuma jimun. Idan aka samu hatimin aka rubuta to sai a wanke asha da Zuma, sannan za'a a sake rubutawa a mudubi watau mirror sannan a wanke fuska, bayan haka za'a sake rubuta shi ayi laya dashi. Wannan sirrin da na gama bayyana muku mujarrabi ne watau tested and trusted ne, ku gwada shi zaku sha mamaki tsantsar sa.

Ga kuma wani mashahurin maganin farin jinin da zaki gwada, shima kar ki yadda kiyi sake wurin jarraba shi.

Ga yadda zaki yi wannan wuridin mai cike da ɗimbin mamaki kamar haka;

Zaki yi wuridin wannan ayar sau adadin sunan ki tsawon kwana bakwai (7) sati ɗaya kenan a jere. Ga ayar kamar haka;

"Wa Alƙaitu Alaika Mahabbatan Minni"

Waɗannan wasu daga cikin laƙanai ko taimakon da akafi amfani dasu domin samun dacewa ta farin jinin mata a wurin samari kenan, sai a karanta a kuma jarraba a nutse ko za'a samu dacewa.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post