Maganin istimna'i na gargajiya

Maganin istimna'i ma gargajiya

A cikin wannan rubutun zanyi duba akan maganin istimna'i na gargajiya da kuma menene Istimna'i kuma ya yake sannan kuma a ƙarshe tare daku zamu tattauna game da magungunan matsalar istimna'i na gargajiya domin shine maƙasudin wannan rubutun. 

Maganin istimna'i na gargajiya

Menene Istimna'i ? 

Istimna'i dai kalmar larabci ce wacce take nufin mutum ya gamsar da kansa ta fuskar sha'awa yayin da duk buƙatar hakan ta taso ko kuma sha'awar ta bijirowa mai yin hakan. Istimna'i na ɗaya daga cikin matsalolin da suka zame mana ruwan dare cikin irin halayen da muka tsinci kanmu a wannan rayuwar. 

Bugu da ƙari, ita matsala ta istimna'i mutane da yawa basu fahimci cewa matsala ce dake ɗauke da abinda ake kira da addiction ba a turance, watau wani abu ne mai wuyar bari. 

Domin mai karatu yafi samun damar fahimtar me ake nufi da kalmar addiction da kuma alaƙar ta da istimna'i ga yadda masana da manazarta suka fayyace mana kalmar addiction a turance kamar haka;

"Addiction is a brain disorder characterised by compulsive engagement in rewarding stimuli despite adverse consequences..

Fassara;

Addiction wata matsala ce ko kuma lalura daga kwakwalwa wacce take alaƙantuwa da  tsananin son yin, ko kuma aiwatar da wani abu domin samun gamsuwa ko jin daɗin yin wannan abun duk kuwa da munanan sakamakon abubuwan da zasu biyo baya. 

Watau anan ana nufin kai tsaye duk abinda akace addiction ne, idan mukayi duba da bayanin dake sama to kuwa zamu fahimce cewa duk wanda yake da addiction nayin wani abu to fa tamkar ya farlantawa kansa yin ko kuma aiwatar da wannan abun ne, ma'ana dai ya zame masa dole ya aiwatar koda kuwa hakan yana nufin cutar da kansa ne, wanda dama kuma sau tari ko kuma nace kaso casa'in watau 90% cikin ɗari na ire iren addiction da ake dasu duk kansu na cutar da kai ne. 

Misalan ɗabi'un addiction sun haɗar da;

Zuƙar taba sigari 

Shan tabar wiwi

Shan giya

Amfani da hodar iblis 

Ta'ammali da miyagun kwayoyi 

Cin goro

Shan lemon coca cola ko lemuka makamancinsa

Shan gahawa (nescafe) 

Yawan jima'i 

Istimna'i 

Amfani da nau'in abincin junk watau junk food 

Idan mai karatu yayi duba da nau'o'in addiction dana lissafa a sama za'a ga wasu nau'ikan ababen cima ne amma kuma suma amfani dasu na tsawon lokaci yana da illa sosai ga lafiyar ɗan adam, to kamar haka ne a cikin addiction na sex watau jima'i ko kuma na istimna'i. 

Istimna'i kamar yadda na bayyana a sama matsala ce da ta yaɗu a cikin al'ummomi daban daban a sassa na duniya haka kuma take a tsakanin maza da mata, waɗanda suka tsinci kansu da tayarwa kansu da sha'awa da kuma kwantar wa kan nasu da sha'awar da suka tsokano ta hanyar gamsar da kansu. Hanyoyin gamsar da kai na istimna'i suna da yawa, musamman a wannan rikitaccen zamanin da muka samu kan mu wanda yake cike da irin abubuwan da zasu tsakano sha'awar mutum da kuma abubuwa da dama da zasu kwantar masa da ita. Misali a wayar hannu mutane da yawa suna downloading watau ma'ana suna sauke fina finai na batsa su riƙa kallo, ta wannan hanyar suna tayarwa da kansu sha'awa kuma suna saukar wa. 

Istimna'i dai a bincike na masana da manazarta an tabbatar da yana taɓa lafiyar ɗan adam, domin kuwa kamar yadda taba sigari take ɓata hunhu watau lungs na masu zuƙar ta, to haka yawan istimna'i yake ɓata ƴaƴan maraina na ɗa namiji kuma haka yake ɓata bakin farjin mace waɗanda suka jima a cikin wannan harkar ta istimna'i. Ga kuma wasu daga cikin matsalolin da mai yin istimna'i zai iya fuskanta kamar haka;

Yawan mantuwa

Ƙunci da Damuwa

Faɗuwar gaba

Ƙanƙancewar gaba

Ƙarancin ibada

Cutar kwakwalwa

Tsinkewar maniyyi

Zubewar ciki

Hana ɗaukar ciki

Ciwon sanyi

Ƙaiƙayin gaba maza da mata

Feshin ƙuraje a gaba

Fitar da farin ruwa a gaba

Jin zafi yayin saduwa

Ƙarancin sha’awa

Ɗaukewar Ni’ima

Saurin inzali

Gaza gamsar da miji ko mata

Saurin fushi da yawan firgita

Idan mu kayi duba zamu ga cewa a cikin waɗannan matsalolin wasu da yawa daga ciki matsaloli ne da zamu iya kira da social, mental ko kuma psychological problems, watau ma'ana matsaloli a zamantakewa wanda kuma duk a dalilin istimna'i mutum zai samu waɗannan matsalolin. Matsaloli kamar; yawan mantuwa, ƙunci da damuwa, ƙarancin ibada, cutar kwakwalwa dukan su zamu ga cewa matsaloli ne waɗanda zasu shafi zamantakewar masu yin istimna'i da kuma mutanen da suke rayuwa a tare da su. 

Wasu mutanen kuma musamman samari da ƴanmata sukan yi jima'in waya ne wanda suke kira da sex call ko kuma hira watau chat wanda ake kira da sex chat. Waɗannan duka wasu nau'ika ne na istimna'i wanda zamani yazo dasu. Istimna'i kuma wanda aka sani tun ada shine wanda mutum namiji ko mace suke zauna ko kwanciya suna wasa ko taɓa sassan jikin su watau al'aurarsu har sai sun kai ga biyan buƙata. 

Da yawan matasa watau youth maza da mata a wannan zamanin kamar yadda na bayyana a sama, sun tsinci kawunansu a cikin wannan matsalar ta istimna'i hakan yasa suke yawan yiwa malamai tambayoyi akan yadda zasu yi da matsananciyar sha'awar da take addabar su. A cewar su ire iren matasan nan wai suna aikata istimna'i ne saboda kar su faɗa zina. Sai dai kuma abun da basu gane ba shine, istimna'i matsala ce mai zaman kanta koda kuwa babu zina. Idan istimna'i yayi wa mutum mugun kamu to kuwa yana cikin garari babba domin kuwa idan ba'a yi da gaske ba mutum ba zai iya denawa ba har tsufan sa. 

Kamar yadda na ambata na kuma yi bayani dalla dalla a sama, shi istimna'i addiction ne, kuma a cikin addiction ɗin ma mai matuƙar wahalar rabuwa saboda haka ne a cikin wannan rubutun a tare da ku zamu yi duba zuwa ga magunguna na gargajiya kenan wanda za'a iya amfani dasu a magance wannan gagarumar matsala ta istimna'i. Sai dai kuma kafin nan, ya kamata mai karatu ya sani ya kuma fahimci cewar matuƙar mutum bai bi wasu matakai domin tserewa cigaba da aikata istimna'i ba, to babu wani magani da zai yi tasiri akan wannan matsalar da yake fama da ita ba. Waɗannan matakan sune kamar haka;

Dole ne mai son rabuwa ko kuma waraka daga cuta ko lalurar istimna'i su nisanta kansu daga labaru irin na batsa, hotuna irin na batsa, tunani da zantuttuka na batsa, kai da duk wani abu da zai iya motsa musu sha'awa da kuma wannan urge din na yin istimna'i. Wannan yana shafar tunanin mutum ta yadda zai siffata yadda yake tunani da aiki a cikin al'umma gaba ɗaya. 

Dole ne mai son rabuwa ko kuma waraka daga cuta ko lalurar istimna'i su nisanta kansu daga kallon blue film watau bf da sauran ire iren bidiyoyi da neman gidajen yanar gizo waɗanda za su iya dawo da kai cikin wannan tunanin. 

Dole ne mai son rabuwa ko kuma waraka daga cuta ko lalurar istimna'i su nisanta kansu daga yawan tunanin jima'i ko kallon tsiraici na mace idan ya kasance namiji ko kuma tsiraicin namiji idan ta kasance mace. 

Dole ne mai son rabuwa ko kuma waraka daga cuta ko lalurar istimna'i suyi kokari su samu wani abu da zasu rika yi wanda zai dauke musu hankali daga wancan tunane tunane masu tsanani da suke fadawa akan istimna'i. 

Maganin istimna'i 

Idan muka zo ɓangaren maganin istimna'i kuma, a nan ma kafin na kai ga yin bayanin magunguna akwai wasu hanyoyi da mutum zai jiɓanta wanda zasu matuƙar taimakawa wurin ganin an nisanta kai daga wannan mummuna kuma gagarumar matsala ta istimna'i. Wasu daga cikin hanyoyin sun hadar da; yawaita yin azumin nafila, ƙauracewa kallon hotunan batsa, ƙauracewa shafukan yanar gizo masu nuna tsaraici, kauracewa kallon mace irin na sha’awa, haka kuma mace ta dai na yiwa namiji kallo na sha'awa, cire rai da son kwanciya da mace ko namiji, a dena kaɗaita ku kaɗai a ɗaki

ba abin da ake yi, a samu a rika yin wani abu da ban da za'a shagalta dashi, a kuma kudurce a rai cewa ana son denawa, ana yawan yin azkar da karatun Alqur’an Mai Girma. 

Maganin istimna'i na gargajiya 

A cikin sahihan abubuwan da suke kwantarwa ko kuma rage tasowar sha'awa a jikin dan adam sun hadar da;

- citta (ginger) 

- waken suya (soya beans) 

- lemon zaƙi orange da cranberry

- lemon tsami

- kanwa (potash) 

- tsamiya (tamarind) 

Ginger

An san citta a matsayin maganin antioxidant mai tasiri. Kuyu amfani da cakuɗa citta ginger da zuma a kullum yana inganta zagayawan jini kuma zai tabbatar da kai daga juriya ga jarabar al'aura watau masturbation. Ku riƙa amfani da ginger a cikin abincinku na yau da kullum. 

Soya beans (Waken suya) 

Ku  riƙa amfani da waken soya kuma kuyi ƙoƙarin rage yawan caffeine daga abincin ku. Ƙara yawan abinci mai gina jiki kamar gyada. Haka kuma a yawaita cin koren kayan lambu, abincin teku watau seafood kuma a guji jan nama da kayan kiwo da yawa. A maimakon soda, sha ruwan 'ya'yan itace orange ko ruwan ƴaƴan itace cranberry kuma, ba shakka, sha gilashin ruwa 8-9 a kullum.

Shan ruwan cranberry da ruwan lemu a kowace rana. Zai samar da mahimman abubuwan gina jiki ga jikinku, don hakan na taimakawa wurin rage illar da ke tattare da istimna'i kamar gajiyar jiki, tunani, da jima'i.

Tsamiya

Idan aka jiɓanci amfani da tsamiya ta hanyar yin tsimi hakan na taimakawa kwarai wurin kwantar da tasowar sha'awar da zata iya kaiwa ga yin istimna'i. Da yake itama tsamiya cike take da sinadaran anti oxidant hakan yasa take taimakawa kwarai wajen rage urge watau tunkudowar sha'awa. 

Kanwa 

Kanwa kuwa koda ban lissafo ta a cikin kayan cima ko na amfanin gida ba wadanda suke kwantar da sha'awar dan adam, to nasan kun san tana da wannan amfani. Saboda haka a duk sanda aka ji an fara jin alamomin ana son yin istimna'i a gaggauta jiƙa kanwa a kada ta a cikin ruwa a shanye tana kwantar da tasowar sha'awa mai ƙarfi hakan zai taimaka muku wajen rage wannan tunkudowar sha'awar da jarrabar gaba ɗaya. 

Lemon tsami shima kamar kanwa ne ko yaya aka dan matsa ruwan sa a baki ana haɗiya ana samun sauki duk irin alamomin da za'a ji ko kuma halin da za'a tsinci kai a ciki.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post