Malama Juwairiyya maganin Sanyi

Jawabi daga malama Juwairiyya na maganin sanyi

Wannan kuma bayani ne daga babbar Malama  Juwairiyya na maganin sanyi (infection), Hajiya ko uwargida zaku iya gwadawa domin samun sauƙi akan cutar sanyi.

Malama Juwairiyya maganin sanyi

Menene cutar Sanyi ?

Menene yake kawo wannan matsala ta sanyi ? Abubuwa da dama yana kawo shi. Kamar yadda muka sani Allah (SWT) Ya halicci ɗan adam da garkuwar jiki, wannan garkuwar jikin yana tafiya ne tare da irin abincin da ɗan adam yake ci. Kamar yadda ake faɗa misali ace abinci mai gina jiki kamar balance diet. Duk lokacin da mutum ya samu abinci mai gina jiki zai ji jikinsa ya ginu, haka kuma idan aka samu naƙasu wurin abincin nan to tabbas a jiki ma zai samu naƙasu.

To amma abinda ake fuskanta na daga matsaloli gabas da yamma kudu da arewa, mutane basa tsayawa suji su kuma fahimci bayanai daga masana halayyar jikin ɗan adam 

aji bayani na irin abincin da ɗan adam yake ci, komai aka samu a afa, haka kuma bama son motsa jiki, bama son yin abubuwa da dama wanda wannan yana daga cikin abinda yasa muke samun cututtuka a jiki.

To kamar mu musulmai ya kamata mu sani cewa Annabi Muhammad (SAW) ya koya mana kamar yanke farce kowace juma'a, wannan yana koya mana tsaftar hannaye kenan, ya koya mana, ya koyar damu cire gashin hammata dana matse matsi, kar mutum ya zauna har tsahon kwana arba'in bai cire ba wannan yana koya mana tsaftar jikin mutum. Haka kuma ya koya mana idan mutum zai shiga bayan gida yayi addu'a saboda akwai miyagun aljanu munana a cikin bayan gidan. Idan mutum yayi fitsari ko yayi bayan gari mutum zai numfasa yayi sarki ya wanke sannan ya wanke hannayensa da sabulu ko omo ko da irin su hand wash ko toka ko ƙasa saboda a cire wannan dattin. 

To wannan yanayin yana nuna mana tsafta musulunci ne kuma tsafta cikon musulunci ce babu yadda za'ai mutum ya zauna babu tsafta kuma ya zama cikakken musulmi. To magana ta wannan sanyi sanyi da ake faɗa abubuwa da dama cikin abinda yake kawo shi musamman ga mu mata, mahaifar mu a buɗe take kamar yadda akace gaba ɗaya jikin mace al'aura ce, muna ganin ƙafar mu a buɗe take to hakan yana da link da mahaifar mu, to link ɗin nan da yake dashi da mahaifar mu kamar yadda Allah (SWT) Ya halicce mu al'aurar mu a buɗe ne, zamu je muyi fitsari wani lokacin ma tsarkin ba mai kyau ba, mace za'a samu wata ma bata cire gashin matse matsinta, yazo ya haɗu, wata macen zata yi sati bata canza pant ba, wata za'a samu pant ɗin mai duhu ne ga datti za'a ga irin wannan yana accumulating ne kuma duk dauɗar nan tana koma mata ne. 

Sa'annan ita al'aurar ƴa mace yana da bacteria masu kyau da marasa kyau, wannan bacteria da ake faɗa sau tarin yawa idan aka samu sabulu mai chemical da abubuwa masu chemical muna wanke al'aurar mu dashi yana ɗauke bacteria ɗin mai kyau shi karan kansa, idan kuma ya ɗauke bacteria mai kyau ɗin zaiyi accumulating cuta ne ya aika dashi cikin mahaifa. Idan ta aika dashi cikin mahaifa wannan zai bawa mahaifa wata cuta ta musamman. To irin waɗannan cututtukan zasu fara ne kamar da ƙaiƙayin gaba, wanda ƙaiƙayin gaba yana iya faruwa idan har kikai aski baki san abinda ya kamata kiyi amfani dashi ba. Shine kullu yaumin muna magana idan mace kamar tayi aski zata yi amfani da kamar ko tumatur ɗanye ko cucumber zata iya amfani dashi to gogawa wurin ko lemon tsami duk da dai wannan da ɗan zafi amma cikin ikon Allah ko kuma tayi amfani da apple salad vinegar zai ciccire wannan dattin dake gurin kuma ba zata samu ƙaiƙayin gaba da yake faruwa a sama ba, sa'annan wannan baƙi baƙin da yake faruwa a matse matsinta zai yi clearing da ikon Allah. 

To a cikin wannan yanayi idan har aka je wani lokaci za'a samu mace tana yawan tafiya babu takalmi. Yawan wannan tafiyar nan babu takalmi wannan sanyi da yake ratsata yana tafiya ne har cikin mahaifa bayan nan kuma za'a samu wata tana irin dariyar nan barkatai wacce Annabi (SAW) ya hana. Irin wannan dariyar tana yiwa mahaifar ƴa mace illa. Bayan nan akwai abubuwa da dama da idan munga canji a cikin jikin mu, muyi amfani da abubuwan daya kamata mu taimakawa kanmu misalin kamar irin magarya mun san magarya ita karan kanta tana da kumfa, magarya abu ne wanda mutum zaiyi amfani da ita wajen tsaftace jikinsa, mun san su lalle suna daga cikin abubuwan da mutum zai iya tsaftace jikinsa da shi.

Babbar malamar dai wato malama Juwairiyya akan maganin sanyi ta ƙara da cewa; 

Amma ya kamata mu sani idan ance maka ga abinda ya kamata kayi amfani dashi mutum ya nemi measurement ɗin daya kamata yayi amfani dashi ba wai kawai mutum ya rika afka duk abinda aka ce a social media ko kuma abinda aka faɗa baka san tabbacin gaskiyar sa ba ai ta amfani dashi har yazo ya zame wa mutane matsala. To wannan ya kamata ku lura. 

Sa'annan yana daga cikin matsalar da ake fuskanta, matsala kuma babba, shine ana aurar da yara wani lokaci sai a samu anje an koro su daga gidan aure. Wannan abin da muke faɗa na ciwon sanyin nan sau tarin yawa wallahi wata za'a aurar da ita bata taɓa yin iskanci ko lalata ba sai aga an kaita gidan aure sai aga an same ta a buɗe saboda carelessness ɗin iyaye ba a koya mata komai banda aikin dubulan da alkaki da za'a kai yarinya da shi ana jere, ba'a koyar da ita tsaftar jikinta ba, ba'a nutsar da ita ta zauna kwayoyin halittar jikinta sun samu nutsuwa ba, haka zata je bazar bazar to daga nan za'a samu matsala.

Shi wannan yanayi na ciwon sanyi yana da wasu abubuwa na siddabaru daban, jiki ya bambanta wasu za'a samu wata za tayi ƙaiƙayin, wata za tayi fitar da ruwan wata kuma ba za tayi ba a maimakon haka zai zauna mata ne taji wani abu ya dunƙulu kamar wani kwallo yana mata yawo a ƙasan mara.  Wata za taji gefen cikinta na dama ko na hagu yana ciwo, wata ciwon baya, wata ciwon ƙafa, wata warin baki da idan yayi yawa alaƙa al'aura da bakin mace, wanda irin wannan ne wanda idan mutum yayi magana za'a ji bakin sa yana wari, ai ta neman maganin warin baki a rasa, to wannan dattin na ƙasa shine yake fitowa. 

Faso wanda muke gani a ƙafar mace ko ta namiji, faso ya fashe yana daga cikin abinda yake komawa cikin jikin mutum yayi masa illa. Rashin wanka akan lokaci, rashin aski akan lokaci, rashin brush na baki, dukkan dattin nan yana komawa ne yaje ya zaunawa mutum kuma yana da illa a cikin jikin ɗan adam. Wani lokacin idan ana mu'amala za'a riƙa jin kamar ana watsa yaji, wani lokacin mace ta riƙa fitar da iska daga gabanta, wani lokaci ba wannan ba, za'a ga bata da sha'awa ko bashi da sha'awa, wani lokacin kuma ƙuraje suna fita, wani lokacin wani ƙurji haka mai ƙarfi zai fito idan yayi ƙaiƙayi ya mutu wani ya sake fitowa haka zai ta bibiya. 

Wani lokacin za'a ga mace ta buɗe haka, al'aura ta zama kamar tumatur, namiji kuma za'a ga girman al' aurarsa yana raguwa, bayan yana raguwa kuma za'a ga idan da farko yana iya mu'amala ta mintuna sha biyar, ashirin ko talatin sai ya dawo ya zamana baya iya yin komai, yazo ya fara baya baya. 

Daga nan shima sai ya fara fitar da wani irin discharge wani lokacin ma har da jini yana fita. Al'aurarsa na ƙanƙancewa ana ta samun matsala to irin wannan fa duk sanyi ne, a irin wannan yanayin abinda ya dace ayi shine a nemi masana su bada magani, amma a maimakon haka sai kuga an zauna ance a'a ga masu dauri. Daga nan idan aka fara shan irin jiƙe jiƙen nan kuma idan akai rashin sa'a sai a kamu da ciwon hanta ko ciwon ƙoda, kunga an samu wasu matsalolin daban. 

Wani lokacin kuma za kuga mutum yana da ƴaƴa sai ya kasance ya sake ƙara aure matar daya aura tazo ata uku ko ta huɗu. Idan aka shekara ko aka shekara biyu, uku matar bata haihu ba sai yace taje asibiti ita kaɗai domin shi yana haihuwa, abinda baka sani ba shifa sanyi babu abinda ya kyale, domin kuwa sanyi yana taɓa lafiyar sperm count kaga koda ana haihuwa da farko sai ya zamana haihuwar ma ta ɗauke. Saboda haka abinda ya kamata duk lokacin da wata matsala ta taso kamata yayi kada namiji ya bar matarsa ita kaɗai yace shi bashi da matsala lafiyar sa lau, kamata yayi a gudu tare a tsira tare. 

Da yawa daga ire iren matsaloli na sanyi da suka danganci ma'aurata sai a kiyaye ta hanyar yin tsafta da neman sahihan magunguna a kuma kiyaye lafiyar jiki sosai.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post