Hirar soyayya mai ban dariya

Hirar soyayya mai ban dariya daga masoya;

Nasan fuska zata murmusa ko kaɗan ne akan labarin hirar soyayya mai ban dariya, wanda muka zo dashi domin jin daɗin masu karatu. Wannan shafi namu zaka iya samun duk abinda kake so, kama daga faɗakarwa, ilmantarwa har ma da nishadantarwa.

Hirar soyayya mai ban dariya

Aliyu saurayi ne kyakkyawan gaske, domin sune samarin da ake cewa Black beauty, wato da kin ganshi zaki san cewa eh lallai wannan ba ɗan wahala bane, a yanzu haka dai shekarun Aliyu ba zasu haura ashirin da biyar ba, amma idan kika ganshi sai kice ya kai ashirin da takwas haka koma da tara, sakamakon wani kyakkyawan gemu daya ajje, gamida isashhiyar ƙasumba, dogo ne sannan akwai shi da yar ƙaramar ƙiba wanda da kin ganshi sak kamarsu ɗaya dame karatun nan. Hmm.

Wata rana da yammaci, Aliyu ya ɗau wankan yamma ya fito bakin layi zuwa wajen abokinsa Usman, kamar yadda suka saba suka zauna a gefen titi domin yin labaran duniyarsu. Nan fa Usman ke gayawa Aliyu, ai ɗazu mun haɗu da mutuniyarka Fatima, waini yarinyar nan ta kalli tsabar idona tace wai tana sona saboda bata da kunya.

Aliyu tuntsirewa da dariya yayi yace "a'a to menene a ciki ba yar gidan wan abbanku bace, Usman ya kalleshi yace " to ni wallahi bana sonta " kaima kasan ta rainani, harfa hararata take idan ina yi mata magana, kuma saita dawo tace tana sona. Kaji dashi cewar Aliyu.

Ahh!!! Aliyu ne ya saki wani ɗan ƙaramin ƙara wanda ya razana Usman, har ya nemi ya tuntsira yana faɗin malam mene haka?.

Ai Usman bai gama rufe baki ba, shima ya gano abinda Aliyu ya gani. Kai ! malam ! wata kyakkyawar yarinya ce son kowa ƙin wanda ya rasa take ƙoƙarin wucewa, yarinya ce fara jajir da ita, daka ganta kaga fulanin Adamawa, ga wani dogon wuyanta daɗin kallo. Tana wani tafiya bata son taka ƙasa, kai malam ubangijin Musa da Haruna yayi halitta a wajen nan, kai ko ni da nake ɗaukar hoton abinda ke faruwa saida yawuna ya tsinke, saboda yarinyar nan tanada tsayayyun kayan Fulani a ƙirjinta ga mazaunai kamar ita tayi su, ga jikinta tamkar fulawa da aka sawa ruwa. 

Ɗanya sharaf da ita, hancinta kuwa masha Allah wannan shi ake kira da zuwet ɗin, domin tsini ke dashi uwa biro. Haba wa! nan fa Aliyu ya kiɗime ya nemi ya haukace domin baisan lokacin daya bi bayan wannan cikakkiyar budurwa yana kallonta gashi nan ya saki baki galala, gaskiya ya bayar da maza wallahi. 

Tafiya kawai yake ko kallon gabansa baya yi, haba wa! ai ji kake rikicaa!! ya faɗa kwata, ahhhhhhh!!  ihunsa ne yasa wannan budurwa ta waigo, ai kuwa ta juyowa ta hau wata shegiyar dariya Hhhh. hada tafa hannu sannan saiga Usman yana yayinda shima dariyar yake -hh ya miƙa masa hannu cikin kunya da murmushin yaƙe Aliyu ya fito. Allah ma ya taimakeshi da wani isasshen ruwa a cikin wannan kwata, a hakan fa bae daina kallonta ba, har dai wannan budurwa ta fahimci komai yanzu. 

Itama ta ɓangarenta ya mata, amma bata nuna hakan ba ko kaɗan. Aliyu yayi ta maza yace " yan'mata gaskiya ba wani boye boye wallahi ammin ' ta kalleshi ta ɓata rai. Nan fa Aliyu yaji gabansa ya faɗi, cewa tayi haba malam kaji da lafiyarka mana, ba kaga abinda ya sameka ba, murmushi yayi sannan karki damu da wannan duka a kanki ne. 

Sai kuma tayi dariya tace a kaina kuma? haka kawai zaka jiwa kanka ciwo. Nan dai wata sabuwar hira ta ɓarke tsakaninsu. har ya rakata ta hau abun hawa domin komawa unguwarsu. Tun daga wannan rana soyayya ta kullu tsakanin Aliyu da Ameera inda suka cigaba da soyayya irinta masoya masu kaunar juna.

Abinda yasa na sawa wannan labari hirar soyayya mai ban dariya, shine akwai wata rana da Usman yazo gidansu Aliyu domin raka shi ganin masoyiyarsa wata kyakkyawar yarinya itama mai suna Salma, Usman yana matuƙar son wannan yarinya, amma matsalar tana yi masa kwarjini da yawa, domin idan yaje gunta ko hirar soyayya da yawa baya iya yi, musamman idan ta tsare shi da kallo da kyakkyawar fuskantarta sai kaga har wani tsuma yake, bayan sun isa, Usman ya kira wayanta domin gaya mata sun ƙara so.

hirar soyayya mai ban dariya kenan, bayan tazo suka gaisa da Aliyu sannan ya tashi ya basu waje domin su sarara, Nan fa Usman ya juya baya domin ko kallonta ya kasa, cike da farinciki Ameera tace " Ya agwalumar zuciyata ya naga kyankyaso a bayanka " ah! haba! wayyo da gaske !!! nan fa ya nemi ya cire riga, saita soma cewa Wallahi da wasa nake, tana yi masa dariya, sai ya juyo ya kalleta yana wani faɗin nifa jarumi ne, kawai so nake naga kinyi dariya shiyasa nayi haka, cewa tayi Hmm, babyna ai kuwa nayi. 

Ashe ashe !! mutuminka tsoron kyankyaso ne dashi uwa ɓera yaga mage, can suna cikin hira sai kawai aka ɗauke wuta, waje yayi duhu, kuma ba abun su kunna fitilar waya ba, suka ci-gaba da fafatawa hirar soyayyarsu. Haba wa! ba sai irin zafi ya ɗan koro wasu tawagar kyankyasu ba, suna wannan firrr!! ɗin a sama da fika-fikai sai kuwa wani ya hau kan Usman, Kutmelesi ahhh!!!! wallahi yanda kasan tashin duniya haka ya soma ƙara wayyo wayyo zan mutu !! Ameera zan mutu har faduwa yayi. 

Ameera ta haska kansa ganin kyankyaso yasa ta soma dariya hhhhhh. yayinda Aliyu ya kawo ɗauki suka taru kuwa suka dinga yiwa Usman dariya. Aliyu cewa yayi daga zuwa hirar soyayya sai kuma abu ya koma mai ban dariya. Hhh.

Tun daga wannan rana, Usman bai ƙara tsayawa idan aka ɗauke wuta, anan muka zo karshen wannan gajeran labari, sai anjima.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post