Maganin mallakar saurayi na islamic

Maganin mallakar saurayi na Islamic

A cikin wannan rubutun yaku makaranta idan kuna tare dani daga farkon sa har ƙarshe, zamu tattauna bayanai akan maganin mallakar saurayi na islamic wato a mahanga ta musulunci. 

Maganin mallakar saurayi na Islamic

Da yake wannan rubutun zai keɓantu ne akan maganin mallakar iya na musulunci to ya kamata mu tuna cewa a musulunce dai mun sani kuma mun yadda cewar bamu da wani magani sama da addu'a. Idan kuwa haka ne, to anan a cikin wannan rubutun zamu yi bayanan addu'o'in da zaki jiɓanci yi domin samun mallakar wannan saurayin da kike ta dakon soyayyar sa. 

Kafin na tsunduma tsundum cikin bayanin abinda wannan rubutun zai ƙunsa watau maganin mallakar saurayi. Zanyi cikakken bayani akan menene wannan mallakar ne, ko kuma me wannan kallama ta mallaka take nufi ne? 

Menene mallaka?

Idan yau aka wayi gari aka ce wance fa ta mallake wane ko kuma idan mace tana neman wani magani ko laƙani ko surƙulle na mallakar namiji to wannan kalmar ta mallaka tana fa nufin hankalin sa, tunanin sa, kai harta hayyacin sa watau conciousness ɗinsa kenan a turance duka zasu dawo abin sarrafawar kine wannan bayanin a dan taƙaice ne kenan. Idan yau aka ce, ko kuma ke da kanki in kin san kin mallake wani namiji to nasan kin kwana da sanin cewa kin gama dashi ma'ana dai anan kinyi possessing ɗinsa. 

Idan har ya zamana an samo kan mutum ta haka kuwa, to mutum bashi da wani kataɓus kenan sai fa abinda wanda ta mallake shin nan take so ayi shi ne kawai abinda za'a yi. Mutumin da duk aka mallake bashi da wani tunanin kansa ko na ra'ayinsa ko kuma na wani abu da yake ganin ya dace sai wanda aka gindaya masa ko kuma aka sharɗanta masa. Wannan a taƙaice shine mallaka. Wannan bayanin na kawo muku shine makaranta domin idan kun kasance ko kuma kun zamanto daga cikin masu son mallakar wani to kusan cikin irin tudun da kuke sin hawa. Wannan kenan. 

Don me ake neman maganin mallaka?

Shi dai maganin mallaka wanda ake ta yawan nema domin a mallake wani, mataye ko kuma mutane da yawa suna yine saboda dalilansu mabambanta. Watau dai dalili ko kuma abinda zaisa waccan macen ta nemi maganin mallaka ba lallai ya zama ɗaya da dalilin ko kuma abinda waccan macen zata hango ta kuma tsaya tsayin daka domin mallake wani namiji ba. Wata macen zata nemi maganin mallaka ne ta kuma yi amfani dashi ta mallake wani namiji domin kawai tana sonsa. Wannan son nasa da take yi za'a iya kai wani mataki da bata son ko kuma ƙaunar alakar sa da kowace irin mace koda kuwa maharramar sa ce wacce babu maganar soyayya ko kuma aure a tsakaninsu. Idan ta mallakeshi sai wacce tayi umarnin ya kula zai iya kulawa.

Wata macen kuwa zata nemo maganin mallaka ne ta kuma mallake namiji domin ya zamana ita take iko da duk wani abin da ya mallaka. Kaga kenan a lissafin ta idan ya mallaka dukiya ita kuma sai ta mallakeshi a matsayin sa na mamallakin wanana dukiyar. Idan tayi haka to babu wanda ya isa ya kawo mata cikas kenan domin wannan shine lissafin ta. 

Bayanin maganin mallakar saurayi na Islamic daga malamai; 

Maganin mallakar saurayi da mata suke amfani dashi domin mallakar  saurayi in dai a musulunci ne kamar yadda na bayyana a sama to nau'i nau'i ne amma na addu'o'i. Waɗannan nau'o'in sun haɗar da;

-Rubutun aya ko ayoyi waɗanda za'a ninke a layance a dɗɗinke ma'ana dai anyi laya kenan. 

-Rubutun sha, watau ayi rubutun allo shima mai ɗauke da ayoyi ko kuma wata aya a wanke a sha. 

-Rubutun hatimi

-Addu'o'i ko wuridai da mace zata jibɓanci yi duk domin biyan bukata.

-Maganin mallakar saurayi na Islamic wanda ake haɗawa;

-Rubutun aya ko ayoyi waɗanda za'a ninke a layance a ɗinke ma'ana dai anyi laya kenan. 

Laya wacce a turance ake kira da talisman, wani ɗan ƙaramin dunƙulallen abune wanda a cikinsa yake ƙunshe da farar takarda wacce aka ninke aka kuma saka fata aka ɗinke ta. Ɗinkin_da_za'a_yiwa_wannan_farar_takardar_kuwa_ana_amfani_ne_da_jemammiyar_fata_wacce_baduku_zaiyi_amfani_da_ita ya_ɗinke. 

Amfani da laya ko layu daɗaɗɗiyar hanyar asararu ce. Laya ta kasance abar da aka jima ana amfani da ita wajen neman taimako kala kala kuma a ire iren taimakon da akeyi da laya sun hadar da na mallaka ko kuma neman sa'a ta wani abu, kai harta mafarauta da sauran hatsabibai suka nemu layoyi da guraye domin shirya kansu kafin fita fagen fama. 

Amfani da laya domin yin magani rashin lafiya kamar irin su ciwon kai ko neman tsari ko kuma karyar sihiri dukkansu an dade ko nace an jima ana amfani dasu. To haka kuma mata su kan sa ayi musu laya mai ɗauke da aya ko ayoyi ko kuma wasu wuridai ko hatimai da ake tunanin suna da tasirin samun farin jini. Idan aka yi wannan layar wasu matan za'a ga suna saka layar ne a ƙarƙashin pillow misali su riƙa kwantawa akai, wasu kuma sukan saka layar ne a jikin pin su ɗaure akan su wasu ma suna iya saka maɗauri su ɗaure ta a hannayensu. Haka kuma akwai wasu hanyoyin yadda ake saka layu a jiki waɗanda ba'a ambata ba. 

-Rubutun sha, watau ayi rubutun allo shima mai dauke da ayoyi ko kuma wata aya a wanke a sha. 

A wannan hanyar idan mace za tayi amfani da ita, za'a bata wata aya ne watau verse ko kuma wasu ayoyi waɗanda za ake rubuta mata a allo a wanke ta sha, misali kuma za'a iya cewa to shafa a fuskarta koma har da jikinta. Anan ana amfani ne da akai imanin suna da tasirin saka farin jini. Ita macen zata riƙa shan wannan rubutun ne tare da wannan niyyar. Sau ɗaya shi irin wannan rubutun akan bada adadi ne, misali za'a iya cewa a rubuta aya kafa dubu goma da ɗaya har na tsawon kwanaki kaza, haka kuma za'a iya cewa idan anyi rubutun za'a wanke shi da ruwan zam zam a kuma saka masa zuma. Waɗannan duka misalai ne na yadda ake amfani da kuma gindaya sharudda na wanke rubutun allon da kuma shansa. 

Wannan nau'in na maganin mallaka dai ya jima ko kuma nace ya dade ana amfani dashi watau abin nufi shine wannan hanyar dadaddiyar hanyar samar da maganin mallaka ce. Haka kuma hanyoyin da ake bi ake kuma samar dasu suna da dimbin yawa. Duk yacce mutum ya kai ga sanin ire iren hanyoyi kamar su ko masu kamanceceniya dasu to sai dai kawai ya zamana mutum ya san iya irin wanda ya sani amma idan da za'a bayyanawa mutum yawan su, to kuwa da zai tabbatar iya ilimin sa a wanna fannin bai ko kai rabin karamin cokali ba. 

Maganin mallaka na hatimi;

Amfani da hatimi itama tana da nata tasirin kwarai da aniya. Haka kuma dadaddiyar hanya ce wacce aka jima ana amfani da ita wurin samar da asararu watau sirrika kala kala wadanda a cikinsu sun hadar harda na mallaka. 

Hatimi a wannan fuskar, watau tayin maganin mallakar saurayi kusan kala biyu ne. Na farko akwai hatimi da za'a iya yi a takarda a ninke ta a kuma saka fata a layance ta domin amfanin mace ko kuma ayi wannan hatimin akan allo ta riƙa wankewa tana sha. Hanya ta biyu kuma shine mace zata iya bayarwa a wurin masu ƙirar zobe musamman zoben azurfa watau bronze. Su masu ƙirar idan aka basu hoton yadda hatimin yake zasu ƙera mata su kuma zana mata hatimin akan wannan zoben ita kuma sai tayi amfani da zoben. 

-Addu'o'i ko wuridai da mace zata jibanci yi duk domin biyan bukata.

Babu abinda aka fi saurin bayarwa a wurin neman taimako na wata bukata kamar addu'o'i wuridai. A wannan hanyar kuma yawanci mata sukan tambayi malami ko malamansu ire iren addu'o'in da zasu keyi domin samun soyayya ko mallakar wani namiji. Akan basu addu'o'i da wuridai da zasu jiɓanci yi kuma ana faɗa musu irin adadin yadda zasu ke yin addu'ar ko kuma wuridin domin biyan buƙatar su. 

-Sirrin ayoyi;

"Wa Alƙaitu Alaika Mahabbatan Minni"

Suna a sama sunan wanda za'a mallaka kuma a kasa kullum a rubuta ƙafa bakwai sannan a wanke asha kwana bakwai.

Maganin mallaka wanda mace zata iya yiwa namiji, kuma da kinyi kin gama dashi sai dai mom ɗinsa watau uwa tasa ta haifi wani domin shi dai wannan sai yadda kika yi dashi

Za'a rubuta hatimi sannan sai a rubuta wannan ayar;

"Wa l'au nasha'u laɗamasna ala a'ayunihim fastabaqussiradha fa'anna yubsirun"

Sai kuma a rubuta sunan wanda ake son mallaka a tsakiyar hatimin sannan za'a yi haka ne tsawon sati ɗaya kuma asha. 

Akwai hatimi da za'a zana sannan a rubuta suratul ikhlas da kuma aya ta talatin a suratul Yusuf da kuma 

Wa Alkaitu Alaika Mahabbatan Minni

 Daga nana kuma sai a saka sunan wanda ake so a mallaka a tsakiyar hatimin za'a kuma rika wankewa ana sha tsawon kwana bakwai watau mako daya kenan 

-Maganin mallakar saurayi na islamic na haɗi

A cikin irin waɗannan nau'in magungunan mallakar da ake amfani dasu ana samar dasu ne ta haɗa kayayyakin amfani na yau da kullum kamar irin su;

-magarya; wanda ya haɗar da yayanta, ganyen ta, saiwar ta da kuma sassaken ta. 

-aduwa; wanda ya haɗar da yayanta, ganyen ta, saiwar ta da kuma sassaken ta. 

-Lemon tsami

-man zaitun; wanda ya haɗar da yayan sa, ganyen sa da duk wani abu daya dangance shi. 

Waɗannan misalan dana kawo na yayan itatuwa da kuma wasu da yawa ma da ban ambata ba a cikin wannan rubutun, ana sarrafa sune misali ta hanyar yin rubutun wasu ayoyi ko hatimai a jikin ganyen su ko yayan itacen nasu. Kuma itama wannan hanyar dai ana yin ta ne kamar misalin yadda akeyi a rubutun sha na ayoyi misali kamar ayi rubutu na asha na tsawon kwana bakwai haka. 

Kamar misali idan aka samu lemon tsami aka kayyade iya adadin wanda za ayi aiki dashi, misali za'a iya cewa a samo lemon tsami koraye guda talatin ko kuma ace lemon tsami yalaye masu ruwa guda talatin sai a rika rubutu a jikinsu kafin a yanka a kuma yi amfani da ruwan ciki har na tsawon kwana talatin din nan.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post