Kalmomin hausa masu wahala post
Ba tareda ɓata lokaci ba wannan rubutu namu munyi shine akan wasu kalmomin Hausa masu wahala, gamida azuzuwan kalmomin Hausa, ire iren gabar Hausa, kalmomi masu gaba huɗu, biyar, shida. Da dai sauransu.
Wasu daga cikin kalmomi masu wahalar:
-Galauniya
-Gansheƙa
-Karakaina
-Katankatana
-Kankane
-Ararraɓi
-Dangarama
-Dumɓaru
-Baubawa
-Kadarko
-Gunduma
-Sulkumi
-Salka
-Takanɗa
-Bambazo
-Kintace
-Shirinya
-Kwarmato
-Kudaku
-Shanshani
-Wushirya
-Kumama
-Tsangaya
-Gajimare
-Lolloki
-Ruguntsumi
-Walanƙeluwa
-Walagigi
-Kududdufi
-Tarzoma
-Borin turke
-Gumurzu
-Uƙuba
-Matsefata
-Dumfama
-Yakana
-Lugude
-Zillewa
-Kainuwa
-Annakiya
-Umbola
-Alkuki
-Dirshan
-Ƙulafuci
-Bulayi
-Tumɓele
-Marisa
-Kufai
-Jarfa
-Jalala
-Ƙawalwalniya
-Gantsarwa
-Ganɗoki
Azuzuwan Kalmomin Hausa:
Kamar yadda kowane irin harshe a duniya masu amfani dashi kan rarraba kalmomin wannan harshen nasu zuwa gida gida ko kuma aji aji to haka ma a yaren hausa akwai azuzuwan kalmomin. Masana ko kuma nace manazarta sun saɓa ko kuma ma iya cewa sun samu saɓani dangane da adadin azuzuwan kalmomin, saboda haka a wannan rubutun dai zan zaɓo guda shida da mafiya rinjaye suka yi tarayya wajen zayyano su. Ma'ana kenan su wadannan ajujuwan babu sabani ko kuma zamu iya cewa sabanin masanan ko kuma manazartan ƙalilan ne akan su.
Ga su kamar haka:
Suna ko Sunaye (Noun)
Walikin Suna (Pronoun)
Aikatau (Verb)
Bayanau (Adverb)
Siffa ko Siffatau (Adjective)
Mahaɗi (Conjuction)
Azuzuwan kalmomi ma'anarsa shine shi ne rarraba kalmomin harshen hausa zuwa aji-aji bisa la’akari da irin aikin da kalmar take yi ko kuma ma'anar da ita kalmar take ɗauke da ita. A cikin wannan rubutun dai nayi amfani da wannan suna watau ajin kalmomi domin ita tafi dacewa da yin bayani ko kuma misali akan rabe raben kalmomin da kuma dalilin da yasa ake rarraba su zuwa waɗannan azuzuwan da na lissafo a sama.
A cikin wannan rubutun na azuzuwan kalmomi kuma kamar yadda aka lissafo azuzuwa shida da suka haɗa da suna, wakilin suna, aikatau, bayanau, siffa, da mahaɗi.
Sunana ko Sunaye (Noun)
Suna shine ko kuma sune kalmomi da mutum yake amsawa a matsayin sunansa haka ma dabba kowace iri, kowane guri yana da suna da kuma sauran abubuwa.
Misali;
Audi sunan mutum ne
Zaki sunan dabba ne
Abuja sunan wuri ne
Kwando sunan wani abun amfani ne.
Waɗannan duka kalmomin sun faɗo ne a cikin ajin sunaye.
Walikin Suna (Pronoun)
Kamar yadda sunan yake watau wakili, to shi walilin sunan yana wakiltar suna ne. Misalin wakilan sunaye sun haɗar da; mu, su, kai, ke, ni, ita, shi da wasu. Waɗannan duka suna wakiltar suna ne a cikin magana ko jumla watau sentence.
Aikatau (Verb)
Shima wannan ajin na kalma yana bayani ne akan duk wani aiki da suna yake yi a cikin jimla. Misalin aikatau a jimla shine;
Audu ya gudu.. A wannan jimlar kalmar 'gudu' aikatau ce saboda shine aikin da Audu yayi.
Siffa ko Siffatau (Adjective)
Wannan ajin kalmar watau siffatau yana siffanta suna ne a cikin jimla.
Misali; Mariya kyakkyawar yarinya ce
A wannan jimlar kalmar 'kyakkyawar' siffatau ce saboda tana siffanta wacece Mariya.
Ire iren gabar kalmomin hausa:
Gaɓa tana nufin wani yanki na kalma wadda ake gina ta ta hanyar haɗa baƙi da wasali, watau (vowel and consonant) kenan a turance. Adadin gaɓoɓin da ke cikin kalma su ke bayyana irin tsawo ko gajartar kalma. Ma sana da manazarta harshen hausa sun haɗu a kan cewa; mafi gajartar kalmar Hausa ita ce mai gaɓa ɗaya kamar ni, ke, ku, shi, su, ita, ko sha; mafi tsawo kuma ita ce mai gaɓoɓi shida kamar sakwarkwatacciya.
Babu wata gaba a kalmomin hausa da suka dara daga shida, haka kuma babu ragi watau kasa da ɗaya.
Ga ire iren gabobin hausa kamar yadda masana da manazarta suka fayyace mana su kamar haka;
1- Baƙi da Wasali (Consonant + Vowel)
Wannan shine misalin farko a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wanda ake alamta shi da /BW/:
A wannan tsarin ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar haɗa baƙi da wasali a waje guda. Misali, B + A ya zama /BA/ kamar a cikin kalmar BABA /BA/BA/ abib aunawa a bisa ma’aunin /BW/BW/.
2- Wasali da Baƙi (Vowel + Consonant)
Wannan shine misali na biyu a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wanda ake alamtawa da /WB/: A wannan tsarin ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar saka wasali a farko sannan kuma baƙi ya biyo bayansa. Misali, A + L ya zama /AL/ wanda za mu iya samu a cikin kalmar ALLO /AL/LO/ abar aunawa a bisa ma’aunin /WB/BW/.
3- Baƙi da Wasali da Baƙi (Consonant +Vowel + Consonant)
Wannan shine misali na uku a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wanda ake alamatawa da /BWB/:
A wannan tsarin ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar saka baƙi da farko sannan kuma a yi masa wasali sai kuma a ƙara wani baƙin. Misali, D+A+N ya zama /DAN/ wanda za mu iya samu a cikin kalmar DANNAN /DAN/NAN/ abar aunawa a bisa ma’aunin /BWB/BWB/.
4- Baƙi, Baƙi da Wasali (Consonant + Consonant + Vowel)
Wannan shine misali na hudu a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wadda ake alamatawa da /BBW/: A wannan tsarin ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar saka baƙi da farko sannan a ƙara wani baƙi sai kuma a kawo wasali a ɗora musu daga ƙarshe. Misali, K + W + A ya zama /KWA/ wanda za mu iya samu a cikin kalmar KWAKWA /KWA/KWA/ abar aunawa a bisa ma’aunin /BBW/BBW/.
5- Baƙi, Wasali da Wasali (Consonant + Vowel +Vowel)
Wannan shine misali na biyar a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wadda ake alamatawa da /BWW/: A wannan tsarin ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar saka baƙi da farko sannan a kawo wassula guda biyu a raɓa masa. Misali, R + A + U ya zama /RAU/ wanda za mu iya samu a cikin kalmar MASARAUTA /MA/SA/RAU/TA/ abar aunawa bisa ma’aunin /BW/BW/BWW/BW/.
6- Wasali da Wasali (Vowel +Vowel)
Wannan shine misali na shida a ajujuwan gabobin kalmar hausa
wanda kai tsaye za a iya kira tagwayen wasulla ababen alamatawa da /WW/: A wannan tsari ana gina gaɓar hausa a kansa ta hanyar jera wassula guda biyu. Misali, A + U ya zama /AU/ wanda za mu iya samu a cikin kalmar AURE /AU/RE/ abar aunawa bisa ma’aunin /WW/BW/.
Kalmomi masu gaba hudu (four syllable words):
Kalmomin Hausa masu gaba huɗu a nan za mu iya samun kalmmomi kamar irin su tumfafiya, mahaukaci, alkantara, aunanniya da sauransu. Waɗanda za a iya auna su da ma’aunan /ma/hau/ka/ci/ /BW/BWW/BW/BW/, /tum/fa/fi/ya/ /BWB/BW/BW/BW/, /al/kan/ta/ra/ /WB/BWB/BW/BW/ da sauransu ababen gani a cikin jimlolin:
Mahaukaci ne yake kwana a bola.
Ana magani da tumfafiya.
Akwai unguwa Alkantara a Kano.
Misalan kalmomi masu gaba biyar:
A nan za mu iya samun kalmomi kamar irin su yarjejeniya, wargajajjiya, taɓarɓararre, bagargajiye, da sauransu. Ababen aunawa da ma’aunan /yar/je/je/ni/ya/ /BWB/BW/BW/BW/BW/; /war/ga/jaj/ji/ya/ /BWB/BW/BWB/BW/BW/; /ta/ɓar/ɓa/rar/re/, /BW/BWB/BW/BWB/BW/; /ba/gar/ga/ji/ye/. /BW/BWB/BW/BW/BW/;
Kalmomi masu gaba shida:
A nan za mu iya samun kalmomi kamar irin su cukurkuɗaɗɗiya, sukurkutacciya, wulaƙantacciya da sauransu. Ababen aunawa da ma’aunan /cu/kur/ku/ɗaɗ/ɗi/ya/, /BW/BWB/BW/BWB/BW/BW/; /su/kur/ku/tac/ci/ya/, /BW/BWB/BW/BWB/BW/BW/; /wu/la/ƙan/tac/ci/ya/, /BW/BW/BWB/BWB/BW/BW
Wasu daga cikin kalmomin turanci da fassarar Hausa:
Turn on- Kunnawa
Turn off- Kashewa
Get in - Shiga
Get out - Fita
Put on- Sakawa
Overlook - Kau da kai
Condolence - Ta'aziyya
Patience - Hakuri
Mourning - Jimami
Favour- Alfarma
Day - Rana
Week - Sati
Month - Wata
Year - Shekara
Black - Baƙi
White - Fari
Green - Kore
Blue - Shudi
Red - Ja
Launi - Kala
Diamond - Lu'u lu'u
Gold - Gwal
Bronze - Azurfa
Witness - Shaida
Judge - Alƙali
Foot - Diddige
Shoulder - Kafada
Scapula - Allon Kafada
Neck - Wuya
Knee - Guiwa
Fire- Wuta
Gun- Bindiga
State - Jiha
Joint - Mahadi
Block - Bulo
Stand - Tsayawa
Sand- Kasa
Sky - Sama
Bird - Tsuntsu
Orphan - maraya
Organization - ƙungiya
Progress - cigaba
Sin - zunubi
Luck - sa'a
Mackintosh - rigar ruwa
Must - dole
Marvelous - mai ban mamaki
Origin - asali/mafari
Medium - matsakaici
Ostentation - Mai fariya/mai Alfahari
Imputation - Zargi
Incest - Auren Haram
Incorrect - Ba dai dai ba
Incurable - ciwon da ba magani
Decency - jin kunya
Indecency - Fitsara
Limit - iyaka
Latch - sakata
Dirt - ƙazanta
Committee - Komiti
Compare - kwatanta
Complain - yin kara
Complete - karasa
Conference - Taron shawara
Condition - halin xama
Defense - Tsaro
Definite - tabbatacce
Detection - Bincike
Delay - Jinkiri
Delegate - Wakili
Delicious - Mai dadin ci
Delight - Murna
Delirium - Magagi
Demand - Neman buƙata
Demolish - Rushewa
Demon - Shaiɗan
Demotion - Ci baya
Dentist - likitan haƙori
Depart - Tashi
Deputy - Mataimaki
Descend - GangareRumor - Jita-Jita
Rope - Igiya
Run - Gudu
Robust - Mai ƙarfi
Dais - Tukuba
Damage - Ɓarna
Damned - La'ananne
Damp - Danshi
Dance - Rawa
Dandruff - Amosanin ka
Danger - Haɗari
Dark - Mai Duhu
Darkness - Duhu
Date - Kwanan wata
Daughter - Ɗiya
Dawn - Alfijir
Day - Rana
Dead - Matacce
Deaf - Kurma
Dealer - Dillali
Death - Mutuwa
Deceit - Ha'inci
Deceive - Yaudara
Kalmomi masu ma'ana iri daya:
Gwadawa da jarrabawa
Misaltawa da kamantawa
Sanyi da bazara
Rani da zafi
Kala da launi
Tufafi da kayan sawa
Kafa da sahu
Sauri da hanzari
Gida da muhalli
Bandaki da makewayi
Wasan kwaikwayo da dirama
Hanya da gwadabe
Wayewar gari da safiya
Horo da koyo
Inganci da aminci
Mataki da gaba
Nisa da tazara
Wa'azi da tunatarwa
Jinsin kalmomin hausa:
Jinsi a kalmar hausa kala biyu ne; Namiji da Mace. Wato kenan, idan kalma ba jinsin namiji bane, to mace ce. Ana bambance tsakanin waɗannan kalmomi ne da wasulla.
Jinsin maza yana ƙarewa da wasalin, e, ko i, ko o, ko kuma u (e, i, o, u).
Sunaye masu wasalin e:
Dambe, tsage, jele, kare, reshe, jemage, talle, tsalle, bene, talge, balarabe, da sauransu duka wadannan kalmomin misali ne na jinsin maza.
Sunaye masu wasalin i:
Santsi, hantsi, hatsi, katsi, santi, zogi, zagi, jirgi, fili, ɗaki, mari, da sauransu wadannan ma misalin kalmomi masu bin jinsin namiji ne.
Sunaye masu wasalin o:
Tsawo, dolo, coko, filo, lilo, doro, dodo, koko, ƙoƙo, nono, tuwo, tsoro, da sauransu. Wadannan ma duk suna cikin misalai na jinsin maza.
Sunaye masu wasalin u:
Tulu, hutu, guru, turu, shiru, tudu, d.s.
Misali, Tulu ne a can. Komai daɗin kiɗa, shiru ya fi shi. da sauransu. Wadannan ma dai suna cikin misalan jinsin maza a kalmomi.
Jinsin mata yana ƙarewa da wasalin a.
Zana, fawa, ragaya, magana, hasara, gardama, tabarma, damina, d.s.
Misali, Zana ta faɗi. Hasara bata da daɗi. Da sauransu. Wadannan misalan jinsin mata kenan.
{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}