Tarihin Fatima Ali Nuhu

Tarihin Fatima Ali Nuhu

A yau idan Allah Ubangijin talikai ya yarda za muyi rubutu akan tarihin Fatima Ali Nuhu, wato ya' ɗaya tilo ga Sarkin Kannywood, duk da dai cewa ba komai ne zamu iya rubutawa ɗari bisa ɗari dai dai ba a tarihin Fatima Ali Nuhu amma munyi iya bincikenmu domin tabbatar da ingancin bayanai.

Tarihin Fatima Ali Nuhu

Cikakken sunanta: Fatima Ali Nuhu 

Jinsi: Mace

Ranar haihuwa: 13 Janairu 2004 Shekaru 20

Alamar Zodiac: Capricorn 

Wurin Haihuwa: Jihar Kano, Nijeriya 

Ƙabila: Hausa

Addini: Musulunci

Launin gashi: Baki 

Launin fata: Baƙar fata 

Launin ido: launin ruwan kasa 

Uwa: Maimuna Garba Ja Abdulkadir 

Uba: Ali Nuhu Mohammed

Dan uwa: Ahmad Ali Nuhu 

Matsayin: Ba aure

College: Yandutse College

Alma mater: Skyline University 

Sana'a (Occupation): Jaruma (actress), abin koyi (social media influencer) mai tasiri a kafafen sada zumunta.

Fatima Ali nuhu ya ce ga sarkin kanny wood watau sarki Ali Nuhu, ko kuma a takaice Ali Nuhu jarumin kanny wood, mahaifiyar ta Maimuna Ja Abdulkadir, tana da Kani Ahmad Ali nuhu, Fatima Ali 'Nuhu haifaffiyar jihar Kano ce inda aka haifeta ta kuma girma a garin na Kano tayi karatu anan, tayi firamare a garin Kano daga Nan ta tafi kwalejin yandutse inda tayi sakandiri, an haifi Fatima a ranar 14 ga watan Janairu shekara ta dubu biyu da hudu 2004, ta taka rawa a masana'antar fim ta fara fim tun tana yar mitsitsiyar ta watau Child actress kenan tare da mahaifin ta da Kuma Dan uwanta Ahmad Ali Nuhu. 

Mahaifinta Ali Nuhu fitaccen jarumin Najeriya ne wanda ke taka rawa a masana’antar fina-finan kannywood da ta Nollywood. Yana ɗaya daga cikin fitattun jaruman fina-finai a halin yanzu a masana’antar.

Jarumin wanda ake yiwa kallon sarkin Kanny wood ya auri kyakkyawar matarsa ​​Maimuna Ja Abdulkadir kuma aurensu ya albarkaci ƴaƴa biyu.

Ali Nuhu ya haifi  kyakykyawar budurwa ƴar tasa  wadda take yaya ga Ahmad Ali Nuhu. Fatima da ɗan uwanta watau ƙaninta Ahmad suna ɗaukar sawun mahaifin su a matsayin jarumai a masana’antar ta kanny wood a yayin da suke ƙananan yara sosai. A yanzu da suka tasa kuwa an ɗebi shekaru da dama ba'a gansu a cikin shirin fina finan kanny wood din ba. 

Wannan taƙaitaccen rubutun ya ƙunshi taƙaitaccen tarihin Fatima Ali Nuhu ɗiya ga shahararren ɗan wasan kwaikwayo Ali Nuhu kuma ɗiyar sa ta fari. Haka zalika wannan rubutun zai yi duba ga asalin jaruma Fatima Ali Nuhu, haihuwar ta, karatunta sana'a da sauran abinda ya shafi rayuwar matashiyar jarumar. 

Fatima Ali Nuhu fitacciyar matashiyar jarumar fina-finan hausa ce a Najeriya. Ta shahara ta kuma samu karɓuwa da kyakykyawar rawar da ta taka a duk wani aikin fim da darakta ko furodusa ya bata a ɗan taƙaitaccen lokacin da ta shafe a masana'antar tana fitowa a cikin shirin fina finan. 

Iliminta (Education) 

Jaruma Fatima Ali Nuhu ta yi karatun firamare a jihar Kano kafin ta wuce kwalejin ƴandutse inda ta kammala karatunta da kyakkyawan sakamako a SSCE. Duk dai a garin na kano. 

Sana’a a tarihin Fatima Ali Nuhu (Occupation) 

Fatima Ali Nuhu ta fara wasan kwaikwayo ne ta hanyar taimakon mahaifinta Ali Nuhu wanda fitaccen jarumi ne a masana’antar. Haka kuma ita jarumar ta fara harkar fim ɗin ne a ƙarancin shekaru ma'ana tun tana yarinya ƙarama watau ma'ana child actress. 

Mahaifinta kasancewarsa furodusan fim kuma darakta ko mai shiryawa da rubutawa ya fara nuna ta a wasu fina-finansa. Kyakkyawar yarinyar ta nuna gwanintar wasan kwaikwayo a fim din ta na farko kuma hakan ne yasa ta samu karbuwa da jinjina daga manyan furodusoshi da daraktoci da manya jarumai da kuma duk wasu jiga jigan masana'antar ta kanny wood. 

A yau Fatima tana ɗaya daga cikin fitattun matasan jaruman mata da suka fito a masana’antar inda suka yi suna. Fatima ko shakka babu matashiyar jaruma ce kyakkyawar gaske mai kyawun jiki da sura wacce duk da kasancewar ta diya ga babban jarumai mai fada a ji a masana'antar ta kanny wood amma hakan bai hana ta nuna jajircewa da nuna kwazo da kuma dagiya akan duk abin da ta saka a gabanta wurin nema ko ganin cikar burinta. 

Matashiyar jarumar watau Fatima Ali Nuhu wacce aka haifa a shekarar dubu biyu da huɗu 2004, wacce a lokacin rubutun nan take da shekarun haihuwa ashirin cif cif, tayi ƙoƙari sosai wurin rayuwa a matsayin yarinya ƙarama sosai wacce mahainta yake sannane, wacce kuma ita ma ɗin tayi suna duka a dalilin ganin fuskokinsu da mabiya da masoyan su suka saba yi a allon talabijin. 

Saurayin Fatima Ali Nuhu (Boyfriend) 

A matsayinta na fitacciya kuma sananniyar matashiyar yar wasan kwaikwayo a masana’antar nishadi, mutane da yawa sun yi ta ta’aliƙi da neman wanene saurayin Fatima Ali Nuhu. Jarumar mai hazaka ba ta da saurayi amma an yi ta raɗe-raɗin cewa  shahararren mawaƙi Hamisu Breaker saurayinta tane wanda ya fito ya ƙaryata zargin da ake masa. Haka kuma itama daga nata ɓangaren, jarumar matashiyar ta fito ta karyata jiya jitar mutane dake alakanta ta da mawaki hamisu breaker a matsayin masoya watau saurayi da budurwa. 

Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya da ta yi suna a fina-finan Kannywood da Nollywood, Fatima Ali Nuhu. Ita ce diyar Ali Nuhu (wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood). Hakanan tana da ɗan bin layi a matsayin mutuniyar kafofin watsa labarun. Fatima Ali Nuhu a hankali tana haɓaka shaidarta ta yanar gizo.

Fatima Ali Nuhu ilimi Fitacciyar jarumar ta halarci makarantar firamare ta jihar Kano kafin ta ci gaba da karatu a Kwalejin Yandutse, inda ta samu digiri bayan ta yi fice a SSCE. Fatima Ali Nuhu Career Mahaifinta Ali Nuhu, wanda fitaccen jarumi ne a harkar, ya taimaka wa Fatima Ali Nuhu ta fara harkar fim. Da yake mai shirya fina-finai, mahaifinta ya fara haɗa ta a cikin shirye-shiryensa da yawa. Ƙwararriyar budurwar ta yi fice a fim ɗinta na farko, kuma a haka ne sana'arta ta yi fice. Fatima a halin yanzu tana daya daga cikin fitattun jaruman da suka taso a wannan sana’ar, inda ta yi suna. Babu shakka Fatima ta ƙunshi kyau a Kannywood. Tana da kyakkyawar fuska da kyawun sura, wanda ke da albarka. Tana da ɗanɗanar kayan kwalliya kuma tana sa tufafi masu tsada, kuma tana kama da mahaifinta Ali Nuhu sosai.

Controversies sorrounding Fatima Ali Nuhu (Kalubalen da matashiyar jaruma Fatima Ali Nuhu ta fuskanta a kananun shekarunta) 

Akwai Jita-jita da ke nuna cewa Fatima Ali Nuhu da mawaƙi Hamisu Breaker suna soyayya. Jarumar ta bayyanawa mabiyanta a shafinta na Instagram da twitter da kuma facebook cewa Hamisu Breaker ba saurayinta bane. The post, ko da yake, ba ya nan. Bugu da ƙari, Fatima Ali Nuhu ta ja hankalin mutane da su guji yada labaran karya. Ta ci gaba da rayuwa ta hankali duk da zato. 

Haka kuma a irin labaran ƙaryar nan ne a kafar sadarwa ta manhajar youtube aka rika sakin wasu bidiyoyi wadanda su wannan bidiyoyin suna dauke da murya ne kawai amma babu hoto, watau irin bidiyon nan mai dauke da magana kawai. To a cikin ire iren bidiyoyin nan ne aka riƙa yaɗa jita jitar ƙarya wai ƴar Ali Nuhu da cikin shege, ko da yake dama ko a masana'antar holly wood dake can kasar amurka sau tari akan samu irin wannan mutanen masu hadawa da kuma yadda labaran karya domin su samu click, watau ma'ana suna son bidiyon su ya samu views ma'ana a gani da yawa saboda su samu kudin shiga. To irin haka ne aka samu wani ko wasu suka, rika yin irin bidiyon nan na ɓacin suna ga matasjiyar jarumar kuma ƴar fitaccen jarumi Ali Nuhu watau yarsa Fatima Ali Nuhu. 

A dalilin ire iren wannan bidiyoyin da aka rika saki a you tube, tare da haka kuma da masu zagin yarsa a sashen tattaunawa watau comment section na shafin yanar giwo watau web site musamman ma dai a facebook, mahaifinta jarumi Ali Nuhu ya taɓa lasar takobi, ma'ana ya taba daukan alkawarin cewa zai shiga kotu da duk mai zagi, damun ta ko kuma yunkuri bata sunan yarsa. To kuwa dai daga wanna lokaci ire iren abubuwa kamar haka sun ja baya. 

Yanayin rayuwa a tarihin Fatima Ali Nuhu (life style) 

Ko da yake tana yawan musayar bayanai game da ayyukanta na yau da kullum, watau ma'ana tana posting ko kuma za'a iya cewa sharonf na day to day ko kuma daily activities nata akan kafofin watsa labarun watau social media irin su twitter, Instagram da facebook amma kuma ba ta bayyana da yawa game da dangin ta watau family ko yarintar ta ba. Fatima Ali Nuhu tana da sha'awar yin kwalliya watau make up baya ga sana'arta ta wasan kwaikwayo kuma tana yawan raba kayan kwalliyarta da shawarwarin salo ga mabiya nta, duka dai idan mai karatu zai tattaro waɗannan bayanan a dunƙule to zai fahimci cewa ita ɗin tana da sha'awa watau passion ko kuma talent watau baiwa ta make up artist. Hatta layin tufafinta watau clothing line an gabatar da ita, don farantawa kwastomominta rai da jin dadin su. 

Lambar wayar Fatima Ali Nuhu

Lambar wayarta, wacce ke da wahalar samu a matsayinta na fitacciyar yarinya, tana ɗaya daga cikin tambayoyin mabiyanta da ake yawan yi. Ba a samun lambar wayar Fatima Ali Nuhu a yanzu. 

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood mai suna Fatima Ali Nuhu ana kyautata zaton a net worth dinta watau jimillar abubuwan data mallaka a kiyasi zai kai ko kuma ya, kai kimanin dalar amurka dala dubu goma 10,000. Idan aka kwatanta da wasu takwarorinta na holly wood, wannan na iya zama kamar ƙanƙanin abu, amma a harkar fina-finan Najeriya, abin lura ne sosai hakan tunda masana'antar kanny wood dai baza a iya hadata da takwarar ta ba watau holly wood wurin cigaba da kuma shigar kuɗi. 

Abubuwan da Fatima Ali Nuhu ta samu za a iya danganta su da hazaka, jajircewa, da kwazonta. Ta yi kokari sosai don ganin ta zama daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, kuma abin bai ci tura ba. Fatima tana taka rawar gani da dama baya ga sana'arta ta wasan kwaikwayo da tambarin sutura. 

Fatima Ali Nuhu Social Media Instagram handle: @fatimaalinuhu Twitter handle: Fatima Ali Nuhu (@FatimaAliNuhu1) Tiktok handle: Fatima Ali Nuhu.

Wannan rubutun ɗan taƙaitaccen tarihin Fatima Ali Nuhu kenan duk da dai wasu daga cikin tambayoyi na mabiya kuma masoyanta ba a akai ga gano amsoshinsu ba.

Tarihin Fatima Ali Nuhu
Hoton tarihin Fatima Ali Nuhu


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post