Fassarar mafarkin taron jama'a - maciji - kuka - ruwan sama - fada da wani - ruwa da fassarar mafarkin makaranta

Fassarar mafarki post

A yau idan ubangiji mai rahama ya nufa, za muyi bayani akan fassarar mafarki. Kuma a wannan rubutu namu munyi fassarar mafarkin jama'a, kuma bamu tsaya nan ba, akwai fassarar mafarkin maciji, wato idan kayi mafarki da maciji me hakan yake nufi, fassarar mafarkin kuka, shima mun kawo shi, Akwai waɗannan ma duka a ciki fassarar mafarkin ruwa dana ruwan sama, fassara akan mafarkin fada da wani da kuma fassarar mafarkin makaranta.

fassarar mafarki jama'a maciji ruwa,
Mafarki shine yanayin da mutum yake samun kansa wanda a ciki akwai hotuna da yake gani wanda ba a cikin hayyaci ba, ko ra'ayoyi, da kuma duk abubuwan da ke iya faruwa ba da gangan ba a cikin tunani yayin wasu matakai na barci. Mutane suna shafe kimanin sa'o'i biyu suna yin mafarki a kowane dare, kuma kowane mafarki yana ɗaukar kusan mintuna 10 zuwa 20, koda yake mai mafarkin na iya ganin wannan mafarkin ya fi wannan tsayi.

Abubuwan da ke cikin mafarkai da aikin mafarkai sun kasance ababen bincike a filayen kimiyya da falsafa shekaru masu yawa. Sai dai kuma duk da irin binciken da masana suka shafe ƙarni fiye da ɗaya suna nazari akai har yanzu babu wanda ya gano ta yaya mafarki yake kasancewa. 

Fassarar mafarki, waɗanda Babila (Babylon) suka yi a cikin ƙarni na uku har ma a baya ta tsohuwar Sumerians, an ƙididdiga su a cikin masu mahimmanci a cikin rubutun addini a cikin labarai da yawa, kuma ya taka muhimmiyar rawa a cikin dan ilimin abinda aka samu na daga ilimin fassarar mafarki. Nazarin kimiyya na mafarki ana kiransa da ilimin oneirology

Mafarki ya kan kasance watau ma'ana yana faruwa ne musamman a matakin motsin ido watau Rapid Eye Movement (REM) na barci lokacin da aikin kwakwalwa ya yi nisa kuma yayi kama dana farke watau kamar mutum yana cikin hayyacinsa. Domin ana iya gano barcin REM a cikin nau'o'i da yawa, kuma saboda bincike ya nuna cewa duk dabbobi masu shayarwa watau mammals suna samun REM, haɗa mafarki da barci na REM ya haifar da zatonsu da kuma hasashe cewa dabbobi suna mafarki. Duk da haka, mutane suna yin mafarki yayin barcin da bana REM ba, kuma ba duk farkawa bane na REM ke haifar mafarki ko kasancewarsa da rahotannin mafarkin kansa. 

Don yin nazari, dole ne a fara mayar da mafarki zuwa rahoto na magana, wanda shine lissafin abin da aka iya tunawa a mafarkin, ba mafarkin abin da ya faru ba. Don haka, mafarkin wanda ba ɗan adam ba a halin yanzu ba shi da tabbas. 

Mafarki na iya zama abin ban mamaki, ko ban sha'awa, ko kuma na ban tsoro, amma fahimtar ma'anar mafarkanmu na iya zama da ban mamaki. Duk da yake akwai ra'ayoyi da yawa don bayyana dalilin da ya sa muke mafarki, har yanzu babu wanda ya fahimci manufarsu sosai, balle yadda za a fassara ma'anar mafarki. Masana da manazarta sunzo da hasashe da yawa sai dai kuma kamar jiya iyau babu wani gamsasshen bayani game da faruwa ko kasancewar mafarki haka kuma fassarar sama da yawa yawan ta hasashe ce. 

Mafarkin Taron Jama'a:

Mafarki da jama'a wanda suka yi shiru ma'ana babu hayaniya a tsakanin jama'ar da aka gani a mafarkin wata alama ce ta inganctacciyar rayuwa. Idan kukai mafarki tare da taron mutane masu yin shiru alamu ne na wata dama mai amfani da zata zo muku. 

Idan kuma ya kasance a wannan mafarkin taron jama'a sunyi shiru sai mutum ɗaya da yake magana to ma'anar hakan kamar wani gargaɗi ne a cikin rayuwar ku. Don haka a gujewa haɗari gwargwadon yiwuwa a cikin yanke shawara wacce ke da ikon haifar da babban tasiri akan rayuwar ku. 

Ganin taron jama'a suna gudu yana iya zama abin ban tsoro. Amma wannan tsoro yana da alaƙa da ma'anar mafarkin. Yana nuna alamar hakan ka ƙi amincewa da wani na kusa da kai saboda rashin adalci.

Idan kuma ya zamana taron jama'ar dake cikin mafarkin na liyafa ne to

mafarkin taron jama'a a wurin liyafa yana kama da farin ciki.

Yanzu, idan kun yi mafarki cewa kuna cikin bikin, duk da haka tare da mutanen da ba su da farin ciki.

Idan taron jama'ar da aka gani cikin mafarki akan titi suke ko kuma akan wata hanya to hakan ba abin tsoro bane. Akwai alamar wani abu mai kyau da zai faru a rayuwarku nan gaba kaɗan. 

Don mafarkin taron mutane a kan titi alama ce da ke nuna cewa za ku sami kyakkyawar dangantaka da kasuwanci.

Mafarkin Maciji

Kai tsaye dai ana alaƙanta mafarkin maciji da wani maƙiyi ko maƙiyanku.

Mafarkin macizai na iya zama mafarki mai ban tsoro, musamman idan macijin ko macizan suna tsorata ku a cikin mafarkin.

Menene ma'anar mafarkin maciji mai launi?

Launuka kuma suna da ma'ana ta musamman wacce yakamata ku sani sosai. Domin idan ka yi mafarkin maciji mai launuka masu haske, to yana nuna cewa canje-canje na zuwa a rayuwarka amma ba ka san yadda za ka fuskanci su ba. Canjin zai iya kasancewa mai kyau ko akasin sa.

Mafarkin kai harin macizai:

Idan macijin ya kai hari ya cutar da ku to yana nuna alama ta wani al'amari daya haɗa da jayayya ko faɗa a cikin rayuwar ku. Wani abu da ya dame ku da gaske amma dole ne ku fuskanci shi kuma ku warware shi da wuri-wuri. Ta yadda har sai kun gyara, ba za ku iya samun kwanciyar hankali ba. 

Mafarkin macizai da yawa:

Wani lokaci ba kawai mafarkin maciji ɗaya bane amma ana iya ganin macizai da yawa a cikin mafarki. Don haka, idan muka ga maciji fiye da ɗaya a cikin mafarki, dole ne ayi bayani game da  fassarar sa. 

A wannan yanayin shi ne cewa akwai mutane da yawa a kusa da ku waɗanda ba sa gaya muku gaskiya, suna yaudarar ku bada zuciya ɗaya suke zaune daku ba, don haka sai kuyi takatsantsan. Maƙiya ne a zagaye daku.

Macizai a gida:

Mafarkin maciji a gida yana muku nuni da cewar akwai wani mutum ko mutane ƴan uwanku na jiki waɗanda akwai dangantaka mai ƙarfi amma basa sonku kuma waɗanda suke ƙoƙarin cutar daku. 

Mafarkin kuka:

Shi dai mafarkin kuka kai tsaye ba tare da wani dalili ba a cikin mafarki to mafi akasarinsa alheri ne ga mutum. Lokacin da mutum ya yi mafarkin kansa yana kuka da baƙin ciki, wannan mafarkin na iya nuna yiwuwar ƙaura ko kuma yiwuwar rabuwa da wani masoyinsa. Har ila yau, ana iya fahimtar wannan hangen nesa a matsayin gargaɗi ga mutum don ya sake yin la'akari da tafarkin rayuwarsa. 

Mafarkin ɓacin rai da hawaye suna zuba wannan kamar wani albishir ne na kawar wa ko kuma yankewar wahalhalun da aka samu kai a cikinsu. Wanda yayi mafarkin yana cikin ƙunci da hawaye sosai wannan ma wata alama ce dake nuni da samun wata nasara a rayuwa. 

Gabaɗaya, mafarkin da ya haɗa da baƙin ciki da kuka na iya zama alamun cewa damuwa da matsalolin da mutum yake fuskanta a rayuwarsa ta ainihi za su shuɗe, suna ba da bege cewa lokaci mafi kyau zai zo.

Idan mutum ya ga a cikin mafarkinsa yana kuka yana karanta Alkur’ani Maigirma wannan yana nuni ne da tuba da komawa izuwa ga Allah, wanda hakan ke nuna tsantsar gaskiya a cikin tuban mai yin wannan mafarkin tare da neman gafarar zunubai da kusanci ga Ubangijinsa. Bakin ciki a cikin mafarki kuma alama ce ta sauye-sauye na farin ciki mai zuwa, kuma yana nuna cigaba a cikin yanayin rayuwar na mai mafarkin. 

Idan mace yarinya ta sami kanta tana zubar da hawaye a cikin mafarki, wannan mafarkin na iya ɗaukar ma'anoni daban-daban. 

Ga yarinyar da ba ta kasance mai aure ba tukuna, alamu ne na aurenta yana nan gaba kaɗan. Dangane da mafarkin kuka ga yarinyar da har yanzu ba ta yi aure ba, yana iya zama alamar samun labari mai daɗi ko canji mai kyau wanda zai ƙara mata farin ciki a cikin kwanaki masu zuwa, kuma yana iya nuna alamar samun kwanciyar hankali a cikin iyali. Jin bakin ciki da kuka a mafarkin budurwa na iya zama alamar yayewar matsalolin da take ciki. 

Idan matar aure tayi mafarkin tana kuka to hakan yana iya nuni da zata samu yayewar matsalolin da take ciki ko take fuskanta a cikin aure. Lokacin da matar da aka saki ta yi mafarki cewa tana zubar da hawaye, wani lokaci wannan yana iya nuna cewar kila akwai wani auren da zata sake a gaba kadan da, wani mijin mai kyawawan halaye. 

Idan namiji saurayi marar aure ya yi mafarki yana zubar da hawaye, hakan yana nuna cewa abubuwa masu daɗi da za su kusance shi, kamar aure, sabon aiki, ko kuma yin tafiya mai cike da nasarori. Ga mai aure da ya sami kansa yana kuka sosai a mafarki, hakan na iya nuni da cewa damuwa da matsalolin da ke tattare da shi za su shuɗe su yaye ba da daɗewa ba.

Mafarkin Ruwan Sama:

Ganin ruwan sama mai ƙarfi da daddare a cikin mafarkin matar aure yana nuni da zuwan wani lokaci na yalwar arziki da kwanciyar hankali, wannan ruwan sama mai yawa na iya wakiltar kwararar albarka da dama da mace da mijinta za su samu a rayuwarsu.

Mafarkin ruwan sama kamar da bakin kwarya da daddare na iya nuni da girma da ƙarfafa alaƙar aure da soyayya mai ƙarfi da ke ƙaruwa tsakanin ma'aurata a wannan lokacin.

Bugu da ƙari, wannan mafarki na iya nuna zuwan lokacin aiki tare da haɗin gwiwa tsakanin ma'aurata don cimma manufa guda da yanayi mai kyau a cikin iyali.

Mafarkin fada da wani:

Mafarkin faɗa na iya nuni ko zama alamar rikici da tashin hankali a rayuwar mutum ta yau da kullum, kuma yana iya nuna tashin hankalin da ba a warware ba a cikin wata alaƙa. Mafarkin rigima gargaɗi ne cewa ana rayuwa mai cike da ƙiyayya da yawan maƙiya da masu hassada.

Rigima a mafarki na iya zama gargaɗi a gare ku kada ku ci gaba da yin wata alaƙa, ko aiki na musamman ko tafiya, musamman da wanda ake rigimar dashi a cikin wannan mafarkin, domin wannan mafarkin ana fassara shi a matsayin gargaɗin haɗarin da za ku iya fuskanta idan kun kasance tare. 

Wasu masu fassarar mafarki da wasu malamai sunyi nuni da cewa mafarkin rigima na iya nuni da rashin lafiya. Idan mutum ya samu kansa a mafarki ana rigima dashi to ana daukar wannan a matsayin shaidar cewa zai iya kamuwa da cuta a nan gaba.

Mafarkin Ruwa:

Mafarkin ruwa ga wanda yayi shi ana alaƙanta shi ne da yalwar arziki ko wata dama da zata  biyo ta hanyar mutum bada daɗewa ba. 

Mafarkin Makaranta:

Idan mutum yayi mafarki da makaranta to alamun rikice-rikice ne a rayuwarsa, wanda kuma ya shagala ya kasa yanke shawara, kuma hangen nesa na makarantar gaba ɗaya shaida ce ta buƙatar tuntuɓar waɗanda suke masu sani a cikin wannan al'amarin domin su warware shi.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post