Amfanin bagaruwa ga budurwa

Amfanin bagaruwa ga mata da namiji

Barka jama'ar Hausa a yau munyi tattaki izuwa jawabi dangane da amfanin bagaruwa ga mata da maza, harma da amfanin shan ruwan bagaruwa, haza zalika dama wasu haɗi kamar na amfanin bagaruwa da zuma da dai sauransu.

Amfanin bagaruwa ga budurwa

Bagaruwa watau Vachellia nilotica a sunanta na kimiyya, wata bishiya ce wacce take da ƴaƴa ƙanana ana samun ta a daji ko cikin gari inda mutane suke haka kuma ana haɗa magunguna da ita sosai. 

Magungunan da ake samarwa daga bishiyar bagaruwa da ƴaƴan ta sun haɗar da; maganin tsutsar ciki, maganin basir, maganin ulcer, maganin sanyi. Bagaruwa na maganin cutar Hepatitis C.  maganin warin jiki, haka kuma tana maganin jan ido da sauran magunguna da suka shafi ɓangaren ƴan'uwa mata da maza. 

Wasu daga cikin amfanin bagaruwa a jikin ɗan adam

Bagaruwa na maganin tsutsar ciki.

Itacen bagaruwa na maganin gudawa mai tsanani. 

Yana kuma kawar da matsalar zubar jini. 

Bagaruwa na maganin ciwon haƙori Ana daka ƴaƴan bagaruwa a riƙa zubawa ko kuma a samu ƴaƴan ta waɗanda basu bushe ba a riƙa matsa ruwanta a cikin wurin. 

Bagaruwa na maganin ciwon sikari wato ‘Diabetes’. 

Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki.  

Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata.

Yana ƙara ƙarfin mazakuta. 

Ganyen bagaruwa idan aka tafasa idan ya tafasu aka juye a buta ana  wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido.

Amfanin shan ruwan bagaruwa 

Shan ruwan da aka jiƙa bagaruwa ko aka tsumata a cikin sa yana da fa'ida da yawan gaske, cikin ire iren fa'idojinsa sun haɗar da;

-Wanko dattin ciki dana mara

-Kashe tsutsotsin ciki da kwayoyin cututtuka na cikin cikin ɗan adam 

- Daidaita sikari wanda ta hakan take ragewa ƙoda ayyuka. 

-Wankin hanta da koɗa daga datti

-Wanko dattin mahaifa a jikin mace

-Shan tsumammen ko jiƙaƙƙen ruwan bagaruwa yana maganin sanyi daga cikin jikin mutum

-Shan ruwan bagaruwa yana kashe wari da kwayoyin cuta masu ginuwa a cikin bakin ɗan adam. 

-Shan ruwan bagaruwa yana taimakawa digestive system na ɗan adam wurin saurin narkar da abincin da aka ci haka kuma yana taimakawa masu lalurar ko cutar basir wurin yin tsuguno ba tare da sunsha wahala ba. 

Waɗannan kaɗan kenan daga cikin irin amfanin da za'a ribata daga shan ruwan bagaruwa. A domin haka sai ku riƙa tsuma ko jiƙa bagaruwa domin samun waɗannan fa'idojin ko kwa samu cigaba a lafiyar jikinku. 

Yadda ake matsi da bagaruwa

Bincike da yawa yawa sun tabbatar da cewar ana yin matsi da bagaruwa. Haka kuma tuni mata suka karɓi bagaruwa suke yin amfanin kansu da ita, ciki kuwa harda matsin farjin su kuma mata da yawan gaske sun tabbatar da sahihancin matsin da ake yi da bagaruwa. Hanyoyin matsi da bagaruwa suna da yawa saboda ya danganta da abubuwan da za'a haɗa tare da ƴaƴan bagaruwar da za'a yi matsin. 

Akwai matsin da mata suke yi da bagaruwa wanda suke haɗa ƴaƴan bagaruwa da kanunfari da ganyen magarya da miski. Akwai irin matsin da ake haɗa bagaruwa da lalle shima yana da kyau kuma yana aiki da gaske matuƙa gaya. 

Hanyar farko wacce ake haɗa matsin bagaruwa shine a samo ƴaƴan bagaruwa da garin kanunfari da ganyen magarya da miski. Bayan an samar da waɗannan kayan haɗin sai a haɗe su guri ɗaya a kuma tafasa su sannan a tace ruwan a zuba miski a  ɗinga zama a cikin ruwan. 

Zaman da za'a yi a cikin wannan haɗaɗɗen ruwan ya kai tsayin mintuna talatin zuwa arba'in. 

Za kuma a iya yinsa na tsawon sati biyu, wanda za'a sha mamaki sosai. Bayan tsukewar farji da matsewar sa haka kuma yana saukar da danshin farji da ni'ima sosai tare da kashe kwayoyin cutar sanyi da suke curewa a bakin farjin. 

Wata hanyar yin matsi da bagaruwa itace hanyar haɗa bagaruwa da lalle. 

Za'a haɗa ƴaƴan bagaruwa da lalle a dafa su a tace ruwan sannan a saka mazarkwaila a ciki. Shima za'a zauna a cikin ruwan da ɗuminsa sosai kuma ba za'a tashi ba har sai ruwan yayi sanyi. 

A wata hanyar ta yin matsi da bagaruwa kuma ana dafa ƴaƴan bagaruwa da ganyen magarya a riƙa wanke gaba dashi ko a zuba a baho a zauna a ciki da ɗumin sa kaman 30 mins a ƙalla sau biyu a sati.

Amfanin tsarki da bagaruwa

Kamar yadda ake shan ruwan bagaruwa a ga amfaninta da kuma matsi to haka ma tsarki da ruwan bagaruwa yana da matuƙar amfani musamman a gurin mace. Idan mace ta jiɓanci tsarki da ruwan bagaruwa zata samu waɗannan fa'idojin kamar haka;

-Tsarki da ruwan bagaruwa zai sa farjin ki tsukewa ya matse ya dawo tamkar na budurwa.

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana ƙara haɓaka danshin gaba watau yana ƙarawa mace flora kenan.

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana kashe kwayoyin cututtuka masu lahani ga farjin mace.

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana tabbatar da kwayoyin bacteria masu alfanu a gaban mace

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana hana ƙuraje da ƙaiƙayi da fitar irin farin ruwan nan mai wari wanda illolin sanyi suke kawowa gaban mace. 

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana taimakawa wurin rage zugi da ciwon mara a yayin al'adar mace musamman ga fararriya ma'ana wacce ta fara. Haka kuma sababbiya ma ma'ana wacce ta saba duk dai yana taimakawa wurin rage wannan ciwon na mara. 

-Tsarki da ruwan bagaruwa yana kashe warin da gaban mace yake yi. 

Maganin sanyi da bagaruwa 

Bagaruwa dai sahihiyar maganin sanyi ce tun zamanin iyaye da kakanni kawo yanzu a wannan ƙarnin da muke ciki. Duk abinda ya danganci bagaruwa kama daga icen ta watau sassaƙen ta da ganyen ta, da ƴaƴan ta haɗe da saiwar ta dukansu ana magunguna dasu sosai kuma magungunan da ake samarwa daga ƴaƴan bagaruwar da saiwarta da sassaƙen da kuma ganyen nata duka ingantattu ne, haka musamman a ɓangaren cututtukan sanyi ma. 

Da farko dai idan aka samu ƴaƴan bagaruwa aka dafa tare da salar tafarnuwa kamar guda uku sannan kuma a samu lemon tsami mai kyau mai ruwa aka matse a ciki ana sha da zafin sa to wannan haɗin yana wanko duk wani sanyi da dattinsa dake kwanciya a marar ɗan adam. Haka kuma yana kashe duk wani sanyi dake kwance a jikin mutum. Idan aka jiɓanci haɗa wannan maganin kuma ana amfani dashi to da hakan yana nufin anyi bankwana da sanyi kenan. 

Idan kuma ana son ayi maganin cututtukan fata na sanyi sai a samu ganyen bagaruwa da ganyen magarya a dake su su daku. Wannan maganin ana iya haɗa shi ta hanyoyi biyu domin samun amfaninsa. Hanya ta farko dai, za'a busar da wannan dakakkun ganyayen bagaruwar da magaryar ne daga nan sai a riƙa zubawa a ruwan mai ɗan zafi wanda za'a iya zama ayi hot bathe. Hanya ta biyu kuwa shine bayan an daka ganyayen nan na bagaruwa da magarya to kar a busar dasu a hakan yadda suke a dake sai a samo man zaitun a ɗiga musu su haɗe su sake curewa sosai. Daga nan za'a riƙa shafawa a fatar duk inda yake da matsala walau ƙaiƙayi ko ƙurajen sanyi da dai duk lalurar fata da sanyi yake haddasawa. 

Idan ana aswaki da icen bagaruwa to bincike na masana da manazarta ya tabbatar da hakan yana kashe kwayoyin cuta na sanyi masu haddasa wannan warin dake fitowa daga bakin mutum wanda kuma tushen wannan warin yana fitowa ne daga cikin mutum. To aswaki kaɗai da sassaƙen icen bagaruwa yana taimakawa wurin yaƙar warin na ciki da kuma wanda ya gume bakin mutum. 

Saiwar bagaruwa kuwa ana amfani da ita tun tali tali watau zamanin iyaye da kankani domin ita ma tsagwaron magani ce ta sanyi. Akan samu roba a zuba saiwoyin nan na bagaruwa a zuba ruwa a barsu su jiƙu sosai. Idan aka jiɓanci shan wannan jiƙaƙƙen ruwan na saiwar bagaruwa to magani ne mai matuƙar tasiri na ciwukan sanyi dake taruwa ya danƙare a jikin ɗan adam ciki da wajen sa. 

Bagaruwa na maganin basir ? 

Kwarai da gaske bagaruwa tana maganin basir. Basir mai rikita ciki, ko basir mai tsiro, ko basir mai fitar baya, ko basir mai hana cin abinci, ko basir mai sa zafin jiki, duka bagaruwa zata iya taimakawa wurin magance waɗannan matsalolin. 

Domin magance waɗannan matsalolin sai a nemi ƴaƴan bagaruwa da ganyen runhu a daka a tankaɗe a riƙa shan cokali ɗaya a cikin shayi ko kunu sau biyu a rana na tsawon kwana biyar zuwa sati ɗaya. 

Bagaruwa na maganin ulcer ?

Sosai ma kuwa. Kasancewar a cikin irin ɗimbin sinadaran da suke cikin ƴaƴan bagaruwa akwai sinadarin anti acid hakan yana sawa bagaruwa ta shiga cikin gagga gaggan mugunguna na ulcer wanda ba kowa ne ya sani ba. Amma kuma dama aka ce rashin sani yafi dare duhu, domin kuwa shan ruwan tsimammiyar bagaruwa kaɗai idan aka jiɓanta to fa da sannu yake kashe ulcer farat ɗaya saboda zai warkar da gyambon ciki. 

Amfanin hadin Bagaruwa da Zuma 

Amfanin haɗin bagaruwa da zuma yana da yawan gaske domin kuwa yin wannan haɗin na bagaruwa da zuma yana magance matsaloli da yawa haka kuma yana samar da fa'idoji da yawa a jikin ɗan adam musamman mace. Haɗin dabino da zuma yana tackling matsalolin sanyi da suka haɗar da;  ƙaiƙayin gaba, ƙurajen gaba, ƙaiƙayi na matse matsi, fitar ruwa mai ƙarni ko wari watau vaginal discharge mara kyau a gaban mace da zafin gaba da kuma rashin juriya yayin jima'i da kuma ɗaukewar sha'awa, kai da duk wata matsala wacce ke da alaƙa da cutar sanyi a jikin ɗiya mace. 

Baya ga wannan matsalolin da wannan haɗin na bagaruwa da zuma yake magancewa yana kuma saukar da ni'ima a farjin mace domin kuwa idan mace tana yin wannan haɗin to kuwa zata wanzu ne cikin ni'ima nasha nasha. Bugu da ƙari kuma, wannan gagarumin haɗin dai har ila yau yana sa mace ta haɗe ta tsuke tamkar wata budurwa sabuwa gal a leda. Wannan lissafe lissafen fa duk suna cikin tagomashin da za'a samu ne idan akai amfani da haɗin bagaruwa da zuma. 

Haɗin gashi kamar haka;

Idan aka samu ƴaƴan bagaruwa aka dake su sukai lukui sai a kawo zuma haɗaɗɗiya mai kyau a zuba a cakwuɗa su. A bar wannan haɗin ya tsumu ya kama jikinsa sosai. Idan an tashi amfani dashi lakata za'a keyi ana shafawa sai a barshi kamar na tsawon awa ɗaya zuwa biyu sannan a wanke. Bayan an wanke sai a shafa miski. 


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post