Amfanin Kanunfari ga maza da budurwa

Amfanin kanunfari ga maza da mata

A wannan rubutu namu na yau zamu yi tsokaci akan abubuwa da dama dangane da kanunfari, kamar su matsi da kanunfari, amfanin shan ruwan kanunfari, amfanin tazargade da kanunfari da kuma amfanin zuma da kanunfari  ga maza da mata gaba ɗaya.

Amfanin Kanunfari ga maza da budurwa

Kanunfari watau clove a turance kenan fitaccen ɗan itaciya ne kuma mai ɗauke da sinadarai kala waɗanda a cikinsu akwai sinadaran da suke ɗauke da properties watau alamomi na anti bacterial agents, haka kuma wasu sinadaran nasa suna ɗauke da analgesic properties watau kashe zugi. Bugu da ƙari, kuma yana da sinadaran da suke da anti fungal properties duk shi kaɗai. Kanunfari abu ne da mutane da yawa a sassa daban daban na faɗin duniya ke amfani dashi ke wajen girki, da haɗin shayi da shan sa da kuma wasu abubuwan na inganta lafiya da jin daɗi.

Ana amfani da itacensa ko ƴaƴansa ko ganyensa ko busasshe ko a gudan sa ko kuma a daka garin sa a sarrafa su domin biyan buƙatu iri iri daban-daban a ko ina a faɗin duniya. Ko da yake galibin ƙasashe ko garuruwan larabawa watau mutanen gabas ko kuma al'ummar yankin mutanen ƙasashen Asiya (asia) sun fi amfani da shi da kuma sanin sirrikansa.

Yana ƙunshe da sindarai irin su Vitamin K da Fiber da Calories da carbs da Manganese.

Yana ƙunshe da sindaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.

Yana iya taimakawa wajen hana kamuwa da kansa ko sanƙara

Yana kashe kwayoyin cutuka

Yana inganta lafiyar hanta

Yana daidaita sukari a cikin jini

Yana ƙara lafiyar ƙashi

Yana hana kamuwa da ulcer

Yadda Ake Matsi Da Kanunfari 

Gareku mata, ga hanyar da za'a bi wurin sarrafa kanunfari ayi matsi da shi. Za'a samu kanunfari a daka shi ya daku sosai ya zama gari yayi lukui, daga nan kuma sai a samo ɓaure watau arabic gum ayi mix watau a cakwuɗe shi da wannan dakakken kanunfarin. Bayan an haɗasu an cakwuɗasu sosai, sai a samo zuma kuma mai kyau, yadda ake amfani da wannan hadin shine za'a zuba babban cokali biyu na zuma a juyata da wannan haɗin dakakken kanunfarin da kuma ɓaure watau arabic gum. Idan haɗin nan ya haɗu sosai za'a ga yayi danƙo sosai to hakan yayi. Za'a riƙa lakata ana shafawa a bakin farji, za'a iya barin sa tsawon awa ɗaya zuwa biyu kafin a wanke, idan kuma an tashi wankewa za'a yi amfani ne da ruwan zafi. Za kuma a iya shafa wannan haɗin da dare ayi bacci dashi watau overnight kenan. 

Wannan haɗin da nayi bayanin sa a sama, baya ga haɗe miki farji da zaiyi zai miki maganin duk wani sanyin da yake gabanki ya kuma saukar miki da cikakkiyar ni'ima. Kin jefi tsuntsu wane biyu, ai anan tsuntsu huɗu kika jefa da dutse ɗaya. 

Amfanin shan ruwan kanumfari

Ruwan kanunfari na da amfani sosai matuƙa ga lafiya saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da bunƙasa garkuwar jiki. 

Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer tasiri . Haka kuma kanumfari yana taimakawa lafiyar haƙora da hana kumburin dadashi da fitar da jini.

Sannan kuma binciken masana ya tabbatar cewa ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa ta hanyar ƙona calories da yaƙar tasirin cholesterol a jikin ɗan adam. 

Ruwan kanumfari yana maganin jiri watau dizziness da kuma cutar kwalara (cholera).

Ruwan kanumfari yana taimakawa wajen saisaita sukari watau balancing a cikin jini da kare lafiyar hanta saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta.

Amfanin Kanunfari Ga Maza kaɗai 

Masana da manazarta a harkokin lafiya sunyi bincike da nazari sosai kuma sun bada bayanai akan amfanin wannan sinadarin na kanunfari a cikin rayuwar ɗan adam.

Kanunfari na ɗaya daga cikin magungunan gargajiya da ke ƙara wa maza lafiya domin kuwa yakan ƙara yawan sanadarin 'testosterone' wanda ke tasiri wajen haɓakar gaɓoɓin saduwa na namiji.

Kanunfari idan ɗa namiji yana shan ruwansa zai taimaka masa wurin kashe cututtukan sanyi na cikin jikinsa dana waje ta hanyar yaƙar su, kasancewar kanunfari yana ɗauke da wasu sinadarai da suke taimakawa white blood cells a jikin ɗan adam. 

Kanumfari yana ɗauke da sinadaran da suke taimakawa jikin mutum rage calories watau rage ƙiba ko teɓa.

Kanumfari yana taimakawa azzakarin ɗa namiji wurin ƙara ƙarfi. Kanunfari yana inganta lafiyar maniyyin namiji. Yana kuma ɗauke da sinadarai da ke ƙara yawan maniyyin ɗa namiji ke samarwa, wanda hakan shi ne abu mafi amfani ga lafiyar maza.

Kanumfari yana magance matsalar saurin fitar maniyyi da rashin miƙewar azzakari ko kuma ƙarancin sha'awa a wurin ɗa namiji. 

Kanumfari yana taimakawa wurin saisaita level na sikari watau sugar dake jikin ɗan adam ta haka yana taimakawa aikin ɗoda watau kidney. 

Kanumfari yana taimaka wurin wankin dattin ƙoda da hanta kuma yana bada kariya daga kwayoyin cututtukan da suke fakewa a cikin bakin ɗan adam. 

Kunumfari yana taimakawa wurin magance ciwukan gaɓɓai masu alaƙa da sanyi da kuma wanda ma bana sanyi ba. 

Amfanin kanunfari ga mata kaɗai

Amfanin kanunfari ga mata da maza kusan abu ɗaya ne, illa iyaka dai ƙarin alfanunsa ga ɗiya mace shine ita yana taimaka mata wurin magance matsaloli na ciwon mara dake alaƙa da al'adar ta.

Kanumfari yana ƙarawa mace ni'ima wannan kuwa binciken masana da manazarta ya jima da tabbatar da hakan. 

Kanumfari yana magance matsalar fitar ruwa da ƙuraje da kuma wari daga farjin mace. 

Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauƙin ciwon mara a lokacin al'ada da taƙaita kwanakin al'adar.

Kanumfari yana taimakawa wurin saukar da ni'ima a farjin mace da kuma tabbatar da wanzuwar flora watau danshin farji duk dai a gaban mace. Haka kuma yana kashe warin gaba wanda illolin sanyi kan sabbaba shi. 

Haɗin Dabino da Kanunfari da Amfaninsa 

Wannan haɗin na dabino da kanunfari ana yi masa kirari kamar haka;

Ba don komai yasa ake wa wannan haɗin na dabino da kanunfari wannan kirari ba sai domin mata da yawan gaske sin karanta, sun haɗa shi kamar yadda akayi bayani, sun kuma gwada shi, tare da haka kuma sun bayar da bayanai watau feed back kenan a turance, sun bada bayanai na irin tagomashin da suka samu daga wannan haɗin na dabino da kanunfari. Ga yadda haɗin dabino da kanunfari yake;

Za'a nemi kanunfari da dabino sai a samu wani abu mai faɗi haka a jiƙasu. Bayan sun juƙu a riƙa ɗiban ruwan ana saka zuma a ciki ana sha. Wannan kenan, su kuma waɗannan jikaƙƙun dabino da kanunfarin a saka a blender a niƙe su, sannan kuma idan anso za'a iya juye musu madarar ruwa a sha. 

Amfanin haɗin dabino da kanunfari 

Yana ƙara ni'ima kwarai da gaske. 

Yana kawo ruwa sosai a farjin mace hakan zai sa mace ta riƙa jinta nasha nasha tamkar taci gumba. 

Zai kuma yiwa mace maganin sanyin gaba da haɓaka sha'awar ta. 

Haɗin tazargade da kanunfari da amfaninsa

Tazargade tana da matuƙar amfani a jikin ɗan adam, hasali ma a shekarun da suka gabata zai yi wahala a shiga gidajen bahaushen mutum ba tare da an tarar da an yi tanadinta ba don magance larurori na jiki ko na al’ada. Ana amfani da ita don magance cututtuka daban daban. 

Da yake tazargade tana da tasiri sosai wurin gyara al’aurar mace musamman wurin kashe kwayoyin cututtuka da ake ɗauka a dalilin amfani da banɗaki marar kyau ko ta hanyar kusantar iyali (infection) daga irin wannan matsalar kan haifar da ƙaiƙayin gaba ko matse-matsi da warin gaba da fitar ruwa a gaban mace mai ƙarni ko wari da bushewar gaba. Tana kuma yin gyara ga wadda ta haihu ko kuma ta samu ƙari a dalilin haihuwa ko wani dalili na daban to kuwa idan akayi haɗin ta da kanumfari, wani sinadarin mai cike da alfanu to kuwa hakan yana samar da fa'idojin gaske. 

Idan aka samu tazargade sai a samu kanunfari a haɗa a tafasa su, asha kuma ana kama ruwa dasu. Wannan shima an gwada, an kuma ga sakamakon gaske. 

Amfaninsa 

Yana kashe kwayoyin cututtukan sanyi na ciki dana waje. 

Yana saukar da ni'ima sosai a mace

Yana ƙarawa namiji ƙarfin sha'awa da ƙarfin mazakuta 

Yana saka kwazo da gwarzantaka a fagen fama watau kan gado a yayin kwanciya. 

Menene fa'idar tsuguno da kanunfari? 

Chab ɗi!.. Fa'ida kai. 

Za'a samu kanunfari a kakkarya ko kuma a daka sama sama, domin idan aka dake ya zama gari ba zai ci wuta ba. Bayan an daka shi sama sama ko kuma an kakkarya shi sai a samu garwashi akai ɗaki a kuma zuba kanunfarin akan garwashin kamar dai yadda ake ƙona turaren wuta. Idan anyi haka sai a tsuguna akan hayaƙin domin hayaƙin ya shiga ya kuma ratsa farji sosai. Wannan shine yadda ake tsuguno na kanunfari. 

Fa'aidar sa ko kuma nace fa'idojin sa sune kamar haka;

-Tsuguno da kanumfari yana ciko da gaban mace 

-Tsuguno da kanunfari yana kashe wari ko ƙarni dake fitowa daga gaban mace

-Tsuguno da kanunfari yana ɗauke vaginal discharge

-Tsuguno da kanumfari yana tsuke ko matse gaban mace ya kuma saukar da ni'ima tare da haka yana ruruta wutar sha'awar ta. 

Menene amfanin tsarki da kanunfari? 

Idan nace zan tsaya zayyano ko kuma lissafo amfanin tsarki da kanunfari sai mu kwana mu wuni anan ban gama ba, amma dai a taƙaicen taƙaitawa, ga wasu daga jikin alfanunsa kamar haka;

-Kama ruwa watau tsarki da ruwan kanunfari yana maganin matsala ko illolin da sanyi yake yiwa farjin mace. Har ila yau kar mu manta da tsagwaron amfanin kanunfari wurin maganin sanyi. 

-Kasancewar kanunfari yana ɗauke da sinadaran da suke da anti bacterial agents cikin tarin sinadaran sa, saboda haka kanunfari yana yaƙar kwayoyin cuta masu samun mafaka a bakin ko ƙofar farjin mace. 

-Tsarki da ruwan kanunfari yana yaƙi da ƙurajen farji ko kuma hana wanzuwar su idan har kika jiɓanci yinsa. Haka kuma shima dai tsarkin kamar tsugunon kanunfari ne domin yana hana vaginal discharge mai ƙarni da wari yana kuma tsayar da ƙaiƙayin gaba wanda ke samuwa daga infection. 

-Har ila yau tsarki ko kama ruwa da ruwan kanunfari yana kawowa tare da tabbatar da danshin gaban mace domin kuwa duk macen data jure ta jiɓanci tsarki da ruwan kanunfari to zata samu wadatar flora. Watau ruwan da yake fitowa daga gaban mace. Ruwa mala kara, mara scent ko odour kuma wanda zubar sa daga farji alama ce ta ni'imar ƴa mace. To tsarki da ruwan kanunfari duk yana samar da waɗannan alfanun idan aka jure yinsa. 

A karanta a fahimta sosai sannan a aikata shi a aikace domin neman yayewar matsalolin gaba da neman ni'ima. 


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post