Yadda ake sarrafa shinkafa kala-kala

Yadda ake sarrafa shinkafa kala-kala 

Yadda ake sarrafa shinkafa kala kala
Shinkafa dai wani nau'in abinci ce da ake nomawa domin samar da amfanin gonarta a ƙasa. Kasancewar shinkafa tayi dominating ƙasashen nahiyar mu ta africa, da wasu ƙasashen gabas da kuma ƙetare, dole ne mutane su samar wa kansu hanyoyi kala kala na yadda zasu sarrafa shinkafa domin ciyar da kansu. 

People read also.

Hanyoyi da zaki girka abubuwa iri-iri da fulawa

A cikin wannan rubutun zanyi bayanin wasu daga cikin hanyoyin yadda ake sarrafa shinkafa kala-kala. Ku biyo ni a sannu. 

Yadda ake dafa farar shinkafa👈

Farar parsley rice da shurba 

Shinkafa kilo guda

Mai chokali 8

Kaza guda 3

Albasa

Tattasai 

Attarugu

Chokalin curry thyme, rose merry 1 rabin karamin

chokalin Citta, Organo 

Maggi 6

Gishiri

7 spices, arabian mix rabin karamin chokali

Method of preparation

Da farko za'a wanke kaza a yanka a zuba a tukunya a jajjaga albasa da tattasai da tarugu a zuba, sannan a zuba ruwa isasshe, sannan a zuba kayan ƙamshi dana lissafa da maggi da gishiri a juya da tafarnuwa, a bashi lokaci yayi ta dahuwa.

Sannan a wanke shinkafa a ɗora a tukunya akan wuta a zuba mai sannan a zuba shinkafar da aka wanke da gishiri a juya kaman na minti biyar sannan a zuba ruwa mai ɗumi wanda aka san zai iya dafa  shinkafar a rufe a bari ta dahu. 

Sannan a zuba ganyan parsley a juya sannan a sauke a zuba a mazubi a zuba shurba a mazubi guda. 

Ya ake Dambun Shinkafa👈

Gas meat mai zaitun da green beans da farar shinkafa

Nama rabin kilo

Zaitun 8

Albasa 6

Attarugu 6

Chokalin curry, thyme, garin yaji,

Spices 

Albasa mai lawashi

Maggi hudu

Gishiri kadan

Green beans kadan

Citta

Rose merry, shammar, black pepper 

Mai kadan

Bay leaf 1

Albasa tagari tafarnuwa ta gari rabin karamin chokali

Ruwa dai dai bukata

Method of preparation 

Da farko za'a tanadi kayan dana lissafa sannan a yanka nama dogwaye a zuba shi a roba asa mai kaɗan da kayan ƙamshi da maggi da garin yaji a juyashi a bashi wasu awoyi sannan a ɗauko.

Sannan a ɗaura frying fan akan wuta a zuba mai da albasa da shammar da rose merry a soya sama sama. 

Sannan a jera naman a cikin frying fan ɗin. Sannan a rufeshi ya sulala ruwan ya fito. Sannan a ƙara ruwa kaɗan a rufe ya dahu sosai.

Sannan a ƙara maggi a zuba albasa a sama da green beans a juya. 

Sannan a zuba albasa mai lawashi da zaitun a juye attarugu a rufe lawashin su ida turara sannan a sauke. 

Sannan a zuba a mazubi ayi masa kwalliya da abinda yayi. Sannan a zuba farar shinkafa a zuba gas meat a gefe. 

Yadda ake Tuwon shinkafa👈

Farar shinkafa da miyan kuɓewa ɗanya

Kuɓewa Rabin kilo

Kaza guda

Mai ƙoshiya biyu

Shinkafa kilo guda

Maggi 8

Chokalin curry, thyme, garin albasa, garin tafarnuwa, 

Karamin cokalin black pepper, tandoori, masala,

7spices rabin karamin

chokali

Citta, 

Rosemary 

Gishiri

Ruwa daidai bukata

Method of preparation 

Da farko za'a tanadi kayayyakin sannan a gyara kaza a wanke a ajiye waje guda sannan a ɗora tukunya akan wuta a zuba mai yayi zafi a yanka albasa a zuba sannan asa naman kaza da citta da gishiri da rose merry da bay leaf a juya.

Sannan a rufe a bashi lokaci ya dahu ya fara soyuwa a tukunyar sannan a wanke shinkafa a zuba ruwa a wata tukunyar yayi zafi a wanke shinkafa a zuba ruwa wanda aka san zai ƙarasa dafa shinkafar da gishiri a rufe ta dahu. 

Sannan a zuba dafaffen chefanen nan da aka markaɗa a juya sannan a zuba kayan ƙamshi a rufe ta soyu. Sannan a wanke kuɓewa a gyara. 

Sannanki a rufe ta soyu, da mai ya fita sai a zuba kuɓewar a juya. 

Sannan a rage wutar a rufe na wasu mintoci sannan ta dahu tafi da. 

Sannan a zuba a mazubi ko kula sannan a zuba shinkafa.

Yadda ake shinkafa da miya👈

Farar shinkafa mai carrot da green beans mai miyan egg plant da kwai

Shinkafa kofi huɗu

Carrot da green beans kofi guda

Attarugu guda 6

Maggi 10

Kwai biyar

Egg plant 8

Albasa 4 tumata8 tattasai 6

Ruwa daidai bukata

Bay leaf 1

Chokalin garin coriander 

Rabin chokalin shammar, thyme curry, gram masala,7spices 

Citta kaɗan

Chokalin gishiri 

Method of preparation 

Da farko a wanke shinkafa a ajiye waje guda sannan asa ruwa yayi ɗumi a zuba shinkafar a tafasa sannan a wanke asa gishiri da ruwan da akasan zai ƙarasa dafa shinkafar, da takusa shanye ruwan a zuba carrot da green beans a rufe ta ƙarasa dahuwa. 

Sannan a gyara chefane a markaɗa sannan asa mai a tukunya a ɗora kan wuta yayi zafi, sannan asa chefanan da aka gyara aka markaɗa. 

Anayi ana juyawa daya fara soyuwa mai yayi sama sai asa kayan ƙamshi da maggi da gishiri. Sannan a wanke egg plant a yanka a soya shi. Sannan a zuba a miyar. 

Yadda ake wainar shinkafa👈

_________________________________

Yadda ake sarrafa shinkafa kala-kala section B

Farar Shinkafa mai carrot da dankalin turawa da green beans

Shinkafa kofi uku

Carrot da green beans

Dan kalin turawa guda biyu

Ruwa dai dai bukata

Chokalin gishiri 

Method of preparation 

Za'a wanke shinkafa a ajiye waje guda sannan asa ruwa a tukunya wanda aka san zai iya dafa shinkafar asa gishiri a basu mintuna su tafasa. Sannan a zuba shinkafa a kawo kayan lanbu a zuba carrot da green beans, wanda aka gyara, a yanka carrot ƙanana shida dankalin turawa.

A juya a rufe shinkafar ta ƙarasa sulala sannan a sauke a zuba a mazubi. 

Tuwon niƙaƙƙiyar farar shinkafa

Farar shinkafa

Ruwa

tukunya

Muciya

Abun girki

Method of preparation 

Za'a auna farar shinkafa sannan a wanketa tas idan kuma akwai tsinta sai a tsinceta sannan a wanke. 

Sai a jiƙata tayi kamar 2 to 3 hours tayi laushi sosai. Idan ta jiƙu sai a ƙara wankewa. Asa a blender da ruwa a niƙa har tayi laushi amma kar a cika ruwa kuma kar tayi kauri. 

Idan yayi laushi sai a samu tukunya asa ta akan wuta, medium heat sannan a juye wanan ƙullin. Sai a samu muciya ayi ta juyawa har ya dahu yayi kauri. 

Idan ya dahu sai a ɗan mai ruwa kaman half cup yanayin dai kaurin da ake so sanan a rufe a barshi ya ɗan sulalu. Idan yagama sulaluwa sai a ƙara tuƙawa. Sai mulmulawa da serving. 

Yadda ake sinasir din shinkafa👈

Farar shinkafa da miyan kuɓewa

Shinkafa kofi biyu

Kuɓewa rabin kilo

Nama rabin kilo

Maggi 4

Tumatar guda biyu,

Tattasai guda biyu

Mai rabin kofi

Chokalin curry thyme 

Albasa guda biyu

Tafarnuwa biyu 

Ruwa daidai bukata

Chokalin citta 

Onga 1

Method of preparation

Da farko za'a wanke shinkafa sannan asa mai kaɗan a tukunya a kunna wuta a soya shinkafar sama sama. 

Sannan asa mata gishiri a kawo ruwa wanda yayi zafi a zuba daidai wanda aka san zai dafa wannan shinkafar, a rufe ta dahu. 

Sai a ɗauko kuɓewa a gyara a yankata biyu biyu in dogwayene a yankata uku. 

Sannan a kawo kuɓewar a zuba a juya abarta ta dahu na wasu mintoci, sannan asa curry da onga a juya sannan a sauke bayan an tabbatar ta dahu. 

Sannan sai a jajjaga kayan miya a soyasu sama sama sannan akawo naman wanda aka yanka dogwaye kaman na shawarma asaka a kuma saka kayan ƙamshi citta da thyme a juya asa gishiri kaɗan a rufe na wasu mintoci sannan asa maggi. 

Farar shinkafa mai manja da tumatir

Shinkafa kofi huɗu

Tumatir guda biyu

Albasa 

Maggi

Gishiri

Manja

Garin yaji

Dafafen kwai

Method of preparation 

Da farko za'a wanke shinkafa a zafka a wanke sannan asake sa ruwa wanda akasan zai iya dafa shinkafar, a dafa ta har ta shanye ruwan in tayi a sauke. Sannan a wanke tumatir da albasa a yanka. Sannan a soya manja da albasa. Sannan a dafa kwai a cire ɓawon. Sannan a zuba dafaffar shinkafar, a zuba mai a saka maggi a zuba yaji asa kwai da tumatir. 

Farar shinkafa da miyar kifi

Shinkafa

Kifi tarwaɗa

Kayan miya

Ganyen ugu

Mai

Kayan kamshi

Method of preparation 

A fara gyara kifi a saka masa kayan ƙamshi da albasa a tafasa shi kaɗan a sauke. 

Sai a gyara kayan miya ayi greting ɗinsu. Sannan a ɗora tukunya asa mai daya fara zafi asa ginger and garlic pest akawo albasa mai ɗan dama a zuba idan ya fara nuna asa kayan miyar nan abarshi har ruwa yaɗan tsotse. 

Sai a kawo kifi a zuba asa ɗanɗano da sauran kayan ƙamshi a zuba abarshi kamar mintuna biyar sai a kawo ganyen ugu a zuba abarshi bayan kamar mintuna uku a sauke. 

Farar Shinkafa da Miyar kayan lambu

Shinkafa kofi 3

Tattasai 9

Albasa 2

Carrots 3

Green beans kofi 1

Cucumber

Maggi

Mai kadan

Cabbage 1

Curry

Method of preparation 

Da farko dai za'a fara tafasa ruwa a wanke shinkafa. Sai a zuba a rufe a bari sai ta tafasa sannan a zuba green beans a bari. 

Sannan ayi parboiling shinkafar a bari ta dahu sai a sauke.

Sai a zuba sliced albasa da tattasai da carrot asa seasonings da curry asa ruwa kaɗan a bari su ɗan dahu. 

Sannan asa cucumber da cabbage a juya a rufe a barshi yayi kamar mintuna biyar a medium heat. Sannan a sauke.

Ayi slicing tattasai,albasa, carrots, cucumber, cabbage a ajiye. A zuba mai kaɗan cikin frying pan a soya su daga nan sai a haɗesu da dafaffun kayan miyar nan su karasa soyuwa.

Farar shinkafa mai zogale da haɗaɗɗiyar sauce

Shinkafa kofi 3

Zogale

Attaruhu 3

Albasa 1

Tafarnuwa guda 2 matsakaita

Koren tattasai 3

Karas 5

Kayan ƙamshi

Kayan ɗanɗano

Kabeji rabi

Method of preparation 

Da farko za'a samu tukunya asa ruwa da yawa sai asa gishiri kaɗan idan ya tafasa sai a zuba shinkafar, amma a wanketa sosai idan tayi laushi ba sosai ba, yadda dai zata ciwu sai a tace idan an tace sai a barbaɗa zogalen wanda ya bushe sai a mayar ta turara.

Sai a zuba mai a tukunya asa albasa me yawa a juya idan tayi laushi sai a zuba duka yankankun kayan miyar nan da nama. Sai asa kayan ƙamshi da kayan ɗanɗano idan sukayi laushi sai asa cabbage shine na ƙarshe shikenan

Za'a samu nama a dafa shi da maggi da kayan ƙamshi idan yayi sai a yankashi ƙanana. 

Farar shinkafa da miyar hanta mai kayan lambu

Shinkafa kofi 3

Mai

Kayan ɗanɗano

Kayan ƙamshi

Attaruhu 5

Albasa 2

Karas 5

Dogon wake 7

Hanta kilo 1

Tafarnuwa

Method of preparation 

Da farko za'a ɗaura ruwa idan ya tafasa sai asa ɗan gishiri sai a wanke shinkafar sosai, sai a zuba idan ta ɗan nuna bata dafe ba sai a tace a mayar ta turara.

Za'a jajjaga kayan miya da tafarnuwa a yanka kayan lambu a wankesu sai a ajiye a gefe. 

Za'a wanke hanta sai a zuba mata ruwa bada yawa ba asa kayan ƙamshi da gishiri kaɗan da ƴar albasa da tafarnuwa. 

Sai a tsameta daga cikin ruwan a zubar da ruwan sai a soya kayan miya asa kayan ƙamshi da ɗanɗano idan ya soyu sai a zuba kayan lambun. Sai asa hantar nan a rufe abarsu kayan haɗin ya ratsa jikinsu. 

Farar shinkafa da kayan lambu da miyar dage dage

Shinkafa kofi 3

Koren tattasai

wake kofi 1

Karas 2

Kayan miya

Mangyaɗa

Nama

albasa 2

Maggi

kayan ƙamshi

Ruwa

Gishiri

Method of preparation 

Da farko in an haɗa komai na miya sai a gyara tsaf a wanke a markaɗa ko jajjage a ajiye. A wanke nama tsaf asa albasa da tafarnuwa asa gishiri kaɗan a tafasa. Bayan ya tafasa sai a soya a rufe a ajiye shi, a ɗauko markaɗen kayan miya a zuba a mai, asa kanwa kaɗan don tsami aci gaba da soyawa.

A ɗauko soyayyen naman a zuba a kayan miyan asa kayan ƙamshi da maggi a rage wuta har su haɗu.

Idan ana buƙatar son ƙara ruwa kaɗan in kuma ba'a so shi kenan miya tayi. Shinkafa in anaso ayi boiling a wanke da gishiri in an tsame sai a ajiye a rufe. A yanka karas, koren wake da tattasai a wanke tsaf.

A haɗa da shinkafar da aka tafasa ɗin asa ruwa kaɗan a mayar wuta a rage wutar ta turara ta ƙarasa. Ba'a so kayan lambun su dafe.

#end of yadda ake sarrafa shinkafa kala-kala article#


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post