Yadda ake sarrafa fulawa

Yadda ake sarrafa fulawa kala-kala

Yadda ake sarrafa fulawa kala kala
Flour, watau garin fulawa ta abinci ko nace garin fulawa da ake amfani da ita wurin haɗa abubuwan cima kala kala, asali ana sarrafa alkama ne a kamfani domin samar da ita. 

Read also

Yadda ake girkin shinkafa ta hanyoyi daban daban

Yadda ake sarrafa fulawa: Ana sarrafa fulawa ayi nau'ikan abinci kala kala musamman waɗannan kayan cimar da ake kira snacks a turance. 

Misalan irin snacks ɗin da ake sarrafa fulawa a samar dasu sun haɗa da;

Cin cin 

Meat pie

Cake

Samosa

Fanke (puff puff) 

Spring rolls

Fish pie

Fanke (Normal) 

Pancakes with honey 

Short bread biscuits 

Flour balls in stew etc.. 

-Cin cin 

Cin cin na daya daga cikin sanannun snacks a kasar hausa tun tali tali. Cin cin abinci ne da ake yinsa a taro kowane iri, haka kuma ana yinsa na sayarwa wanda zaku ga ana tallan sa a cikin roba. 

Abubuwan da ake buƙata domin yin Cin cin (Ingredients). 

Fulawa kofi uku

Butter 

Madarar ruwa

Sugar 

Baking powder 

Yeast 

Ruwa 

Mai

Haɗi (Method of preparation) 

Za'a samu fulawar nan a kwaba ta amma kar tayi ruwa sannan a saka butter da madarar nan a cigaba da juya wannan dough din fulawar. Idan ya kama jikinsa sai a debo kadan daga ciki a shimfida akan board ko tray ana yanka shi dai dai misalin yadda ake so, kafin nan an dora mai akan wuta yayi zafi, daga nan sai suya. 

Ana iya hada cin cin da tea ko soft drinks haka kuma ana iya ci haka kawai. 

-Meat pie

Meat Pie yana ɗaya daga cikin fitattun snacks, watau kayan cima na karɓar baƙi. Wannan nau'in cimar na meat pie yana daga cikin farko farkon snacks ɗin da aka wayesu. An daɗe ana amfani dashi wurin tarɓar baƙi kamar yadda na ambata a sama, haka kuma an jima ana amfani dashi a bikin taro. 

Abubuwan da ake buƙata domin yin meat pie (Ingredients). 

Fulawa

Butter

Gishiri (kadan)

Nama ko kaza

Dankalin Turawa

Attarugu da albasa

Magi

Curry da thyme

Baking powder

Meat pie cutter

Man gyada (in soyawa za'a yi)

Oven (in gasawa za'a yi)

Meat mincer

Haɗi (Method of preparation) 

Bayan an yanka nama ko kaza, sai a silala da magi da curry da thyme da albasa har sai naman yayi laushi. Sannan sai a tsame a zuba a meat mincer a gauraya naman. In babu  meat mincer sai a yayyanka naman ƙanana sannan a jajjaga shi da attarugu. Sai asa mai kaɗan akan wuta kafin a mayar da dakakken naman a yanyanka dankalin turawa, sannan sai a dafa shi, sai a yanka shi ƙanana. Sai a haɗa da dakakken naman a wuta ana gaurayawa. Idan sun nuna tare sai a sauke daga wuta.

Daga nan sai a ɗauko fulawar a zuba butter kamar ƙaramin cokali biyu da baking powder da gishiri kaɗan. Sai ayi ta kwaɓawa da ɗan ruwa kaɗan. Sai anyi masa kwaɓin cincin. Sannan sai  asa shi a tray filla-filla kamar za'a yanka cincin. Sai a ɗauki meat pie cutter a yanka. Sannan sai a zuba kayan su nama da dankalin a tsakiyar meat pie cutter sannan sai a kulle, a soya. Ko kuma a gasa shi a gas. Lallai sai kunnen maigida yayi motsi.

-Cake

Shima dai cake yana ɗaya daga cikin jiga jigan kayan cimar snacks na tarɓar baƙi, haka kuma na fitar kunya a taro. A wannan zamanin akwai nau'ikan cake da ake sarrafawa kala kala wanda wani cake ɗin ma kunnuwanmu basu taɓa jiyo sunansa ba, haka kuma idanunmu basu taɓa gani ba, to a wannan rubutun dai zan karkata ne akan cake irin namu na gida. 

Abubuwan da ake buƙata domin yin cake (Ingredients). 

Kwai guda shida(6)

Butter gwangwani (1)

Sugar cup (1)

Filawa cup(1)

Madara cup(2)

Baking powder (½) tea spoon

Gishiri (½) tea spoon

Flavour

Haɗi (Method of preparation) 

Yadda ake haɗa kayan haɗin cake da farko dai za'a fara da fasa kwai  a haɗa da butter da sugar har sai sun narke, sannan sai a zuba madara da baking powder sai a cigaba da motsawa kada a zuba ruba ruwa a cigaba da motsawa har sai

ta damu sosai, daga nan kuma sai a shafa butter a gwangwanin da za'a gasa sai a zuba kwaɓin a gwangwanin da aka shafa butter sai a gasa shikenan.

-Samosa

Samosa kayan cima ne na snacks mai daɗin gaske, wanda indai taro ya amsa sunansa taro ko wane irine to kuwa ido zai kyallo samosa a cikin kayan kwalamar da aka tanada domin mahalarta wannan taron. 

Abubuwan da ake buƙata domin yin samosa (Ingredients). 

Flour kofi 3

Gishiri pinch

Corn flour chokali 3

Ruwa

Nama (niƙaƙƙen nama) ½ kg

Attaruhu manya 5 (jajjagaggiya)

Albasa matsaƙaita 2 (a yanka ƙanana)

Carrot (Karas babba 1) a yanka kanana

Tafarnuwa

Curry da thyme

Kayan ɗanɗano (dunƙule 3-4)

Haɗi (Method of preparation) 

Farko za'a samu bowl a zuba fulawa da corn flour da ɗan gishiri, sai a kwaɓa shi kamar yadda ake yin dough ɗin meat pie, za'a buga shi sosai har fulawar ta saki jikinta.

Sai ayi rolling ɗinta da faɗi kamar circle, a shafa mai a kan ɗaya sai a barbaɗa fulawa akai, sai a sake ɗora wani dough ɗin, haka za'a yiwa dukkansu, sannan sai a sake rolling ɗin yayi faɗi.

A ɗora wannan fulawar a kan non stick pan na tsawon mintina 2-5, sai a sauke a yanka shi gida huɗu. Kar a sa wuta sosai (medium heat).

Don yin fillings, a dafa nama tare da albasa, attarugu, karas, tafarnuwa, maggi, curry da thyme.

A ɗauko kowane side na dough ɗaya, a saka fillings sai a kwaɓa flour da ruwa don manne bakin samosa ɗin.

Sai a soya samosa a cikin deep frying pan har sai ya soyu.

-Fanke (puff puff) 

Abubuwan da ake buƙata domin yin puff puff (Ingredients). 

Fulawa kofi 1

Sugar 1/3 kofi

Salt pinch

Yeast chokali 1 teaspoon

Mai (na suya)

Haɗi (Method of preparation)

A cikin roba mai zurfi, a zuba flour da yeast da sugar da ruwan ɗumi, a kwaɓa ya kwaɓu sosai, yayi ruwa-ruwa amma ba sosai ba, sai a rufe a wuri mai ɗumi.

Ya sami kamar awa ɗaya, idan yayi, za'a ga ya tashi, sai a ƙara buga shi.Sai a ɗora kasko a wuta, asa mai yayi zafi. sai a rinƙa ɗiban ƙullin da chokali ana sawa a cikin mai. A soyawa kuwa, yayi jar suya.

___________________________________

Yadda ake sarrafa fulawa section B

-Spring rolls

Kamar yadda na ambata a sama yana ɗaya daga cikin nau’ikan abincin snacks wanda hausawa suke yin abincin zamani ba abincin gargajiya ba.

Kuma ana haɗa shi ne da fulawa, a launi kalar ruwan ƙasa ne wanda a ciki ake samashi kayan miya domin a gyara shi. A ɗanɗano yana da sauƙin ci ba tauri ba.

Amfaninsa ga lafiyar mutum kuwa, yana ƙara bada ƙarfin jiki a sanadiyyar fulawa kuma akwai sinadarai na vitamins wanda suke ƙara wa mutum lafiya kamar su Vitamin C.

Abubuwan da ake buƙata domin yin spring rolls (Ingredients). 

Ga kayan da ake bukatar a siyo a kawo kamar haka zan lissafa su ɗaya bayan ɗaya.

Fulawa

Mai

Kwai

Kabeji

Nama

Kyan kamshi (maggi,gishiri da kuma thyme)

Karas

Albasa

Tunda mun lissafa kayan da ake buƙata a sama ga bayani nan zan yi yadda za'a fahimta daki-daki yadda da an tashi yi ba wahala.

Haɗi (Method of preparation)

Za'a samu nama mai kyau sai a wanke shi sannan kuma sai a samu tukunya a ɗora shi a kan wuta a dafa shi ya dahu sosai.

Bayan ya dahu sosai, sai a yanka shi ƙanana sai a daka shi ko kuma a samu blender ayi blending ɗinsa. 

Bayan haka kuma sai a samu karas da kuma kabeji sai a yanka su ƙanana, sai kuma a  kawo mai a zuba a cikin kasko, a zuba su duka da naman, kabejin da kuma karas ɗin duka sai a zuba a soya su. 

Kar a manta asa gishiri da maggi da kuma kori a wajen soyawar ana motsawa amma kar a bari su soyu sosai kaɗan ake so su soyu.

Bayan wannan matakin kuma sai a  samu fulawa a kwaɓa ta, a samata kwai a ciki da kuma ruwa a ɗanyi mata damun laushi haka kamar za'ayi waina.

Daga nan kuma sai a samu kasko a riƙa zuba mai ana soyawa kamar yadda ake waina, daidai suyar waina yadda zatayi falan-falan haka.

Bayan anyi abinda aka ambata a sama sai a ɗauko nama da abubuwan da aka soya shi a matakin farkon dana faɗi.

Sai a samu naman ana yaɓawa akan wannan filawar wadda aka soya kamar waina, ana yaɓawa a saman ta ana nannaɗewa kamar tabarma.

Yadda za'a rufe bakin shine za'a samu kwai sai a riƙa shafawa a bakin filawar shine zai taimaka wajen liƙe filawar yadda kayan baza su fito ba.

A wannan matakin kuma sai a ɗauko kasko a zuba mai a cikinsa sai a samu naɗin da akayi a sama sai a riƙa zubawa a ciki.

Zaɓi yi masa wara-wara yadda ba zai haɗe ba a wajen soyawar, daya soyu kuma sai a sauke a samu wuri a zuba shi, shikenan.

-Fish pie 

Abubuwan da ake buƙata domin yin fish pie (Ingredients). 

Flour kofi uku

Gishiri

Butter

Baking powder

Ruwa

Kifi

Attaruhu da Albasa

Mai

Maggi

Kayan kanshi

Haɗi (Method of preparation)

Da farko a fara haɗa fulawa da butter da baking powder a kwaɓa. Sai a samu kifin a gyara shi sosai a wanke shi a cire ƙayarsa. Sai a zuba a kasko asa maggi da gishiri da kayan ƙamshi da ruwa kaɗan ya ɗan dahu sai a jajjaga attaruhu da albasa a zuba sannan a ɗan sa mai a soya, sai a murza haɗin fulawar a yanka gefen a zuba haɗin a farko a naɗa kamar tabarma asa a abin gashi a gasa.

-Fanke 

Abubuwan da za a buƙata domin yin fanke (Ingredients). 

Butter

Kwai

Madarar fulawa

Fulawa

Sukari

Baking powder/ Yeast

Gishiri kaɗan

Flavor

Haɗi (Method of preparation)

A samu fulawa a tankaɗe ta sannan a jiƙa sukari a dama da ruwa kaɗan a kofi ayi ta gaurayawa har sai ya narke. A zuba fulawa a kwano, a zuba butter kamar cokali 2, a dirzata da fulawa har sai ta ɓata a cikin fulawa. 

Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan ɗumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za'a ga ya ɗan yi kumfa a saman kofin. Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri rubu’in cokalin shan shayi da flavor, a fasa kwai kamar biyu.

Sannan aci gaba da murzawa. A zuba ruwan yeast a kwaɓa sannan, a ɗauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwaɓawa har sai ya ɗan yi kauri haka daidai kwaɓin fanke. Bayan sun kwaɓu sosai sai a rufe na tsawon yini guda. Waɗansu kuma zasu iya jiransa sai ya tashi kafin tuya.

Bayan kwaɓin ya tashi, sai a ɗora man gyaɗa a tukunyar tuya a yanka albasa. Bayan yayi zafi sai a riƙa yankawa daidai girman fanken da ake so. Har sai sun toyu sannan a kwashe a sanya wa maigida a kwanon karyawarsa.

Za'a iya cin wannan fanken da shayi kuma yafi dacewa da karyawa.

-Pan cakes with honey

Abubuwan da za a buƙata domin yin pancakes (Ingredients). 

Filawa

Baking powder

Gishiri

Kwai

Butter ko Mai

Madarar ruwa .

Haɗi (Method of preparation)

A kwaɓa filawa da kwai, gishiri da madara har sai kwaɓin yayi ruwa-ruwa (Ana amfani da madara

a matsayin ruwa). 

A zuba mai ko butter a cikin kasko idan yayi zafi sai a riƙa zuba kwaɓaɓɓiyar filawa ana soyawa,

amma banda juyawa kamar dai yadda ake sinasir.

-Short bread biscuits 

Abubuwan da za'a buƙata domin yin short bread biscuits (Ingredients). 

Filawa

Suger

Butter

Gishiri

Kwai

Haɗi (Method of preparation)

A kwaɓa filawa da kwai, butter da kuma sugar amma kaɗan saboda za'a saka a wurin murji, a kwaɓa kamar yadda ake kwaɓin cin-cin.

A goge katakon murza meat pie a barbaɗa sugar akai sai a rinƙa murza kwaɓin akan sugar ɗin,

idan ya murzu sai a samo gwan–gwanin cake amma ƙanana sai a rinƙa sawa ana fidda

(shape) dashi .

Idan angama sai a shafa kwai akai, a gasa a cikin oven.

-Flour balls in stew 

Abubuwan da za'a buƙata domin yin flour balls in stew (Ingredients). 

Filawa

Ruwa

Kaza ko Nama

Maggi ko [spices]

Tafarnuwa [mint]

Albasa mai lawashi

Mai

Tumatir (Tomtos )

Tattasai ko Attaruhu. 

Haɗi (Method of preparation)

A kwaɓa filawa da gishiri da mai a cikin kwano ayi kwaɓin ruwa – ruwa, a ajiye gefe ɗaya. A zuba kaza ko nama a cikin tukunya, sai a zuba ruwa, gishiri, albasa da citta har sai sun dahu. Idan ruwan ya ɗan tsotse, a zuba tumatir da attaruhu yayi ɗan romo romo.

Sai a rinƙa zuba wannan kwaɓin a cikin miyar da kaɗan da kaɗan (kamar sakin ɗan wake) har sai

angama zubawa, a rufe tukunya har zuwa ƴan mintina idan ya dahu a sauke.

Amma za'a ci da zafinsa kafin yahuce.

Da fatan an ilimantu, idan kuma akwai ilimin to da fatan an ƙaru.

#end of yadda ake sarrafa fulawa post#


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post