Tarihin Kawu dan Sarki

Cikakken tarihin kawu dan sarki post#

Tarihin Kawu dan sarki
A farkon lamari dai Kawu Ɗan Sarki ya shaidawa manema labarai cewa shi kafinta ne kafin ya fara waƙa. Mawakin yace a lokacin da yake sana'ar aikin kafinta, yakan samu naira dubu ko kuma naira dubu biyu a rana, a wajen sana'ar tasa. Kasancewar irin ƙarancin kuɗin da yake samu ne yasa mawaƙin ya karkata akalarsa ya bar aikin kafinta ya koma studio domin yin aiki a can. 

Mawaƙin wato Kawu Ɗan Sarki ya shaidawa manema labarai cewar baije studio neman aiki ba domin yin waƙa, kawai dai waƙar tazo ne bayan ya fara aiki a studio. Kuma mawaƙin ya bayyanawa manema labarai cewar dalilin fara wakar shine neman kuɗi. 

A lokacin da manema labarai suke tambayarsa mai yasa yake saka kalmomin batsa a waƙa, mawaƙin yace shi ba kalaman batsa yake sawa a waƙoƙinsa ba, yace kawai dai yana zurfafa kalamai ne saboda suyi kwari a cikin waƙoƙin nasa. 

Kawu Ɗan Sarki mawaƙine mai fasalin waƙoƙi daban daban, kama daga waƙoƙin soyayya, biki, suna, waƙoƙin siyasa da dai sauransu. 

Mawaƙi Kawu Ɗan Sarki ya fara waƙa ne a cikin shekarar 2015, kuma kama yanzu yayi waƙoƙi da dama a wannan shekarar har zuwa shekarar 2022.

Sai dai ɗaukaka ba ta riskeshi ba sai a shekarar nan ta 2022 bayan ya saki wata waƙa mai taken, "Ingallo" wacce ta karaɗe lungu da kewaye na arewacin najeriya.

Daga baya kuma ya saki waƙar da ta biyo bayan Ingallo mai taken, "Kina A Raina" wacce ita ma ta samu karɓuwa tsakanin hausawa.

 Aina aka haifi Kawu dan Sarki 

An haifi mawaƙi Kawu ɗan sarki a jihar Kano dake arewacin Najeriya yayi karatunsa na firamare da sakandare duka a jihar Kano.

Wasu daga cikin fitattun waƙoƙinsa sun haɗa daga;

Ingallo

Kina a Raina

Sanadinkine

Gyara

Sai Da Ido

Cikon Burina da sauransu.

Wasanni a Ƙasashen ƙetare

Kawu Ɗan Sarki ya yi wasanni a ƙasashen afrika ta yamma waɗanda ke ɗauke da al'ummar hausawa.

Ya yi wasanninsa a ƙasashe irinsu;

Nijar

Kamaru

Cadi

Cote D'ivore da saurasu.

Kawu Ɗan Sarki matashin shahararren mawaƙin hausa ne, marubucin waƙa, mai tasiri, kuma fitaccen jarumi a harkar waƙa. 

Mawaki Kawu Ɗan Sarki ya bayyanawa manema labarai cewa mawaƙi Dauda kahutu rara shine uban gidansa a masana’antar ta kannywood, mawaƙin ya ƙara da cewa Dauda kahutu rara shine wanda ya ɗauki nauyin bidiyoyin mafi yawan waƙoƙinsa. 

Mawaƙi Kawu Ɗan Sarki yace yana da burin barin baya mai kyau a masana’antar ta kannywood. Sannan yace yana fata yaci lokacinsa da kyau haka kuma yana fata ya kafa mutane da yawa. 

Izuwa yanzu dai mawaƙin wato Kawu Ɗan Sarki yana da waƙoƙi aƙalla sun kai talatin da biyu a halin da ake ciki. Mawaƙin ya bayyanawa manema labarai cewa shi baya rubuta waƙa, kawai dai da yaji kiɗa to fa baya tashi sai ya kammala waƙa, sai dai ƴan gyare gyare da ba'a rasawa.

Mawaƙi Kawu Ɗan Sarki yace babbar matsala ko ƙalubalen da yake fuskanta shine mutane da yawa suna zaton ya tara kuɗi ne sosai a yanzu duba da irin masoya daya tara tun daga lokacin da tauraruwarsa ta fara haskawa.

Mu'amalar Kawu Ɗan Sarki da Masoyansa. 

Mawaƙi Kawu Ɗan Sarki yace yana da mu'amala mai kyau tsakaninsa da dubban masoyansa a faɗin duniya, mawaƙin ya faɗa cewa a rana yana samun amsa kiran waya kamar sau dubu biyu daga masoya masu taya shi fatan alheri a sassa daban daban na faɗin duniyar nan. Haka kuma dai mawaƙi Kawu Ɗan Sarki yana amsa saƙonni masu yawan gaske ta hanyar sadarwar whatsapp da kuma sauran shafukansa na sada zumunta a yanar gizo.

Kawu Ɗan Sarki yayi nasarar zama fitaccen jarumin mawaƙin hausa tun sanda ya fara fito da waƙoƙinsa ba tare da gajiyawa ba, sannan ya fito da wani sabon salo na yin waƙa, wanda hakan ya taimaka mai sosai gurin sace zuciyar mutane. Kuma ya girgiza mawaƙa ta hanyar samar da fitattun waƙoƙi daban-daban ba jinkiri.

Daga Shekarar 2021 Zuwa 2023 A tarihin Kawu Ɗan Sarki yayi waƙoƙi fitattu da dama kamar haka:

Kawu Dan Sarki -In Gallo

Kawu Dan Sarki-Ribar So

Kawu Dan Sarki-Wasa Farin Girki

Kawu Dan Sarki-Sanadin Damuwa

Kawu Dan Sarki-Bani Da Kowa

Kawu Dan Sarki-Soyayyace

Kawu Dan Sarki-Cikon Burina

Kawu Dan Sarki-Sanadinkin Ne

Kawu Dan Sarki-A Duniya Ta

Kawu Dan Sarki-Kina a Raina

Ya kuma fitar da waƙoƙi da dama daga baya.

Anan na kawo ƙarshen wannan taƙaitaccen tarihin mawaƙi Kawu Dan Sarki, mawaƙin da tauruwarsa take haskawa ake kuma damawa dashi a masana’antar kannywood. 

Da fatan an nishaɗantu da wannan taƙaitaccen tarihin na Kawu Dan Sarki.

End#of Tarihin kawu dan sarki.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post