Tarihin Maryam Yahaya

Tarihin Maryam Yahaya da Hausa

Kamar yadda muka saba yau kuma zamu yi tarihin Maryam Yahaya jaruma a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood. Maryam Yahaya tauraruwa ce mai haskawa a masana'antar a yanzu.

Tarihin Maryam Yahaya
Wacece Maryam Yahaya

Cikakken Suna: Maryam Yahaya 

Shekaru: Sha bakwai ga watan juli alif dari tara da casa'in da bakwai, 17 july 1997

Iyaye 

Yahaya Bello (mahaifi) 

Ruƙayya Bello (mahaifiya) 

Aiki: Jarumar fim 

Aure: Babu

Gari: Kano 

Kasa: Najeriya 

Maryam Yahaya zaƙaƙurar matashiyar mace kuma shahararriyar jaruma a masana’antar Kannywood wacce ta jajirce ta kuma tsallake siraɗi da yawa wajen ganin ta cimma burinta na zama jaruma wanda izuwa yanzu tayi nasarar cimma burin nata. Ta fara fitowa ne a wani shiri mai suna Taraddadi wanda tayi nasarar shiga jerin waɗanda suka cancanci kyautar karramawa ta jaruma mai nagarta daga city people entertaiment award a shekarar dubu biyu da sha bakwai 2017. 

Maryam Yahaya (An haife ta ne a ranar sha bakwai 17, ga watan julin shekara ta alif ɗari tara da casa'in da bakwai 1997) a unguwar goron dutse. Jarumar tayi karatunta na firamare a yelwa sannan tayi karatunta na sakandire a barikin bukabu a jihar kano amma har yanzu bata cigaba da karatu ba. 

Maryam Yahaya ƴar fim ɗin najeriya ce a masana’antar kannywood. Ta samu yabo ne a dalilin rawar da ta taka a cikin fim ɗin Taraddadi, fim ɗin da el-nass ajenda ya shirya.

Auren Maryam Yahaya 

Har izuwa yanzu da muke wannan rubutu babu wata kafa sahihiya data tabbatar da auren wannan jarumar wasan kwaikwayo.

Saboda rawar da ta taka, an zaɓi Maryam Yahaya a matsayin kyakkyawar ƴar wasa mai kwazo daga City People Entertainment Awards a shekara ta 2017. Hakanan an zaɓe ta a matsayin ƴar wasan kwaikwaiyo ta City People Entertainment Awards a shekara ta 2018.

Maryam Yahaya ta rasu

A'a Har izuwa yanzu haka da nake wannan rubutu babu wata sanarwa data tabbatar da cewa wannan jaruma ta bar duniya wato da ranta idan ma maƙiya ne tofa sai a gaya musu cewa wannan baiwar Allah da ranta.

Kaɗan daga cikin fina finan Maryam Yahaya a masana’antar Kannywood sune kamar haka;

Gidan Abinci 2016

Barauniya 2016

Tabo 2017

Mijin Yarinya 2017

Mansoor 2017

Mariya 2018

Wutar Kara 2018

Jummai Ko Larai 2018

Matan Zamani 2018

Hafiz 2018

Gidan Kashe Awo 2018

Gurguwa 2018

Mujadala 2018

Sareenah 2019

Ɗaukakarta 

Ɗaukakarta ta fara ne a shekarar dubu biyu da sha bakwai, 2017 tun bayan fitowarta a wani shiri mai suna "mansoor" wanda ta fito tare da Bilkisu Shema da kuma Umar M Shareef. Jarumar ta taka rawa sosai wanda hakan ya bata damar fitowa a manyan fina finai. 

Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya fina finan hausa watau kannywood, ya kwana da sanin ɓullar sabuwar jaruma Maryam Yahaya wadda za a iya cewa ta shigo farfajiyar fim da ƙafar dama, kasancewar ta zamo cikin jerin taurarin da ake sa ran za su haska nan da shekaru masu zuwa.

Akwai mamaki matuƙa yadda cikin lokaci ƙanƙani jarumar ta yiwa takwarorinta fintikau wajen yawan fitowa a fina finai masu kyawun gaske, ko da yake ba abin mamaki bane idan aka yi la’akari da kamfanin FKD Production da ya tsaya tsayin daka wajen yi mata babban fim watau MANSOOR,

Maryam, ƴar asalin jihar kano, ta shimfiɗa kwarewarta a farfajiyar, gwana ce ta gwanaye, wadda take yin kyau da zarar an ɗora mata kyamara. Wani ƙarin armashi game da ita shine, yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin jaruma.

Bajintar da ta nuna a fim ɗin, MANSOOR, duk da cewa ba shine fim na farko da ta fara fitowa ba, amma an ga yadda tauraruwarta ta haska (wanda aka gani tun kafin fim ɗin ya fita) shi ne ya janyo mata farin jinin tun kafin ya fita. Tallansa kawai jama’a suka gani, amma suka tabbatar da cewar Maryam Yahaya za ta yi abun kirki a masana’antar fim.

Tun daga nan manyan furodusoshi suka fara nuna ra’ayinsu na sanya ta a finafinansu, kafin kace kwabo jarumar ta kai matsayin da take a yau, na zamowa cikin jerin manyan jaruman da kannywood ke alfahari da su.

Cikin shekara ɗaya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo tauraruwar da kowane lungu da saƙo ake labarinta.

Gwana ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka kowace irin rawa da aka ɗora ta matuƙar ba za a wuce gona da iri ba.

Masana’antar kannywood ta daɗe ba ta samu jaruma da cikin lokacin ƙanƙani ta shige sahun takwarorinta ba, domin an saba ganin yadda wasu jaruman ke ɗaukar shekaru kafin ƴan kallo su gamsu cewar kwararru ne, balle har manyan furodusoshi su riƙa aiki dasu a kai a kai.

Sai dai masana na ganin tagomashin data samu na horo daga wurin maigidanta jarumi Ali Nuhu, shine ummul’aba’isin kasancewarta kwararriya a masana’antar kannywood a yanzu. 

Babban abin da yake ƙara mata farin jini tsakanin abokan sana’arta shine girmama na gaba, karamci, mutunci da sanin girman mutane.

Har ila yau, jarumar ta ɗan yi tsokaci kaɗan game da abubuwan data fuskanta daga gida kafin a amince mata ta fara harkar fim.

“Dole ne duk wanda ya samu kansa a wannan hali zai iya samun matsala, musamman a gidansu za a ji irin ba daɗi ɗin nan. Amma daga ƙarshe ina nuna masu harkar fim sana’a ce tamkar kowane irin aiki, lokacin da kake bakin aiki magana a waya ma jarumi ba shi da damar yi balle ya samu damar zuwa yawo.

"Kuma ina son mutane su sani, fim sana’a ce kamar ko wace masana’anta akwai nagari akwai kuma na banza. Idan ka tsare kanka Allah Zai taimake ka, saboda kai dai ka san me kaje yi, idan kaje iskanci ne kai ka sani, idan ma ka je a wulakance ne kai ka sani idan kuma ka je da mutuncinka Allah Zai kare maka mutuncinka.” A cewar Maryam.

Jaruma Maryam Yahaya ta ciri tuta, ta kafa tarihi a masana’antar kannywood, ta zamo gwana data yi bajintar a zo a gani cikin ƙanƙanin lokaci, alamu sun nuna matuƙar jarumar ta dage kan ƙadamin data taho a kai, babu shakka nan da wani lokaci zata shiga sahun manyan jarumai mata da duniyar fim ke labari.

Cikar jaruma shi ne yin abin da darakta yake so, a lokacin da yake so. Haka zalika rawar da jaruma kan taka a fim kan zamo wani siraɗi na sirrin nasararta. Batun kyau da cikar zati kuwa na ƙarawa jaruma kwarjini a idanun ƴan kallo, ta yadda idan ba jarumar da suke so suka gani a fim ba, bai cika birge su ba.

Haɗaka

Jaruma Maryam Yahaya tayi fim da manyan jarumai da dama kamar;

Ali Nuhu

Adam A Zango

Umar M Shareef

Shamsu Dan Iya

Abdul M Shareef

Amal Umar

Bilkisu Shema 

Maryam Booth da dai sauransu. 

Fitowa a bidiyon waƙoƙi 

Jaruma Maryam Yahaya ta fito a bidiyon waƙoƙi da yawa kamar; 

-Hafeez tare da Umar M Shareef

-Mata zaman tare Garzali Miko

-Jaruma tare da Shamsu Dan Iya

-Mujadala tare da Umar M Shareef da Abdul M Shareef

Yawon ƙasashe 

Jaruma Maryam Yahaya tayi yawo a ƙasashe da dama kamar su;

Saudi Arabia 

Ghana 

Dubai 

Niger 

Gambia da dai sauransu. 

Maryam Yahaya Illness rashin lafiya

A wani lokaci daya wuce, jarumar tayi wata irin rashin lafiya mai tsanani, wanda har hakan yaja hankalin mutane ya koma kanta sannan ya zama sanadiyyar dakatar da fitowarta a shirin fina finai amma dai a ƙarshe ita jarumar da bakinta tace wai rashin lafiyar ba fa yadda mutane suke tunani bane, a cewar ta wai rashin lafiyar tata zazzabi ne kawai. 

A halin da ake ciki jaruma Maryam Yahaya dai ta samu lafiya, a inda ta miƙe ta cigaba da fitowa a shirin fina finai na masana’antar kannywood ɗin daban daban. Haka kuma dai jaruma Maryam Yahaya tana fitowa a bidiyoyin tallace tallace na kamfaninka daban daban. 

Aure

Maryam Yahaya bata da aure. A wata hira da gidan rediyon freedom yayi da jarumar, ta bayyana dalilinta na rashin aure. Fitacciyar jarumar ta bayyana rashin miji shine abinda ya hana ta yin aure. 

"Da aure da mutuwa duk lokaci ne, idan lokacina yayi ai zan daga, babu mijin ne, ku fito ku aureni, rashin miji ne ya hanani yin aure, kunsan maza na wuya yanzu. 

Wannan sune kalaman jarumar a yayin da take amsawa mabiya wannan shirin hirar da gidan radio freedom sukayi da ita. 

Da fatan mai karatu ya ƙayatu da karatun taƙaitaccen tarihin fitacciyar jaruma Maryam Yahaya.

Tarihin Maryam Yahaya post#


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post