Alamomin so na gaskiya

Alamomin so na gaskiya

Alamomin so na gaskiya
Nuna alamar soyayya a wasu lokutan yana da matuƙar wahala a tsakanin maza da mata. Zaka ga mace na son namiji, amma  duk alamar da ta nuna masa dan ya gane tana son shi, amma kuma wasu na ɗaukan hakan wasa. Hakan ma ke faruwa a tsakanin maza. Wasu halayen da za kaga wasu matan ko maza na nuna wa hakan na nufin wani abu a tsakani. Domin sanin mene so na gaske, tare da haka kuma da hanyar da ake ganeta cikin sauƙi, cigaba da karanta wannan rubutun dan wasu kuwa basu iya banbanta tsakanin so da ƙauna. In hakan na ma wahala, wannan rubutun naku ne!

Read also

Alamun soyayya ta bangaren maza

Menene so?  

Abunda ake nufi da kalmar so ita ce haɗin motsin rai, ɗabi'a, da imani masu alaƙa da ƙaƙƙarfan ji na ƙauna, karewa, zafi, da mutunta wani mutum. So wani abu ne da ke faruwa tsakanin mutane biyu kuma yana girma cikin lokaci ƙanƙani ta hanyar sanin shi ko ita da fuskantar matsaloli masu yawa na rayuwa tare. 

An yi ta muhawara mai yawa game da ko soyayya zaɓi ce, abu ne mai dawwama ko mai wucewa, da kuma shin soyayyar da ke tsakanin ƴan uwa da ma’aurata an tsara tane ta ilmin halitta ko kuma ta hanyar al’ada. Ƙauna na iya bambanta daga mutum zuwa mutum da kuma al'ada zuwa al'ada. Kowace muhawara game da soyayya na iya zama daidai a wani lokaci da kuma wani wuri. Alal misali, a wasu lokatai, ƙauna na iya zama zaɓi yayin da wasu kuma yana iya jin ba za a iya kamewa ba.

Wasu mutanen sukan shiga cikin kokwanto akan menene so da kuma ƙauna duk da yake yawancin mutane sun yarda cewa ƙauna tana nufin so mai ƙarfi, akwai rashin jituwa da yawa game da ainihin ma'anarta, kuma "Ina son ki/ka" na mutum yana iya nufin wani abu dabam da na wani dan ma'anoninta ba'a iya faɗarsu duka. Banbancin so da ƙauna daga mahanga ta itace duk son da zakayi wa wani ko wata da har za kaji a zuciyarka/ki bazaki iya rabuwa dasu ba hakan ya zama ƙauna.

Alamomin so na gaskiya post conti..

Yadda ake gane so na gaskiya 

A matsayin ka/ki na saurayi ko budurwa kaga wata ko wani kina so kuma kuka samu nasarar ganawa da juna. In soyayya ta shigo tsakani, to ta hanyar alamomin so ne kawai zaka gane hakan. Akwai alamomi da dama wanda ake gane wa in nasara ta samu. 

Alamomin mace na son saurayi  da gaske 

Yawan Kallo 

Yana daga alamomin kamuwa da so kaga mace tana yawaita kallon ka batare da kasan tanayi ba a wasu lokutan. A matsayin ka na saurayi kaga budurwa kuna yawan haɗa ido da ita. To hakan na nuna tana sonka.

Farin Ciki

A cikin alamomin gane mace na sonka, wannan shine alamar so na gaskiya kaga mace a koda yaushe in tagan ka, kaga tana cikin jindaɗi da walwalar da bazata iya rikewa a zuciyarta ba. Daga lokacin da ka fahimci hakan, ba komai bane face so da ƙauna.

Shiga damuwa

Idan budurwa ta cika nuna damuwa gare ka musamman in wani abu mara daɗi ko wani iftila'in ya faɗa maka, wannan alamar soyayya ce bayyanan na. Wasu lokutan ma zaka ga kamar basu da lafiya amma kuma soboda kai hakan ta faru. Ko kuma in wani abun ya faru tsakaninku kanuna mata kaji haushi. Hakan nasa ta shiga damuwa.

Murmushi

Yawan murmushi na ɗaya daga cikin alamomin soyayya wanda mafi yawancin mata ke nuna wa. Zaka ga mace inka kalle ta tayi murmushi, in tana ma magana, kaga murmushi tare da farin ciki mai ƙayatarwa a fuskar ta. Wasu lokutan ma zaka yi abunda bai kai na ayi dariya ba. Amma sai kaga tana murmushi. So da ƙauna ne ke kawo hakan. Soboda haka maza a lura kada ayi sake.

Yin Magana

Wannan alamar son yafi aiki ne idan kai da ita baku magana ko kuma kuna gaisawa ko a makaranta, wurin aiki ko a tsakanin yan uwan ka ma. Idan ka mace na yawaita ma magana ko da yaushe, koda a ce baka ganta ba, shima ya faɗo cikin ire iren alamomin so da ƙauna. Ta yadda zaka tabbatar da hakan shine in tama magana baka amsata ba, zaka cewa bata ji daɗi ba.

Shawara

Yana da jerin alamomin so kaga budurwa tana yawaita baka shawara a duk sanda kowa ke gudun ka ko in ka shiga wani hali kana neman mafita. Zaka ga tana iya bakin ƙoƙarin ta taga ce wannan abun da kake nema ka same ta ta hanya sassauka.  Duk macen da kema hakan, karka sake wani yasa ka rabu da ita, dan zai sa kayi nadamar yin hakan.

Alamomin so na gaskiya post Conti...

Alamomin namiji na son budurwa da gaske

Farin Ciki

Yana daga alamomin so kiga namji ya yawaita kasance wa cikin farin ciki. So ce kawai zata sa shi hakan. Inbai yi maki magana alokacin ba karki damu, nan ba da daɗewa ba zuciyar sa zata aiko shi. 

Nunaki ga abokansa

In namiji na yawan nuna ma abokan shi ke ko kuma kiran sunan ki a tsakanin abokanshi hakan na nuna cewa kina da matukar mahimmanci a rayuwar sa. Hakan na sa shi cikin jindaɗi da annashuwa. Sai yaji kamar yafi kowa in yayi hakan.

Mutuntaki

Wasu lokutan zaki ga namiji baki mai komai ba, ba abunda ya hada ku, sai kiga duk in ya ganki, gurinsa yaga ya faran ta maki rai dan hakan muradinsa ne. Wannan ma yana daga cikin alamomin so da ƙauna. Amma ba kowacce bace zata gane hakan.

Yawan tambaya a kanki

Duk namijin da kika ga yana yawan tambaya akan ki. Alamar so ce ta gaskiya. Inku ka kwana biyu baku hadu ba ya ringa kiranki ko ya tura maki sako ta hanyar amfani da waya ko kuma ya turo a gaisheki. Toh in hakan ya faru, alamar soyayya ce.

Son ganinki

In baku hadu kwana biyu ba sai ya kira ya tambaye ki ina kika shige. Da kin kalle shi, kiga kuna yawan haɗa ido ko da yaushe. Kada kiyi tunani biyu wannan soyayya ce ba komai ba. Kallon fuskarki na bashi nishadi mai matuƙar ƙayatarwa shiyasa a koda yaushe yake son kallon ki.

Yawan baki kyauta.

Bada kyauta ga budurwa yakan ƙara wa soyayyan namiji ƙarƙo , da kuma tunawa mosoyiya da cewan ana tunaninta. Masoya na gaskiya suna mutunta wa juna, bayar da kyauta ga juna, shima wani ƙari ne. a taƙaice, bayar da kyauta abune mai karfi da gaske, wadanda ake yi ba tare da sanin wanda za'a ba ba yana ƙara zumunci sosai, musamman ma a soyayya.

Daga ɓangaren mace

Kin roƙo

Kasancewa mabuƙaciya da yawan roƙo yana iya kawo matsala tsakanin masoya. Idan kin zamto mai son ganin sa a ko da yaushe, ko kuma ki ringa tunanin shine kawai a duniyarki, toh hakan na nuna kina buƙatar da yawa daga garesa.

Kasancewar mace haka yana kawa gundura ga maza. Kina tunanin wannan halin zai taimake ki wajen riƙe shi, amma yana da haɗari sosai.yana korar sa.

Bashi lokaci sosai 

Nasan na faɗi cewan ɗaukar hutu da kuma samun ƴanci a soyayya yana da kyau, amma a wani ɓangaren, baza ki iya ɗaukan lokaci mai tsawo ba ba tare da shi ba. Idan ba haka ba , mai yiwuwar soyayyar zata mutu.

Soyayya na buƙatar kulawa, don haka, a ringa ɗaukan lokaci tare da shi ta hanyar fira ko wani makamancin hakan don ƙara ƙarkon soyayyar.

Nuna masa godiya

Kowa na son godiya da yabo daga masoyansu, me yasa kike tunanin taki daban ne?

Ko wani ɗan kankanin abu yayi, a gode masa , hakan zata sa ya ci gaba da yin waɗannan abubuwan don ya ganki cikin jin daɗi a ko da yaushe.

Alamomin so na gaskiya post conti...

Abubuwan da ake gujewa a soyyaya ta gaskiya

Yaudara tana da haɗari sosai kuma ta kasance ɗaya daga cikin matsalar da ake fuskarta a yayin soyayya. A yayin da wasu suke kau da fuska a lokacin da suka fara ganin wasu halaye daga masoyan su, wasu sukan fara zargin yaudara sakamakon wasu munanan halayen da masoyan su ke nunawa.

Mummunan canji a tattaunawa

Samun irin wannan canjin a soyayya ba abu bane mai kyau ba. Idan baku samun tattaunawa ingantacce daga masoyan ku, basu bada labarin abunda ya awku a yininsu,  ko kuma a daina faɗa maku "I love you" , mai yiuwar akwai matsala a ƙasa.

Za'a iya gano canji a tattaunawa ta waɗannan hanyoyi kamar haka:

Idan ana share maganganun ku

Canja abinda ake magana akai don rashin natsuwa

Idan ana shiru ba tare da wani dalili ba

Ƙin amsar tambaya idan anyi musu.

Yawan zargi maimakon tattauna matsalar dake ƙasa.

Yin anfani da yaren jiki ta hanyar kulle idanu ko kuma jujjuya su.

Ƙarya

Rashin gaskiya a soyayya babbar haɗari ne. Wannan rashin gaskiyan na iya zamo yin ƙarya kan ita kanta yaudara, ko kuma ƙarya kan wani abu na daban.

Alamomin yaudara game da ƙarya sune kamar haka:

Zaku sami masoyan ku suna muku ƙarya akan wasu irin abubuwa na rayuwa.

Idan ka tambaye su da wa suke tare ko menene suke yi, zaku fahimci rashin natsuwa a tare da su.

Idan masoya sun kasance suna abubuwa a sirri.

Gujewa

Idan masoyi ya zamo mai gujewa, wannan alama ne na yaudara. Wani sahin, mutane masu yaudara sukan guji masoyan su don kar a zarge su ta hanyar auna masu tambayoyi akan inda suka je ko suke.

Hanyoyin gane gujewa a soyayya sun ƙunshi:

Zaku ji kamar an guje ku. Masoyan ku ba su son fita ko yin abubuwa tare da ko kuma zaku fahimci ransu a ɓace idan suna tare daku.

Canjawa a tunani

Idan masoyan ku na nuna kiyayya ga abubuwan da suka zamo suna so a abaya, ku tattauna da su ku gane abun da ya kawo wannan canjin. Amma idan kuna zargin yaudara, wannan alama ne da ke nuna yaudara a soyayya.

Zargi ga yin yaudara.

Idan mutum ya zamo ba shi da gaskiya akan wani abun da yayi, zai iya turo wannan rashin gaskiyan ga wani ta hanyar tunanin shi ma haka yake, su ringa zargin kai ma ai hakan kake yi. A hali irin wannan, masoyan ku na iya zargin ku da yin yaudara ko da ka kasance kana basu alamun gaskiya.

Idan tana zargin ka da yin yaudara, ko in ka tambaye ta tana mayar maka da shi, toh babban alama ne tana yaudarar ka.

# alamomin so na gaskiya


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post