Alamomin so ga namiji

Alamomin so ga namiji 

Alamomin so ga namiji
Sau da yawa mata su kan kasa fahimtar ko namiji ya na son su, ko kuma shaƙuwa ce da abotaka tsakanin su da shi. Ga kaɗan daga cikin waɗansu alamomin da za su tabbatar maki lallai namiji na son ki, so kuma na gaskiya da soyayya.

Soyayya ta kan canza da kuma girma a kowani lokoci, kuma mutane su kan nuna ta ta hanya daban-daban. Ko wani irin matsala a soyayya mai wucewa ce in har muka kasance a shirye don ganin cewa mun magance su.

Also read

Alamomin soyayya a gaskiyance

Menene alamomin so ga ɗa namiji ?

Su dai alamomin so ga namiji sune alamomi ko waɗansu signs da yake nunawa waɗanda kuma ake iya gane su kai tsaye idan har namiji yana son wata yarinya ko kuma wata mace. Duk yadda namiji ya so ya ɓoye waɗannan alamomin ko kuma ita soyayyar kacokan ga wacce yake yiwa to fa indai mutanen dake kewaye dashi suna da lura, to lallai ne zasu harbo jirginsa ko ba daɗe ko ba jima, saboda idan ya iya ɓoye wasu alamomin to wasu alamomin ba zasu ɓoyu ba. 

Yawan Kallo 

Yana daga alamomin kamuwa da so namiji ya yawaita kallon mace ba tare da tasan yana yi ba a wasu lokutan. A matsayin ki na budurwa kika ga saurayi kuna yawan haɗa ido da shi. To hakan na nuna yana sonki.

Farin Ciki

Yana daga alamomin so kiga namji ya yawaita kasancewa cikin farin ciki. So ne kawai zai sa shi hakan. In bai yi maki magana a lokacin ba karki damu, nan ba da daɗewa ba zuciyar sa zata aiko shi. 

Shiga Damuwa

Idan namiji ya cika nuna damuwa gareki musamman in wani abu mara daɗi ko wani iftila'in ya faɗa miki, wannan alamar soyayya ce bayyanan na. Wasu lokutan ma zaki ga kamar bashi da lafiya amma kuma soboda ke hakan ta faru. Ko kuma in wani abun ya faru tsakaninku kika nuna masa kinji haushi. Hakan nasa ya shiga damuwa.

Murmushi

Yawan murmushi na ɗaya daga cikin alamomin soyayya wanda mafi yawancin maza ke nuna wa. Zaka ga namiji in mace ta kalle shi yayi murmushi, in tana masa magana, kaga murmushi tare da farin ciki mai ƙayatarwa a fuskar sa. Wasu lokutan ma zata yi abunda bai kai na ayi dariya ba. Amma sai kaga yana murmushi. So da ƙauna ne ke kawo hakan. 

Yin Magana

Wannan alamar son yafi aiki ne idan ke da shi baku magana ko kuma kuna gaisawa ko a makaranta, wurin aiki ko a tsakanin yan uwan ki ma. Idan  namiji na yawaita yi miki magana ko da yaushe, koda a ce baki ganshi ba, shima ya faɗo cikin ire iren alamomin so da ƙauna. Ta yadda zaki tabbatar da hakan shine in yayi miki magana baki amsa shi ba, zaki ga cewa bai ji daɗi ba amma fa zai cigaba da yi. 

Shawara

Yana cikin jerin alamomin so kiga saurayi yana yawaita baki shawara a duk sanda kowa ke gudun ki ko in kika shiga wani hali kina neman mafita. Zaki ga yana iya bakin ƙoƙarin sa yaga cewa wannan abun da kike nema kin same sa ta hanya sassauƙa.  Duk namijin da ke miki hakan, karki sake wani yasa ki rabu da shi dan zai sa kiyi nadamar yin hakan.

Alamomin so ga namiji post Conti...

Nuna ki Ga Abokansa

Abokanai suna daga cikin alamomin da zaki fahimce cewa namiji yana ƙaunar ki. Ki kula in abokanin sa na gayama ki cewa baya da aiki sai masu hirar ki, abu kaɗan zai ce "wance kaza" toh wannan mutum yana sonki.

In namiji na yawan nuna ma abokan shi ke ko kuma kiran sunan ki a tsakanin abokanshi hakan na nuna cewa kina da matuƙar mahimmanci a rayuwar sa. Hakan na da shi cikin jindaɗi da annashuwa. Sai yaji kamar yafi kowa in yayi hakan.

Mutunta ki

Wasu lokutan zaki ga namiji baki mai komai ba, ba abunda ya haɗa ku, sai kiga duk in ya ganki, burinsa yaga ya faran ta maki rai dan hakan muradin sa ne. Wannan ma yana daga cikin alamomin so da ƙauna. Amma ba kowacce bace zata gane hakan.

Yawan tambaya a kanki

Duk namijin da kika ga yana yawan tambaya akan ki. Alamar so ne na gaskiya. In akai kwana biyu baku haɗu ba ya ringa kiran ki ko ya tura maki saƙo ta hanyar amfani da waya ko kuma ya turo a gaisheki. Toh in hakan ya faru, alamar soyayya ce.

Son Ganinki

In baku haɗu kwana biyu ba sai ya kira ya tambaye ki ina kika shige. Da kin kalle shi, kiga kuna yawan haɗa ido ko da yaushe. Kada kiyi tunani biyu wannan soyayya ce ba komai ba. Kallon fuskarki na bashi nishaɗi mai matuƙar ƙayatarwa shiyasa a koda yaushe yake son kallon ki.

Kowa na buƙatar wuri ko kuma lokaci a wajen soyayya. Masu bayar da shawara kan soyayya sun tabbatar da hakan ya kamata, kuma yin haka yana da tasiri da gaske a soyayya.

Hidimtawa wacce yake so

Kasancewa a rayuwa buƙatu basa yanke wa bawa, saurayi idan yana son budurwa zai ke yi mata hidima, a wasu lokutan ma zai iya shiga takura idan har yayi hidimar. Sai dai kuma duk da hakan maza da yawa zaku ga sun jure sun ƙeƙashe har sai sun hidimtawa masoyiyar su. 

Bada lokacin sa ga wacce yake so

Namiji idan yana son mace zai iya ware wani lokaci na musamman ya bata shi kacokan domin zantawa da ita. Duk irin harƙallolin dake kansa zai sauke su domin bawa masoyiyar tasa lokaci. 

Soyayya na buƙatar kulawa, don haka, a ringa ɗaukan lokaci tare da shi ta hanyar fira ko wani makamancin hakan don ƙara ƙarkon soyayyar.

Alamomin so ga namiji post conti...

Tausayi

Wani feeling ne da ke ratsa zuciyar duk wani namiji da ya kamu da ciwon son mace. Tausayi yana ɗaya daga matakan farko da ke tabbatar wa mace lallai namiji yana gab da, ko kuma ya kamu da sonki. Zaki ga abu kaɗan  wanda bai taka kara ya karya ba, namiji yana tausayawa mace, ciwo kaɗan zaki ga yana nuna matuƙar kulawar sa da tausayin sa gare ki. Ƴar uwa ki kula duk namijin daya ke jin tausayin ki, toh yana maki son gaskiya. 

Sadarwa

Idan namiji yana matuƙar sonki, za ki riƙa samun kiran wayar sa akoda yaushe, baya iya zama na tsawon lokaci ba tare da ya kira yaji lafiyar ki ba. Yakan so ki zama farkon wacce zai yi magana da ita bayan tashin sa daga bacci, haka kuma ta ƙarshe da zai yi sallama da ita kafin ya kwanta. Zaki riƙa samun saƙon sa na wayar sadarwa (SMS). Haka kuma idan kika masa flashing duk abinda yake yi zai ajiye sa, ya kira wayar ki, ko ya dawo maki da  saƙon da kika tura masa. Yar uwata ki kula namijin da baya damu da ya kira ki ba, sai in ke kin gaji dan kanki kin kira sa, ko kin tura masa sako, toh baki cancanci ɓata lokacin ki garesa ba.

Kasancewa dake 

Namiji kan so kasancewa tare da wacce yake so akoda yaushe, baya gajiya da ganinta, duk yanda ba yada lokaci zai saman maku lokaci don kasancewa tare da ita. Duk namijin da baya kiran ki, sai dai ke dan kanki ki nemi ko haɗu, toh shima ƴar uwa ina maki tsoron in wannan namijin da gaske yana sonki. Saboda wanda ke sonki na gaskiya, yana son kasancewa da ke

Satar kallonki 

Namijn da ya kamu da sonki, baya gajiya da kallon ki. Idan kuna tare ki kula, abu kaɗan zaki yi, zai tsura maki ido, wani lokaci ma zaki kama sa yana satar kallon ki. Haka kuma zai riƙa ƙoƙari ya tausasa idon sa wurin magana da ke, in kika kula zaki iya hango tausayi da soyayya a idon sa. 

Gabatar dake ga danginsa

Duk namijin da ke ƙaunar ki saboda Allah, zaiyi ƙoƙarin gabatar da ke ga ƴan uwansa da abokanan sa. Baya jin kunya ko wani haufin nuna ki a matsayin wacce yake so, yake kuma fatan zama uwar 'yayan sa. Ƴar uwata ki kula, duk namijin da kike zaune da shi, yana maki boyon kisan asalin sa, ko iyayen sa, da abokanin sa, toh wannan namiji yana da wata manufa daban gareki, yar uwa kiyi hakuri ki kama gaban ki, ina shaida maki zai bata maki lokaci ne ga banza. 

Yarda da aminci

Namiji na yarda da amincewa ga macen da yake so. Zai riƙa gaya maki sirin sa, musamman dangane ga abinda ya shafi aikin sa. Zai gaya maki sirri kansa da yake tsoron gayawa abokanin sa, saboda ya yarda da ke, baya taɓa tunanin zaki toni asirin sa. Idan namiji na maki ɓoye ɓoyen sirrukan sa, toh ki bincike son da yake maki.

Alamomin so ga namiji post conti....

Kyauta

Kyauta na ɗaya daga cikin alamomin da za su tabbatar maki cewa namiji na sonki, so na gaskiya. Wanda ke sonka baya jin ƙiwar ma kyauta, ko da ko mutumin nan talaka ne, ako yaushe fatan sa yayi abinda zai faranta maki rai, ta hanyar saya maki wani abu ko mai ƙanƙantar sa, muddin yasan zai saya ki farin ciki. Sai dai ba lallai bane a samu ko wane namijin a hakan, saboda shi alkhairi daga jini ne, wani duk son da yake maki, sai ki same sa marowaci, baya iya wa ko kansa alkhairi balla ya yi maki. Yar uwa sai ki kula in dai kin samu wasu daga cikin alamomin da a ka kawo, amma kuma kin same sa da halin rashin maki kyauta, sai kiyi hakuri, rowar ajinin sa take.

Bada kyauta ga budurwa yakan ƙara wa soyayyan namiji ƙarƙo , da kuma tunawa mosoyiya da cewan ana tunaninta. Masoya na gaskiya suna mutunta wa juna, bayar da kyauta ga juna, shima wani ƙari ne. a taƙaice, bayar da kyauta abune mai karfi da gaske, wadanda ake yi ba tare da sanin wanda za'a ba ba yana ƙara zumunci sosai, musamman ma a soyayya.

Tsara rayuwarsa da ke

Ƴar uwa ki lura, a duk lokacin da kuna tare da shi, yana kawo zancen auren ku, kamar ya ce maki; lokacin auren mu za ayi kaza, ko kuma ƴaƴan mu kaza, yana dai ƙoƙarin tsara rayuwar sa tare da ke. Toh wannan mutunen yana maki so na gaskiya, so kuma na aure. 

Faƙat!

End of the alamomin so ga namiji


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post