Mahaifiyar Fati Washa

Wacece mahaifiyar Fati Washa ?

Mun gabatar da bincike cikin kulawa kuma iya iyawarmu akan wace mahaifiyar fati washa, ga kuma abinda muka taho dashi.

Mahaifiyar Fati Washa

Kamar dai yadda muka sani, jaruma Fatima wacce aka fi sani da washa tauraruwa ce a masana'antar shirya fina-finai ta kannywood, kuma kamar yadda ahlan kabir ya binciko ya tabbatar da cewa mahaifiyarta mai suna Nana Aisha haifaffiyar birnin Bauchi ce dake arewacin Najeriya. Haka zalika kuma wata majiyar tace mahaifiyar fati washa yar asalin jihar Adamawa ce kuma tanada alaƙa da Fulani. shekarun mahaifiyar fati washa an ƙiyasta zaku kai aƙalla hamsin da wani abu, kyakkyawar gaske ce kamar yadda yarta ta kasance kyakkyawa, da alama dai jarumar ta biyo mahaifiyarta sosai wajen kama.

Mahaifiyar Fati Washa

Ta bangaren mahaifi kuwa, Fatima washa tanada mahaifi wanda ya kasance cikakken bahaushe kuma ɗan asalin garin Bauchi, duk da bamu da sani akan ainihin sana'ar mahaifinta amma majiyoyi da dama sun ce maaikacin gwamnati ne, a halin yanzu yana raye ko yana mace Allah shi ya barwa kansa sani.

Wacece ita kanta fati washa:

An Fati Abdullahi Washa an haifeta a ranar Ashirin da ɗaya 21 ga watan Fabrairu na shekara ta alif dari tara da casa'in 1990 a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya, kuma tayi karatu na firamare da sakandare duka a wannan jiha tasu wato Bauchi.

Fati washa ta kasance tauraruwa mai haskawa kuma gogaggiyar jaruma a masana'antar Hausa ta kannywood, wacce ake matuƙar yabawa hazaƙarta da kuma ji da ita kuma tayi tashe yadda ya kamata, yanzun ta ɗanyi sanyi sakamakon lokaci kunsan kowa da nasa lokacin, har izuwa yanzu ana damawa da ita a industry, ta kuma ƙaro wuta a sabbin fina-finanta. Jarumar ta kannywood ta samo sunanta ne na washa saboda yawan fara'arta da dariya a cikin shirye-shirye. 

Fati Abdullahi Washa tana daga cikin jerin matayen da ake saka su a manyan yan'mata kuma taurarin kannywood, izuwa yanzu da nake wannan rubutu Fati Washa ba wani labari daya riskeni na aurenta ko wani abu makamancin haka, a matakin karatunta tanada satifiket na gama sakandare. Amma kuma kamar yadda ta faɗa tanada burin cigaba da karatu.

Jarumar ta ƙware wajen iya hawa waƙoƙin Hausa, har wasu daraktocin suna matuƙar yaba iyawarta, fagen kafce ma ba'a barta a baya ba domin kuwa tana taka muhimmiyar rawa a fagen acting, a cewar wasu bayanai da muka binciko washa fati tayi soyayya da babban jarumi a masana'antar ta kannywood wato Adam a Zango, wacce har sun ɗauki hanyar yin aure sai kuma maganar ta lalace, tayi fina-finai da dama a kannywood, musamman ma kuma yanzu data zama babbar tauraruwa a cikin shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango na (Labarina).

Wanda sakamakon rashin tsohuwar jarumar data fara take wasa wato Nafisa Abdullahi yasa aka nemi Fati Washa domin ta maye gurbinta, hakan kuwa ya biyo bayan jajircewarta da hazaƙarta, wannan ya zama babbar nasara da ƙarin ɗaukaka ga jarumar a cikin faɗin masana'antar, shigarta cikin shirin dogon zango na Labarina. Sannan kuma ta albarkatu da samun wani suna da yin fice a wani shiri mai suna Manyan Mata wanda jaruma Hadiza Aliyu Gabon ke ɗaukar nauyi. Babban burin gida nawa shine samar da bayanai domin masu nema, mahaifiyar Fati Washa kuma bincike ya tabbatar da cewa sunanta Nana Aisha.

Wasu daga cikin jerin fina-finan jaruma Fati Abdullahi Washa:

1. Na gaba

2. Makahon Gida

3. Make Da Bake

4. Ya daga Allah

5. Yar Tasha

6. Ana Wata ga Wata

7. Baya da Kura

8. Fari Da Baki

9. Farida

10. Labarina


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post