Kalaman soyayya masu dadi, ratsa zuciya, nishadantarwa, kwantar da hankali, ratsa jiki da jijiyoyin da sanyi

KALAMAN SOYAYYA MASU DA DADI

A kullum burinmu mu kyautatawa kowa sannan mu daɗaɗawa masoya shiya mukai rubutu kan kalaman soyayya masu dadi, kalaman soyayya masu ratsa zuciya, bamu tsaya nan ba akwai kalaman soyayya masu nishadantarwa, kalaman soyayya masu kwantar da hankali dama kalaman soyayya masu sanyi. Da bincike yayi bincike mun haɗo har da kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin masoya, zuwa ga budurwa ko saurayi.

Kalaman soyayya masu dadi - ratsa zuciya - nishadantarwa - kwantar da hankali da sanyi 2024

Gareku masoya ko nace lovers!.. 

Idan kana ko kina tare da budurwarka ko saurayinki, ya kasance kanayi mata ko kinayi masa kalamai masu daɗi na jan hankali, waɗanda zasu ɗinga faranta mata ko faranta masa rai. A yau zaku samu duk abinda kuke buƙata kamar haka kalaman soyayya masu dadi - ratsa zuciya - nishadantarwa - kwantar da hankali da sanyi.

Kalaman soyayya masu dadi section a

*Na daɗe ina kallon taurarin samaniya yayin da naga wacce tafi kowacce haske, sai naga bakowa bace nake gani ba sai ke masoyiyata. 

So gamon jinine, haƙiƙa sonki ya zamo jinin jikina. Kin fita daban a cikin mata.

*Duk lokacin dana kalleki, sai naga kamar babu kyakykyawar mace sai ke, ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kaɗai. Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.

*Farin ciki baya ɗorewa a rayuwa sai tare da baƙin ciki, dan haka kowane hali nake bazan taɓa mantawa dakai ba masoyina. Nakan raba dare ina tunaninka abin bege na. 

*Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a ƙasa, haka sonka ya mamaye dukkan jikina.

*Ina ma ace na kasance dake a duk bugun numfashina, ƙaunarki ce take ƙara tasiri a ruhina, babban burina naga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarta taki, ya kuma zamana nine sanadin hakan.

*Kina da wadatar abin da mata da yawa suke nema sun rasa, ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kaɗan ne, da a ce na iya rubuta labari da akan fuskarki zan rubuta littafi mai suna masoyiyata. 

*Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran ƙasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki, bata gushewa kamar yadda taurari basa gushewa a sararin samaniya, bata ƙafewa kamar yadda teku baya ƙafewa, haka zalika bata bushewa kamar yadda ciyayi sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar birnin zuciyata. Da akwai wanda zai tsaga jikina da yaga jininki yana gudana, a kan ƙaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika ɓoye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki, kin kasance a fatar leɓena. 

*Duk wani taku da nayi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya yayi min saƙa tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.

*Ganinki ne burina, idanuwana a cikin bacci ko idan na farka, ki amshi soyayyata abadan kada na koka bani barinki cikin ƙunci yaki zo nayi miki tarba. 

Kalaman soyayya masu dadi section b

*Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tunanina kece jin daɗina kuma kece ɓacin raina ke kaɗai ce a zuciyata, kalamaina, zaɓina jin daɗina, ɓacin raina, saboda dake kawai nake rayuwata, ƙaunarki ce ke kula dani take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni, kasantuwata zan zamana a tare dake har abada. 

*Kamar yanda baki bai isa ya furta ba, haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya tayi kaɗan ta kwatanta, ruhinki ne kaɗai yasan yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare, ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.

*Soyayyata dake bata mutuwa kuma bata tsoron mutuwa koda za'a yi mana kwace, ko da zamu mutu ko zamu lalace to soyayyar mu zata kasance a raye, na bayar da zuciyata na karɓi taki na kamu da sonki. 

*Ki tallafi rayuwata data tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar data shagala a kan tsananin soyayyarki kada rintsi ko zugar mahassada yasa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana danƙare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke danƙare a kan ɗan adam, da a ce zan samu ikon fito miki da shi da nayi domin ki ƙara gasgata tsananin ƙaunar da nake miki.

*Na sanya jarin da har yanzu nake samun ribarsa, amma babu asara. Asusun dana sanya jarin nawa bako wane asusu bane sai zuciyarki. 

*Kinyi min miliyoyin ƙananan abubuwan da suka kawomin farin ciki a raina. Kinyi ruwa kinyi tsaki a cikin birnin zuciyata yake masoyiyar raina. 

Daɗaɗan kalaman soyayya idan suka shiga cikin birnin zuciyar masoyi sukan samu wani bigire mai yawa su kuma zauna daram. Tura masa/mata kalamai na soyayya masu sururutar haɗe da shagaltar da zuciyar masoyi kamar haka;

*Ya ma'abociyar/ma'abocin kyan fuska da kamala ki/ka buɗe min ƙofar zuciyarki/ka na shiga ciki na wataya.. 

*Ka/ki nasawa na mance yadda ake numfashi. Haka zalika kece/kai ne madubin dubawa.. 

*Kowa tara yake bai cika goma ba, amma kai/ke ka/kin kusa.. Abinda kaɗai nake buƙata a yanzu kai/ke ne/ce..

Kalaman soyayya masu dadi section c

*Ina sonka/ki jiya amma nafi sonka/ki yau, kuma zan fi sonka/ki a gobe.

Na ƙagu na dawo gida domin nayi katari da kyakkyawar fuskarka/ki.. 

*Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a haɗa son da nake yi musu da kuma na wadda take a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.

*Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki daki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya daya ce babu wadda zaki ɗauko ki sauya a lokacin da baƙin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar taki.

*Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm! saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda na samu wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai bane ba face "KE" masoyiyata, ina son ki.

*A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa take tare da ƙara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu, kada ki manta dani ki kasance mai yin tunani na kamar yadda nima na kasance a koda yaushe.

*Abun dana keji a dangane da kai gaskiya ne kaima na san ka san da haka cewa ina son ka, a duk lokacin daka bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ka.

*So tamkar wata sarƙar zinari ce da ta ɗaure zuciyoyinmu a waje guda, a duk lokacin daka tsinka wannan sarƙar tofa ka tabbatar da cewa tamkar ka kore farin ciki ne daga cikin zuciyata.

*Ina son ka, meya sanya kake yin kokwanto a bisa kalmar so dana furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haɗuwa da shi ya kore min baƙin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciyata, ya yalwata murmushi a saman fuskata hakane dalilin da ya sanya nake kiran ka da "SADAUKI". Kayi nasara kayi nasarar jan ra’ayin soyayya ta akan ka, kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko dana taɓa furtawa kalmar "SO" kuma a yanzu ma zan kara mai-maitawa a gare ka, ina son ka.

*Ka amince muyi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun daya kai samun masoyi daɗi, a duk lokacin dana rasaka ban san halin da zan shigaba, daga ƙarshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikinka a koda yaushe.

*Sarauniyar ƴan mata kyawawa mai cikar haɗuwa a matsayin mace, kisani inasonki sosai na kuma yi missing ɗinki sosai love you.


KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYA

A koda yaushe ka kasance mai kula da budurwarka ko matarka domin hakan shine zai nuna musu irin kaunar da kuke yi musu kema haka karki bari wata ta kwace miki abun alfaharinki.

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya section a

*Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke ƙawatawa da kallonsa, hanci yaji daddaɗan ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba zata yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka nima ba zan iya rayuwa ba tare dake ba.

*Masoyiyata gaskiya nayi nishaɗi da wayarmu ta jiya sosai domin kuwa kin nunamim cikakkiyar kulawa Love U so much!

*Idan rayuwa ba zata yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Jin daɗi da walwala ba zasu taɓa samuwa a tattare dani ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata. Kin zama tauraruwa dake haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke a lambun zuciyata.

*My lovely one kana araina pls ka faɗa min me kayimin na yarda dakai lokaci guda bayan kuma ni ba haka nake yarda da namiji lokaci ɗaya ba, kuma anya kana sona kuwa? Nasan kana sona a baki amma bansan zuci ba, amma fa idan harkana sona ya kamata ka nunamin kulawa aha!

*Hi ƴan mata da fatan kina cikin nutsuwa ana sauraren wa'azi da kyau, kin sace zuciyata soyayyarki ta mamayeni tunanin ki yazama aikina kowane lokaci Love U! So Much..

*Babbar yarinya kin sace zuciya ta, tunaninki da kuma jin muryarki sune muradina da fatan zaki wayi gari lafiya Love you!

Jin daɗin soyayya da mace shine ku kasance tare a koda yaushe, sannan kuna buƙatar wasu kalaman soyayya gajeru domin inganta wannan soyayyar, kalaman kaɗan ne amma suna da ma’ana sosai.

*Mutane suna cewa hoto yana nuni da kalmomi masu yawa, amma ni ba abunda na gani sai kalmomi uku: “I Love You”

*Ina kewarki ldan ba kya kusa dani, idan bana tare dake ba abunda nake sai tunanin ki, idan ina tunanin ki sai naji kawai ina son nayi rayuwa dake, idan nayi rayuwa dake shine mafarkina zai zama gaskiya.

*Naga cikar kamalar ki, kuma nace ina son ki, yayin dana ga rashin cikar kamalar ki, sai naji na ƙara son ki sosai!

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya section b

*Tunani na yana da damar zuwa ko ina ne, amma ina mamakin yadda yake zuwa ga naki tunanin ko da yaushe.

*Na faɗa soyayya a lokuta da dama saboda ke!

*Rayuwa babu ke kamar karyayyen alƙalami ne wanda bashi da amfani.

*Kin cancanci mallakar wannar duniyar, bazan iya baki ita ba, amma zan iya baki duniyata.

*Kafin na haɗu dake, ban taba sanin daɗin da ake ji har yasa murmushi ba!

*A wasu lokutan idan ina tunawa dake idan bakya nan, sai nayi murmushi, sai mutane su min zaton ko na haukace ne!

*Zuciyata tana fara tafiya yawon duniya, da zarar tayi arba da kyawawan idanun ki.

*Sauraron sassanyar muryarki, shine yake tada hankalin tashin hankalin dake zuciyata, sai naji sanyi a cikin zuciyata.

*Nakan samu nutsuwa sosai idan ina kusa dake.

*Ina sonki, ba dan yadda kike ba, sai dan yadda nake idan ina tare dake!

*Zan iya jarraba rayuwa babu ke, amma nasan a hanya zan faɗi matacce.

*Ɗaruruwan zukata sunyi kaɗan su ɗauki soyayyar da nake miki.

Kalaman soyayya masu ratsa zuciya section c

*Nakan faɗa soyayya sabuwa a duk lokacin dana kalle ki!

*Koda yaushe kece amsata idan wani ya tambayeni wa nake tunawa.

*Zan iya haura dutse duk girman shi, kawai dan na haɗu dake, zan iya tafiyar kilo mita dubu dan na zauna dake, ke wata jin daɗi ce ga ruhina. Ina son ki.

*Ke sarauniya ce a zuciyata; Sakan ɗaya baya wucewa ba tare da nayi tunanin ki ba, koda yaushe cikin begen ki nake.

*Taya mace ɗaya zata iya mallakar duk wasu abubuwan da mace ke buƙata na ƙawatuwa? Kece mafarkina. Kyakkyawar zuciyar ki da murmushin ki mai daɗi sune mafi kyawun bangarorin jikin ki.

*A wasu lokutan nakan tsinci kaina ina tunanin lokacin dana fara sanyaka a idanuna. Tun a wannan lokacin nasan na haɗu da mahaɗin zuciyata. Tun daga wannan lokacin, iya abinda nakeso a rayuwata shine kasancewa dakai. Duk yadda rayuwa tayi tsanani, duhu ya mamaye ni kallon fuskarka kaɗai, yana haskakani ya kuma mamaye duhun daya rufeni. Babu komai a cikin zuciyata sai kai, kai kaɗaine tare da tunaninka kuka taru kuka cika min zuciya. 

*A cikin dubban ko miliyoyin mutane, idanuna ke kaɗai suke nema. Kisani masoyiyata ke zara ce a cikin miliyoyin taurarin mata, kece tauraruwarsu kece ƴar autarsu, kuma kece kike haskaka su indai a cikin zuciyata ne. 

*Ina so kasan cewa babu wanda zai iya chanjaka ya ɗauke matsayin da kake dashi a zuciyata ya canja shi. Tunaninka daban ne a cikin zuciyata. Kallon cikin idanunka yana sanyaya ruhi na, begenka shine abincin zuciyata.


KALAMAN SOYAYYA MASU NISHADANTARWA

Ita soyayya ta kasance wata ni'ima wacce ubangiji ya saukar a zukatan masu yinta, aba ce mai matuƙar amfani a rayuwar kowane ɗan adam saboda kowa ya buƙata. Shin yaya kake ji ko kike ji idan kina tareda masoyinki ko masoyiyarka? Nasan ko ba'a bamu amsa ba to tabbas akwai dadi.

Kalaman soyayya masu nishadantarwa section a

(1). Kamar yacce kowace bishiya keyin rassa a sama, kuma tayi saiwa a ƙasanta, haka sonki ya mamaye dukkanin jikina, idan na kalleki sai naji wani farinciki, idan naji zazzaƙar muryarki sai nishaɗi da walwala tareda annashuwa gami da farinciki su lulluɓe zuciyata!

(2). Abinda nake ji a dangane dake gaskiya ne kema nasan kinsan da haka cewa inason ki, a duk lokacin da kika barni bazan iya motsawa koda nan zuwa can ba, wannan shine abinda zai faru dani a duk lokacin dana rasa ki.

(3). So kamar wata sarƙar zinariya ce data ɗaure zuciyoyinmu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka wancan sarƙa tofa ki tabbatar da cewa kamar kin kore duk wani farinciki ne daga cikin zuciyata.

(4). Ina sonka, meya sanya kake yin kokwanto a bisa kalmar so dana furta a gareka?

(5). Tabbas kaine mutum na farko da haɗuwa dashi ya koremin bakinciki na, ya wanzar da farinciki a zuciyata ya yalwata murmushi a saman fuskata haka ne dalilin daya sanya nake kiranka da suna sadauki. Kayi nasarar jan ra’ayin soyayyata a kanka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko dana taɓa furtawa kalmar so kuma a yanzu ma zan ƙara maimaitawa a gareka ina sonka.

(6). Ka amince muyi tsaftatacciya kuma ingantacciyar soyayya. Sai a yau na gano cewa a duniya babu abinda ya kai samun masoyi daɗi, a duk lokacin dana rasa ka bansan halin da zan shiga ba, daga ƙarshe ina mai sanar da kai cewa burina yanzu a duniya bai wuce na ganin ranar da zaka zamo angona ni kuma na zamo mata a gareka, ina alfahari da kai a duk inda na kasance a kowane lokaci, ka huta lafiya daga mai son ganin farincikin ka a koda-yaushe.

(7). Yana ɗaya daga babban burina naga bayyanar fitar murmushi akan wannan kyakkyawan fuska taki, ya kuma zamana cewa nine sanadin yin wannan murmushi naki.

(8). Bana fatan Allah ya kawo lokacin da za kiyi fushi dani sosai, domin kaina bazai iya ɗauka ba.

(9). Na ɗaga kaina sama na daɗe ina kallon taurarin dake sararin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga ba kowa bace na ke gani ba saike masoyiyata! so gamon jinine, haƙiƙa sonki ya zamo jinin jikina!

(10). Kin fita daban a cikin yan mata, duk lokacin dana kallleki, sai naga kamar babu kyakkyawar wata mace bayan ke!

Kalaman soyayya masu nishadantarwa section b

(1). Haƙiƙa Allah ya wadata ki da abinda mata da yawa suke nema kuma sun rasa. Babu ko shakka mata irinki kaɗan ne, ke da ace na iya rubuta labari, to da tabbas akan kyawun fuskarki zan rubuta gagarumin littafi mai suna kyauta daga Allah.

(2). Ki tallafi rayuwata data tsunduma cikin kogon lubiyar soyayyarki, ki tausayawa zuciyar data shagala akan tsanananin soyayyarki, kada rintsi ko zugar masu hassada yasa ki gujeni ko kuma ki rage son da kike min.

(3). Inata neman wata kalma ɗaya wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta izuwa gareki cewa. Ke ta daban ce ke kyakkyawa ce, kin zarce duk sauran mata. Zuciyata da taki ba zasu taɓa rabuwa ba har abada. Ina sonki har cikin ƙalbina.

(4). So shine abinda ya dunƙule zuciyoyinmu waje ɗaya har muka tsinci kan mu a cikin soyayya, ina fatan ba zaki bari wani ɗan ƙaramin abu yazo ya raba tsakanin mu ba. Ke kamar gishiri ce a cikin rayuwata, idan na rasa ki zanyi rayuwa ne mara armashi. Ki huta Lafiya.

(5). Da akwai waɗansu tarin tsuntsaye da suke yini suna tattauna batutuwa akan irin matsayin dana baki a cikin zuciyata. Zan so kiji irin abinda suke cewa, domin kuwa a lokacin ne zaki gamsu kuma ki tabbatar da irin soyayyar da nake yi miki.

(6). Da akwai furanni marasa adadi cikin lambun masoya a faɗin wannan duniya. Da ace zan tsinko kowane fure na baki shi ki karɓa a hannunki, to hakan bai isa ya bayyanar da irin adadin yadda nake sonki ba. Kece murmushina, kuma kece farinciki na.

(7). Akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye mara adadi saboda ke, nasan zaki ce saboda me? hmm ni nasan ba zaki gane ba.

(8). Da akwai wasu lokuta da suke zuwa naji tamkar nayi fika-fikai na tashi sama. Kin kuwa san saboda menene? saboda motsawar sonki a cikin zuciyata da tsantar kauna a cikin matsanancin shauƙi a dukkan lokacin da naji muryarki ko na tuna dake.

(9). Ina fatan zaki amince mu rayu a tare da juna har abada. Inason ki!

(10). A duk ranar lokacin da dare yayi ki ɗaga kanki ki kalli sararin samaniya, za kiga wani tauraro yana saukowa izuwa gareki, karda kiyi mamakin meyasa haka ya faru? ki yarda dani hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa nima nayi hakan har takai ga na sameki. Hmm! ki huta lafiya.

Kalaman soyayya masu nishadantarwa section c

*A lokacin dana samu soyayyarki sai naji tamkar nine nafi kowa sa’a a faɗin duniya. A duk lokacin dana rintse idanuwa na saina hango ni tareda ke muna tafiya a bisa doron gajimare. Idan na kwanta bacci kuwa sai nayi mafarkin mun zama mata da miji. Ina matuƙar sonki tareda son kasancewa a tareda ke har abada. Ki huta lafiya.

*Sama cike take da taurari masu haske dake haske sararin duniya a cikin kowane dare. Amma haske mafi haskaka zuciya da yaye duhun zuciya, na ganshi ne a cikin idanuwanki. Ki kulamin da kanki.

*A koda yaushe ina tambayar kaina shin kuwa idan ba kai a wannan rayuwa to ina zan saka kaina inji sanyi, kaine wanda in na kalla nake samun farin ciki da annashuwa.


KALAMAN SOYAYYA MASU KWANTAR DA HANKALI

A wannan ɓangare munyi duk iya yinmu domin samar muku da dadadan kalamai wanda zasu kwantar da hankalin masoyanku, sai ka zaɓi wanda kaga zaifi maka amfani kayi amfani dashi.

Kalaman soyayya masu kwantar da hankali section a

1. Masoyiyata ina matuƙar gudun fushinki fiye da yanda nake gudun kamuwa da talauci ƙaunarki tabi duk wani sashe na jikina. Ina sonki har ƙarƙashin zuciyata kuma ina ji dake fiye da yadda nake son duk wani abu mai faranta min rai.          _______________________________

2. Kai alheri ne sannan ni'ima a cikin rayuwa ta kai wata ne da hasken sa ya haskake zuciyata ina jin daɗi idan na kalle ka doran ƙasa na cike da tsirrai sararin samaniya kuma na cike da taurari masu hasken ni'ima, ita kuma duniya na cike da halittu ita kuwa zuciyata na cike da tsantsar so da ƙaunarka.               ________________________

3. Kiyi sani cewa shi so wani abu ne mai kyau, kuma wani nutsattsen yanayi ne da mutum zai so ya damƙe. So shine yanayin da kansa ɗan-adam ya jishi a raye. Ina fata kin fahimci cewar komai wuya komai rintsi zan soki har ƙarshen rayuwata, saboda baki kasance budurwata kaɗai ba, ke ɗin amintacciyar aminiyata ce.                _____________________________

4. Amincin sarki maɗaukaki ya tabbata a gareki yake wacce tafi taurari da duk wani irin haske. Hmm ina fata dai ba fushi kike yi da ni ba ko?. Zan iya manta komai amma kiyi sani cewa bazan iya manta ki ba, haka kuma zan iya jure rashin komai a faɗin duniya amma ba zan iya jure rashinki ba, haƙiƙa daga jiya zuwa yau ina cikin ƙunci wanda baya misaltuwa, baƙin-ciki ya ziyarci zuciyata wanda har kawo izuwa yanzu banajin zan iya kula wani cikin walwala shin kinsan ko mene ya saka nake cikin wannan hali ba wani abu bane illa rashin jin muryarki da banyi ba da ɗan lokaci.                  ______________________________

5. Idan ya kasance wata yar tafiya ta kama ka, to idan har nace zan iya nayi ƙarya domin ni kaɗai nasan irin halin da nake shiga na rashin jindaɗin tafiyar ka.

_______________________________________

6. Zuciyata na ƙuna da tafasa har nakan ji tamkar zata fashe da kuka, kayi sani cewa, wannan saƙon da zuciyata ke sanar da kai bawai abune wanda idanu zasu iya gani amma ruhi mai ƙawa zuci zai iya fahimta. Shi dai hannu aikinsa rubutawa ba wai ina faɗa bane, bawai kuma don tsoro ko dan kaji daɗi ba Hmm kai jinin jikina ne.            ________________________________

7. Duk a lokacin daka haɗa yanaka-yanaka kayi gaba to nima ka sani cewa daga wannan lokacin zan tattara duk wata walwala tawa da annashuwa ta na ajiye su daga gefe kuma ajiyewar da baza su taɓa kusantowa inda nake ba.          _______________________________

Kalaman soyayya masu kwantar da hankali section b

1. A koda yaushe ina sanar da kai cewa banayin fushi da duk abinda ka aikata a gareni koda kuwa abin ya sani fushi to idan na tuna dashi sai dai ka ganni ni kaɗai ina murmushi kamar wadda aljanu suka shafa. Idan nayi kiranka bawai na kiraka bane don ka bar abinda kake yi ba, illa kawai na kiraka naji numfashin maigidana hakan na saka ni cikin alfahari da nutsuwa.         ___________________________

2. A koda yaushe inayi maka fatan ka kasance cikin farinciki sannan kuma ka huta lafiya. Nagode da kulawarka habibina.            ________________________________

3. Inaga a duk lokacin rabuwarmu bakya kaini shiga cikin kewa da zullumi, dama ance ba'a sanin muhimmancin mutum sosai sai a yayinda yayi nisa da kai. Haƙiƙa jiya na ƙara gaskata wannan jawabi na yan magana.

_____________________________________________

4. Domin nisan da nayi dake na yini ɗaya saida naji tamkar shekaru dubu nayi ganki ba, kin riga kin zama ni nima na zama ke kamar fatar jikina duk wanda ya raba ni dake to tamkar ya rabani da kyau na da kwarjini na haɗe da suturata gaba ɗaya.               ________________________________

5. Ke kin kasance garkuwa a gareni mai kareni daga abubuwa da yawa, hasken zuciyata farincikin raina, annashuwa da jindaɗi na. Ina sonki ina ƙaunarki, bazan iya nisa dake ba.             ________________________________

6. Bazan barki ba duk rintsi duk wuya a wannan rayuwa, sai dai idan ke kika barni, zuciyata kuwa bata fatan ko mafarkin hakan ballema a gaske. Inaso kiyi sani cewa soyayyarki tayi nisa cikin zuciyata.         ________________________________

7. Abu kamar wasa inata baki filayen zuciyata inaso na rasa kaina a garin yin hakan ta yadda bazan taɓa samuwa ba cikin sauƙi, da sannu-sannu dai inata miƙa rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kin zama abar ƙaunata hakan ko ya biyo bayan karamcin kine a gareni a yayin da nake ƙara kusantuwa dake.             ________________________________


KALAMAN SOYAYYA MASU SANYI

Sanyi dai yana nufin salama da ni'ima irinta soyayya ga masoya, idan Allah ya albarkaceka ko ya baki masoyi mai kaunarki wallahi kina ɗaya daga cikin masu babban rabo a wannan rayuwa domin kuwa kinada wanda kome ake ciki bazai watsar dake ba.

Kalaman soyayya masu sanyi section a

1. Duk ruhina ya fara bayyanawa zuciyata kedin ta daban ce ya masoyiyata kin zama abar ƙaunata kamar giza-gizai haka kika zamto inuwa a gareni kamar ruwan sama haka kika zamo kin jiƙani da farinciki, haka kuma kamar iska haka kika tafi da ilahirin tunanina kin sabunta ƙaddara ta hanyar samar da sabuwar safiya a wannan rayuwa tawa.

_______________________________

2. Da kai kawai nake so na ƙare rayuwata ya masoyiyata kin zama abar ƙaunata kada ki taɓa mantawa da cewa ni ina rayuwane kawai saboda ke. Ko ina zaki je ki tuna da hakan wato ina rayuwa ne kawai saboda ke a duk inda kike ina miki fatan alkhairi, wannan itace addu’ar da zuciyata keyi a kanki a koda wane lokaci.     ________________________________

3. Kyakkyawar alaƙar dake tsakaninmu mai amfani ce haka rayuwa take idan kina tare dani a duk lokacin da kika yi nesa dani rayuwata sai ta zame mun ba daɗi irin son da nake miki ta yaya zan iya bayyanashi, waɗannan idanuwan nawa tsawon dare suna tsayawa cir! kuma sunayin kuka duk da kasancewar ina tareda ke meyasa nake jin kewarki ne? na kasa fahimtar menene hakan.                 ________________________________

4. Yayinda kika iso bakin ƙofar zuciyata tofa daga wannan lokaci na sadaukar da rayuwata da sunanki, kuma na koyi yadda zan rayu dake masoyiyata ada ban taɓa koyon yadda zan rayu ba ba tare dake ba, masoyiyata waɗannan yabo ne na gaskiya nake miki da kyakkyawar zuciyata yayinda na sameki sai duniyata ta kawatu matuƙa.           ________________________________

5. A cikin dare ko da safiya inason jinka a kusa dani, ta yadda numfashi na tareda naka zasu gauraya, ta yadda zan dinga juyo sautin bugun zuciyoyinmu suna fita a tare.     ________________________________

6. Ina fata mu kasance a tare har abada. Ina son ka! duk mai shiga tsakanina da kai to shi ɗin magulmaci ne da zan ganshi, to tabbas da sai na tsone idanunsa.

______________________________________

7. Na baki sirrika na, ki adana su, ko kuma ki binne, ke kaɗai ce a ƙalbina har abada bazan manta da ke ba. Na fito wajen aiki hakan yana nufin munyi nesa da juna nasan kuwa zan kasance cikin kewa.    ________________________________

8. Amma inaso, ki sani cewa, duk inda nake, kuma a duk inda na shiga, ba zan daina tunaninki a matsayin ki na matata da nake matuƙar so da ƙauna ba. Ina nan tafe akan hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tuna cewa, bani da kamar ki ke kaɗai ce kuma ta musamman. Ina son ki.        ________________________________

Kalaman soyayya masu sanyi section b

1. Duk inda kika je kiyi sani cewa ina biye dake, ko da banzo a zahiri ba to kuwa zan-zo miki a cikin bacci, kema zaki bayyana a cikin mafarkina, mu kasance a tareda juna, cikin wani katafaren lambu mai cike da furanni mabambanta masu launi kala-kala daban daban. Begenki shine abun yina a kullum safiya da maraice. "       ________________________________

2. A lokuta da dama, kalmomi sukan ga-gari furtawa, domin na bayyana miki irin adadin yadda sonki yake ƙara mamaye zuciyata a kullum. Haka zalika bana fatan zuwan ranar da zan kasa wajen samo kalmomin da zan furta miki cewa ina sonki, Hmm! kada ki manta dani a rabon naman sallah. Barka da babbar sallah masoyiyata kuma abincin ruhina."         ________________________________

3. A yayinda dana fara ganinki, sai dana rintse idanuwana domin fahimtar cewa, shin a zahiri nake ganinki ko kuma kawai kin shigo mafarkina ne ta cikin tunani na. Lallai ke ɗin ta musamman ce, kina da wata baiwa wadda ba kowane zai gane hakan ba, daga ciki akwai ta zazzaƙar muryarki da tattausan murmushi. ina ƙaunarki"   ________________________________

4. Inason jimillar wasu abubuwa guda uku a rayuwata sune rana da wata sai kuma mafi soyuwa a gareni shine ke. Inason wata ne domin ya haskaka min dare, inason rana kuma domin ta haskaka min yini, Hmm ke kuwa ina sonki ne domin mu rayu tare har abada.        ________________________________

5. Ke kin kasance tauraruwa ce a cikin wannan duniya, haka kuma ke duniya ce ga wani tauraro, zanso ki amince mu rayu a tare cikin shauƙi da ƙaunar juna. Hmm! zan kuma zo na karɓi nawa goron sallar. Barka da babbar sallah. "        ________________________________

6. Farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a duk lokacin da naji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yayemin duk wata damuwata, bana kasancewa dai dai da shaƙar numfashi ba tareda tunaninka ba a cikin zuciyata, kaine ɗaya tilo dana damƙawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada, ina sonka habibina.        ________________________________

7. Nawan ko kasan cewa cikin kowace rana kyawunka daɗa ƙaruwa yake a cikin idanuwana? Tabbas bazan dakata daga begen kallon kyakkyawar surarka a zahiri da cikin zuciyata ba har sai sabuwar rana ta kama hasken idaniyata, hmm! kuma kada ka manta a goben ma sai wata goben. Ina sonka Nawaan "    ________________________________

8. Babu ko shakka furanni suna da ƙamshi, zuma kuma tana da zaƙi launin ciyawa kuwa kore ne sharr, amma ke babu wata kalma ko jimlar da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai nace ke kyakkyawa ce. Ina sonki nutsattsiyar nutsattsu.


KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA JIKI DA JIJIYOYIN

Idan kanason matarka ko budurwarka ko kina so mijinki ko saurayinki ta/ya samu nishaɗi ta/ya kuma san ka/ta yaba da irin madarar soyayyar da take/kake shayar da kai/ita, tura mata/masa saƙon kalamai na irin yadda kake/kike jin ƙaunarta/sa a zuciyarka/ki na ɗaya daga cikin hanyoyi masu sauƙi haka kuma masu tasiri wurin ƙara danƙon soyayyar taku. 

*Wai shin ada can tunanin me nakeyi wanda ba naka/ki ba ? 

*Idan kai/ke shirin fim ne/ce a rayuwa to da kuwa zanci gaba da kallonka/ki a matsayin wannan shirin fim ɗin har ƙarshen rayuwata. 

*Idan sonka/ki wani aiki ne, to da zanfi kowa cancantarsa, zanfi kowa maida hankali. A taƙaice zan iya aiwatar da aikin a kyauta ba sai an biyani ko taro ba. 

*A cikin dubban ko miliyoyin mutane, idanuna ke kaɗai suke nema. Kisani masoyiyata ke zara ce a cikin miliyoyin taurarin mata, kece tauraruwarsu kece ƴar autarsu, kuma kece kike haskaka su indai a cikin zuciyata ne. 

*Inna rungume ka/ki, da gasken gaske banason na sake/ki

*Haƙika lallai na taki sa'a dana samu kaina a cikin soyayyar babbar Ƙawata/ Abokina

*Ka/Kin san yadda nake kewar ka/ki a kowane sakan ɗin agogo a rayuwata ? 

*Murmushin ka/ki shine abu mafi burgewa dana taɓa gani a rayuwa

*Idan wata/ni sukace in siffanta ka/ki a kalmomi uku kacal, cewa zanyi "kayi/kinyi a rayuwa.. 

*Soyayyarki/ka gareni tayi hanin duk wani sukuni ba dare ba rana, akanki/ka nake yawaita tunani, ki/ka jani a sannu sannu, sassarfata ta samo asaline saboda nazarin ki/ka.. Idanu na sun gaza runtsawa matuƙar ba'a cikin marfinki/ka ba..

Kalaman soyayya masu dadi ga budurwa

1. Na sanya jarin da har yanzu nake samun ribarsa, amma babu asara. Asusun dana sanya jarin nawa bako wane asusu bane sai zuciyarki. 

2. Kinyi min miliyoyin ƙananan abubuwan da suka kawomin farin ciki a raina. Kinyi ruwa kinyi tsaki a cikin birnin zuciyata yake masoyiyar raina. 

3. Idan da ace zan iya baki abu guda ɗaya a rayuwa, dana baki damar ganin kanki a cikin idanuna. Hakan ne kaɗai zaisa ki gane ke ta musammance a gareni. 

4. Yanzu nasan cewa tatsuniya takan zamo gaske saboda ina dake.. 

5. A lokutan biyu kaɗai nakeson Kasancewa dake: yanzu da kuma har abada. A yayin duk da rana zata ɓullo akwai ka/ki a zuciyata, yayin da rana zata faɗi ka/kina cikin tunanina. Tiririn son ka/ki shike ɗumama ɗumin jikina.

6. Labarin soyayyata cikin kalmomi shida: "Bazan iya hasaso rayuwa babu ke/kai ba" 

7. Kece mahaɗin raina, kace babbar ƙawata. Me zanyi babu ke? Tunanin me zanyi wanda ba naki ba? Abinda kawai nakeso ki sani a cikin kalmomi uku kacal shine; INA SON KI! 

8. Ke kamar wata sassanyar iskar numfashi ce, kuma ke ɗin kamar hasken hudowar rana ce ta yau da kullum a cikin rayuwa. 

9. Zubar hawayenki indai na ɓacin raine to tamkar ɗigar dalma ne a ƙahon zuciyata. Ina son na zama dalilin kyakkyawan murmushinki, na yau da kullum. 

10. Ki taka ɗai ɗai kuma a sannu yake sarauniyar kyawawa, kiyi ƙasaitarki akan karagar mulkinki da kike mulka a cikin birnin zuciyata. 

Kalaman soyayya masu dadi zuwa ga Saurayi

1. Kinason mijinki yasan cewa ya shiga cikin zuciyarki yayi kane kane tunda sanyin safiya ? Tura masa saƙo na kalaman Soyayya na barkwanci wata hanya ce mai karfin gaske daza ta sashi nishaɗi.. 

2. Wai har sai yaushe zaka dena sani inta tunaninka a koda yaushe? Nauyin awon soyayyarka yafi tsaunin nan na kilmanjaro nauyi. Baka buƙatar yiwa soyayyarka ban ruwa domin ta riga ta girma, tayi ganyayyaki,  manyan reshina, haka kuma tayi fure tayi ƴaƴa. Baka buƙatar kiwata soyayyarka a cikin ruhina domin kuwa tayi ƙarfi ta tsaya da ƙafafunta. 

3. Idan babu abinda zai tabbata har abada, zan iya zama abadarka ? 

4. A koda yaushe kana narkar min da zuciya 

5. Bana iya banzatar dakai konayi ƙoƙarin yin hakan. 

6. Duk wani lokacin dana samu da babu kai a cikinsa ɓacin lokaci ne

7. Nagode, ako da yaushe kana sawa naji nafi kowace mace kyau a duniya 

8. Da kai nake shaƙar numfashi da kai nake sauke numfashi, a kowane daƙiƙa na rayuwa akwai ka a cikin tunani na.. Kai ne dalilin iya zancena na zuci kuma kaine dalilin da zancen zucin nawa ke fitowa fili kowama yaji.. 

9. Kai ne inuwata idan ana zabga rana, kai ne lema ta idan ana tsuga ruwan sama. Nan gaba idan na rungumeka, bazan sake kaba har abada...

10. Kai ne silar murmushina, kai ne silar dariya ta, kai ne dalilin kukan farin cikina kuma zuciyata bata da ƙarfin ayyanawa ko kuma hasaso nisanta da kai ko kuma rasa ka.. 

11. Na kasa samun matsaya tsakanin wannene yafi, tsakanin tashi daga barci kusa da kai ko kuma kwanciya barci tare da kai, kayi sauri kazo gida domin na sake kwatanta biyun. 

12. Kowane mutum akwai abinda yake ƙarfafa masa guiwar dazai tashi da safe ya fuskanci ƙalubalen rayuwa. Kaine ƙarfin guiwata. 

Daɗaɗan kalaman soyayya masu dadi idan suka shiga cikin birnin zuciyar masoyi sukan samu wani bigire mai yawa su kuma zauna daram. Tura masa/mata kalamai na soyayya masu sururutar haɗe da shagaltar da zuciyar masoyi kamar haka;

*Ya ma'abociyar/ma'abocin kyan fuska da kamala ki/ka buɗe min ƙofar zuciyarki/ka na shiga ciki na wataya.. 

*Ka/ki nasawa na mance yadda ake numfashi. Haka zalika kece/kai ne madubin dubawa.. 

*Kowa tara yake bai cika goma ba, amma kai/ke ka/kin kusa.. Abinda kaɗai nake buƙata a yanzu kai/ke ne/ce..

*Ina sonka/ki jiya amma nafi sonka/ki yau, kuma zan fi sonka/ki a gobe

*Na ƙagu na dawo gida domin nayi katari da kyakkyawar fuskarka/ki.. 

A wasu lokutan mafiya yawan kalamai na soyayya da suka fi ma'ana sune waɗannan kalaman masu bayyana tsantsar soyayya a cikin ƴar ƙaramar jimla. Ma'ana a cikin kalmomi kaɗan. A cikin wannan ƙananan jimlolin daza ka/ki karanta a ƙasa, zaku samu jin yadda ake sarrafa kalaman soyayya daga mutane ma'abota iya kalamai na soyayya:.

*Sace zuciyarka/ki shine laifin dazan mutu ina alfahari dashi. 

*Zama dakai/ke yafi komai daɗi, ka/ki na sawa naji zuciyata tana murmusawa

*Shin ka/kin san cewa nafi kowa sa'ar dacen abokin/yar zama ? 

Ina sonki/ka a kowane taku ɗaya na rayuwa ta.. 

Kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin na rufe wannan rubutu:.

_A wasu lokutan nakan tsinci kaina ina tunanin lokacin dana fara sanyaka a idanuna. Tun a wannan lokacin nasan na haɗu da mahaɗin zuciyata. Tun daga wannan lokacin, iya abinda nakeso a rayuwata shine kasancewa dakai. Duk yadda rayuwa tayi tsanani, duhu ya mamaye ni kallon fuskarka kaɗai, yana haskakani ya kuma mamaye duhun daya rufeni. Babu komai a cikin zuciyata sai kai, kai kaɗaine tare da tunaninka kuka taru kuka cika min zuciya. 

_Ina so kasan cewa babu wanda zai iya chanjaka ya ɗauke matsayin da kake dashi a zuciyata ya canja shi. Tunaninka daban ne a cikin zuciyata. Kallon cikin idanunka yana sanyaya ruhi na, begenka shine abincin zuciyata. 

_Gaba ɗayana ina cikin ramin so da ƙaunarki ne. Nakan farka daga baccina da tunaninki, haka kuma zanyi bacci domin ganinki a cikin mafarkina. Tun daga haɗuwata dake komai ya chanja. Haƙika nayi sa'ar faɗawa da zurfi cikin ramin ƙaunarki. Zan kuma ci gaba da ƙaunarki har abada. 

Shawara kyauta domin inganta soyayyarku

Bawa masoyinki/masoyiyarka dama yasan/tasan cewar shi/ita ɗin na/ta musamman ne/ce, yasan/tasan cewa shi/ita ɗin duniyarka/ki ne ta hanyar zama ki shirya masa ƴan gajerun kalmomi na soyayya. Ina mai tabbatar miki/maka saƙon ki/ka zai shiga cikin kahon zuciyarsa/ta, tamkar yadda kibiyar ajali ke barin cikin kwarinta zuwa ga inda maharbinta ya aike ta. 

_Muryarka/ki itace sauti mafi soyuwa a cikin raina

_Har zuwa yanzu, duk wani lokacin da muke tare da kai/ke, lokaci ne mai cike da nishaɗi abin tunawa, amma nai maka/miki alƙawari fiye da hakan zai faru matuƙar muna raye. 

_Daka/kin san yadda nake tsumayin zama da kai/ke da ka/kin fi fahimtar matsayinka/ki a zuciyata. 

_Baka/ki san yadda bugun zuciyata yake canjawa ba da zarar idanuwa suka hangeka/ki

_Ina son koda yaushe na ɗago kaina na kama ka/ki kana/kina kallona. 

_Ambaton sunanka/ki kaɗai yana kwantar min da hankali. 

*Daga lokacin dana haɗu da kai zuwa yanzu nayi kuka kaɗan, nayi murmushi nayi dariya sau babu adadi saboda kawai akwai ka ko nace ina da kai, rayuwata da kai a cikinta tafi kyautuwa 

*Kowace rana tare da kai wani kyakkyawan ƙari ne a cikin rayuwata. 

*Kai ɗin wata aljannar duniya tace, cikin ɗinbin farin ciki zanso na samu kaina da bacewa ɓat a cikin ta. 

*A duk lokacin da nayi tunanin cewa bazai yiwu na ƙara maka so akan wanda nake maka ba kai kuma sai ka tabbatar min da yiwuwar hakan. 

*Kai ba abokin zama bane kai ɗin abokin ruhi nane

*A kowace rana ina cigaba da zaɓar ka, kuma a kowace rana wannan zaɓin nawa yana ƙara zama mafi sauƙi a cikin zaɓukan raina. 

A ƙarshen wannan rubutu namu wannan gida mai albarka na hausaland.com.ng yana yiwa kowa fatan alkhairi a kullum da ko yaushe.

{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post