Kalmomin turanci da fassarar Hausa:
Wasu kalmomin koyon Turanci
Abacus- Abin ƙidayaThrift – Tanadi
Orphan – maraya
Organization – ƙungiya
Progress – cigaba
Sin – zunubi
Luck – sa’a
Mackintosh – rigar ruwa
Must – dole
Marvelous – mai ban mamaki
Origin – asali/mafari
Medium – matsakaici
Ostentation – Mai fariya/mai Alfahari
Imputation – Zargi
Incest – Auren Haram
Incorrect – Ba dai dai ba
Incurable – ciwon da ba magani
Decency – jin kunya
Indecency – Fitsara
Limit – iyaka
Latch – sakata
Dirt – ƙazanta
Wrapper – Zani
Jump – Tsalle
Decision – yanke hukunci/shawara
Tinuid – Mai tunzuri
Tomb – kabari
Gown – Babbar riga
Hamlet – ƙaramin ƙauye
Handcuff – Ankwa
Gain – Samu
Judge – hukunta
Kindred – Dangi
Loyal – Mai biyayya
Magician – mai sihiri
Miracle – Mu’ujiza/Abin Al’ajabi
Misdemeanor – Karamin laifi
mist – hazo
Moist – Danshi
Nature – yanayin mutum
Naughty – Hatsabibi
Reveal – Bayyanawa
Reward – Lada
Yadda zaka iya turanci
A yanayin yadda muke ciki yanzu a wannan rayuwa turanci ya zama hanyar sadarwa wacce ta kasance duk duniya ana amfani dashi, kuma koda kaɗance ya kamata ka iya wannan yare na masu jajayen kunnuwa. A shawarar da zan bayar shine gaskiya idan har kanason iya turanci tofa dolene saika cire kunya da girman kai musamman idan ya kasance ka girma.
Zaka iya shiga makarantar turanci wacce komai nasu suke yi da turanci ko kuma ka samu wani a anguwarku ya rinƙa dan koya maka a hankali zuwa wasu yan shekaru zaka sha mamaki wato yadda zaka bunƙasa maganarka da turanci. Sannan kuma kamar yadda ka samu wannan rubutu a wannan gida zaka iya cigaba da bincike akan yanar gizo domin koyon wasu kalmomin da jimloli.
Cockroach – kyankyaso
Committee – Komiti
Compare – kwatanta
Complain – yin kara
Complete – karasa
Conference – Taron shawara
Condition – halin xama
Defense – Tsaro
Definite – tabbatacce
Detection – Bincike
Delay – Jinkiri
Delegate – Wakili
Delicious – Mai dadin ci
Delight – Murna
Delirium – Magagi
Demand – Neman buƙata
Demolish – Rushewa
Demon – Shaiɗan
Demotion – Ci baya
Dentist – likitan haƙori
Depart – Tashi
Deputy – Mataimaki
Descend – Gangare
Describe – Misalta
Desert – Sahara
Design – Zane
Desire – Kwaɗayi, Muradi
Desist – Daina
Destiny – ƙaddara
Destitute – Musaki
Destroy – ɓatawa
Destruction – halakawa
Detach – bamɓarewa
Develop – cigaba
Device – ƙirƙirowa
Devil – Shaiɗan
Dexterity – Gwanintar hannu
Devote – Duhufa
Dice – Ya’yan ludo
Diamond – Lu’u Lu’u
Dictionary – ƙamus
Differ – Bambanta
Different – Daban daban
Difficulty – Wuya
Dig – Tona
Wasu daga hanyoyin iya hira da turanci
Cad – mutum mara ladabi
Calabash – kwarya, ƙoƙo
Caliph – kalifa
Callous – Mara imani ko tausayi
Canteen – wajen cin abinci
Careful – Mai kulawa
Careless – mara kula
Carpenter – kafinta
Carpet – Darduma
Cave – Kogo
Chameleon – Hawainiya
Change – dama
Change – canji
Charcoal – Gawayi
Chasm – Kwazazzabo
Chest – ƙirji
Civilian – farar hula
Clap – tafi
Clay – Yamɓu
Comet – Tauraruwa mai wusiya
Combine – Haɗawa
Diligence – Kwazo
Dim – Duhu
Direct – fuskanta
Director – Shugaba
Dirt – Dauɗa
Disaster – Masifa, Bala’i
Discard – Cirewa
Disdain – Raina
Discord – Saɓani
Disgust – Kyama
Dishonest – Rashin gaskiya
Dislike – Ƙinjini
Dismoy – Tsorata
Display – Gwaji, Nuni
Disapprove – Ƙin amincewa
Dissension – Jayayya
Distance – Nisa
Distribute – Rabawa.
Divide – Raba
Do – yi
Dock – Tashan jirgin ruwa
Document – Takardun shaida
Dodge – kaucewa
Doll – Ƴar tsana
Donkey – Jaki
Door – Ƙofa
Double – Riɓanyawa biyu
Doubt – Shakka
Dove – Kurciya
Dozen – Goma shabiyu
Drama – Wasan kwaikwayo
Draw – Zana
Drawer – Aljihun tebur
Dream – Mafarki.
Dried – Busashshe
Drink – Sha
Drum – Ganga.
Duck – Agwagwa
Dump – Bebe
Duplicate – Kwaikwayo
Dwarf – Wada, Gajere.
Exact – Sak
Fire – wuta
finish – gamawa
Confirm – Tabbatarwa
Congress – Taro
Connect – Jona
Consent – Yarda
Constitution – Tsarin mulki
Contest – Takara
Contract – Kwangila
Conversation – Hira, zance
Convict – Mai laifi
Crevice – Lungu, saƙo
Crime – laifi
Criminal – mai laifi
Critical – mai haɗari
Crocodile – kada
Crusade – Jihadi
Cudgel – kulki
Culture – Al’ada
Curse – La’ana
Cut – Yanka, sarewa
Culvert -kolbati.
Hurry – hanzarta
Equalize – daidaita
Intention – niyya
Sacrifice – Sadaukarwa
Scarcity – matsi/ƙaranci
Sense – hankali
Spendthrift – Almubazzari
Residence – wurin zama
Rumor – Jita-Jita
Rope – Igiya
Run – Gudu
Robust – Mai ƙarfi
Dais – Tukuba
Damage – Ɓarna
Damned – La’ananne
Damp – Danshi
Dance – Rawa
Dandruff – Amosanin ka
Danger – Haɗari
Dark – Mai Duhu
Darkness – Duhu
Date – Kwanan wata
Daughter – Ɗiya
Dawn – Alfijir
Day – Rana
Dead – Matacce
Deaf – Kurma
Dealer – Dillali
Death – Mutuwa
Deceit – Ha’inci
Deceive – Yaudara
Declare – Furta
Decorate – Yiwa ado
Decrease – Ragewa
Deduct – Zame
Deep – Mai zurfi
Dad – Baba
Daft – Taɓaɓɓe
Fassara Turanci English zuwa Hausa
*Does anyone here speak English? Akwai wanda yake jin turanci anan kuwa?
*Does she like the school? Shin tanason makarantar kuwa?
*Does this road go to market? Shin wannan hanyar ce ta zuwa kasuwa?
*Does she came yesterday? Shin tazo kuwa jiya?
*Don’t do that, kada Kayi haka.
*Don’t worry, kada ka damu.
*Don’t bother me, kada ka dame ni
*Don’t come near me, kada kazo kusa dani.
*Don’t take my phone, kada ki/ka ɗaukar min waya ta.
*Don’t touch my money, kada ka taɓamin kuɗina.
*Every week. Kowane sati.
*Everyday I get up at 5am, kowace rana ina tashi ƙarfe 5 na safe.
*Everyone knows it, kowa ya sani.
*Everything is ready, komai ya kammala.
*Excuse me, what did you said, Dan ji Mana, me kace ne?
Expiration date, lokacin lalacewar Abu.
*Fill it up, cika shi taf
*For how many days, zuwa kwanaki nawa?
*From time to time, daga lokaci zuwa lokaci.
*From here to there, daga nan zuwa can.
*Forget her, manta da ita.
*Do you study English? Kana karatun turanci?
*Do think it will rain today? Kana tunanin za’a iya yin ruwa yau?
*Do you think it is possible? Kana tunanin zai yiwu kuwa?
*Do you think you will be back by 2:30? Kana tunanin zaka iya dawowa wajan karfe 2:30 kuwa?
*Do you understand? Ka fahimta?
*Do you want me to come and pick you up? Kana son nazo na dauke ka ne? (A abin hawa).
*Do you want to come with me? Kanason ka tawo tare da ni?
*Do you want go with me? Kana son/kina son ki/ka tafi tare dani?
I will pray hard, sanyi addu’a sosai..
I will work hard,, zanyi aiki tukuru..
I will study hard, zanyi karatu sosai..
I will make a pilgrimage this year,, zanyi aikin hajji wannan shekarar..
I will pay for you, zan biya ma kudin..
I will make you proud,, zan sanya ka alfahari..
I will make you happy, zan sanya ka farin ciki..
I will complain to him about the problem, zan masa korafi a kan matsalar.
I will find a solution, zan nemo mafita.
I will accompany you, zan raka ka.
I will go and visit the patient, zan je na ziyarci mara lafiyar.
I will deliver the message,, zan isar da saƙon.
I will extend your greetings to him, zan isar da gaisuwarka gare shi.
I will stop here, zan tsaya a nan.
Let me tell you the truth,, Bari na faɗa maka gaskiya..
Let me show the visitors in, Bari na shigo da baƙin ciki.
Let me go and do the washing-up, bari na je nayi wanke-wanke.
Let me go and do the cooking, bari naje nayi girkin.
Let me go and do the ironing, bari naje nayi gugar.
Let me go and do the washing, bari naje nayi wanki..
Let me contact them,, bari na tuntuɓe su.
Let me discuss with you, bari na tattauna da kai..
Let me go and apologize to him, bari naje na nemi gafararsa.
Stop blaming me, daina ganin laifina.
Stop laughing at me, daina yimin dariya..
Stop flattering me,, daina kwarzanta ni..
Stop telling lies, daina faɗin ƙarya..
Stop insulting me, daina zagina..
Stop talking rubbish, daina maganar banza.
Keep learning, ci gaba da koyo.
Keep trying, ci gaba da ƙoƙari.
Keep moving, ci gaba da tafiya.
Keep practicing, ci gaba da gwadawa.
Don’t interrupt me, kar ka katseni.
Don’t rely on me, kar ka dogara da ni.
Don’t insult me, kar ka zage ni.
Don’t deceive me,, kar ka yaudare ni.
Don’t be rude to me, kar kayi min rashin kunya.
Don’t approach him now, kar ka tunkare shi yanzu.
Don’t make me angry, kar ka fusata ni.
Don’t be angry with me,, kar ka yi fushi da ni.
Don’t be afraid of speaking english, karka ji tsoron yin turanci.
I want to buy something for you, ina so na siya maka wani wani abu.
*I want to give you a gift, ina so na baka kyauta.
*I want to show you something, inason na nuna maka wani abu.
*I was about to leave the restaurant when my friends arrived, na kusa na bar gidan cin abincin a yayin da abokai na suka iso.
*I was going to library, zanje ɗakin karatu ne.
*I went to the supermarket, nace shagon siyayya ne.
*I wish I had another one, naso ace ina da wani.
*If you need my help, please let me know, idan kina bukatar taimako na, ki sanar dani.
*I’ll call back later, zan kirawo daga baya.
*I’ll call you on Friday, zan kira ka ranar juma’a.
*I’ll call you when I leave, zan kira ka yayin dana tafi.
*I’ll come back later, zan dawo nan gaba.
*I’ll give you a call, zan kira ka.
*I’ll pay for dinner, zan biya kudin abincin daren.
*I’ll pay for the ticket, zan biya kuɗin tikitin.
*I’ll pay, Zan biya.
*I’ll take it, zan ɗauka
*I’ll take that one also, zan ɗauki wancan ma kuma.
*I’ll talk to you soon, zanyi magana da kai nan bada jimawa ba.
*I’ll tell him you called, Zan faɗa masa ka kira.
*I'll teach you, zan koya muku.
Turanci da Hausa mai sauki
*I’m 26 years old, Ni ɗan shekara 26 ne.
*I’m 32, ina da shekara 32
*I’m 61, Ina da shekara 61.
*I’m a beginner, ni ɗan koyo ne.
*I’m a teacher, Ni malami ne.
*I’m a student, Ni ɗalibi ne.
*I’m Nigerian, ni ɗan Najeriya ne.
*I’m cleaning my room, ina gyara ɗakina ne.
*I’m Cold, ina fama da mura.
*I’m coming right now, ina zuwa yanzu haka.
*I’m coming to pick you up, zanzo na ɗauke ki yanzu haka.
*I’m fine, and you? Ina lafiya kefa.
*I’m from kano and you, Ni ɗan kano ne kefa/kaifa?
*I’m full, na ƙoshi.
*I’m getting ready to go out, na shirya fita waje.
*I’m going to kano next week, zanje kano wani satin.
*I’m going to bed, Zan je na kwanta.
*I’m going to have a dinner, zanje naci abincin dare.
*I’m good, ina lafiya.
*I’m happy, ina cikin farin ciki.
*I’m hungry, Ina jin yinwu.
*I’m just looking, kawai ina nema ne.
*I’m married, ina da aure.
*I’m not afraid, bana jin tsoro.
*I’m not married, bani da aure.
*I’m not going, bazan tafi ba.
*I’m leaving now, zan tafi yanzu.
Who are you? Waye kai?
Who are you looking for? Wa kake nema?
Who are they, su waye su?
Who is she? Wace ita?
Who is that? Waye wancan?
Who sent this letter? Waye ya turo da wannan wasiƙar?
Who taught you that? Waye ya koya maka haka?
Who taught you? Waye ya koya maka?
Who was your teacher? Waye ya kasance malamin ka?
Who won? Waye yayi nasara?
Who would you like to speak to? Da waye kake son kayi magana?
Who’s calling? Waye yake kira?
Who’s that man over there? Waye wancan mutumin da yake tsaye a can?
Whose book is that? Littafin waye wancan?
Why are you laughing? Me yasa kake dariya?
Why aren’t you going? Me yasa baka tafi ba?
Why did you do that? Meyasa kayi haka?
Why did you say that? Meyasa kace haka?
Will you hand me a towel please? Zaka iya muƙomin shawul?
Will you put this in the car for me? Zaka iya saka min wannan a cikin mota?
Will you remind me? Zaka tunamin?
Will you take me home? Zaka kaini gida?
Would you ask him to come here? Zaka iya tambayarsa yazo nan?
Where have you been for a long time?
Ina ka shiga ne kwana biyu?
He helped us to do this assignment,
Ya taimake mu wajan yin wannan aikin.
She will see them tomorrow,
Zata gansu gobe.
I asked her to come and see me,
Na tambayeta tazo ta ganni.
They played a football game and we beat them,
Sunyi wasan kwallon kafa damu kuma mun ci su.
I taught you, na koyar da kai.
He saw me, ya ganni.
We know her, mun san ta.
She thanked me, tagode min.
He threw it, ya jefar.
He broke the window, ya karya taga.
They blamed him, sun zarge shi
Why did you go there, meyasa kaje can?.
Her kindness is beyond compare,
Kirkinta ya wuce a kwatanta
I’m sick of your behaviour,
Halayyarka tana damuna.
I meet her gaze, mun hadu ido da ido.
I was taken unawares, an shammace ni.
I will keep a close eye on him,
Zan sa ido sosai a kansa.
I’m no Match for you at football,
Ni ba sa’anka bane a kwallon ƙafa.
She gave me the money on her own accord,
Ta bani kuɗin don ra’ayin kanta.
Sit down and make yourself at home,
Zauna ka saki jikin ka.
I will part company with aminu,
Zan daina mu’amala da aminu.
Identify yourself, yi bayanin kanka.
Can I borrow your phone, zan iya aran wayarka?
Why you do you come late?
Meyasa kazo a makare.
What do you expect? Me kake tsammani.
She request me to help her,
Ta roke ni na taimake ta.
She followed my instruction,
Tabi umarni na.
She disgrace him, ta wulaƙanta shi.
She asked me for money,
Ta roƙe ni kuɗi.
I can’t hear you, bana iya jinka.
I don’t feel well, bana jin daɗi.
I don’t have a girlfriend, bani da budurwa.
I don’t have any money, bani da ko sisi.
I don’t have enough money, bani da ishashshen kuɗi.
I don’t know, ban sani ba.
I don’t like him, bana ƙaunar sa.
I still have a lot of things to buy, har yanzu ina da abubuwan siya da yawa.
I still haven’t decided, har yanzu ban yanke shawara ba.
I think I need to see a doctor, ina tunanin ina buƙatar ganin likita.
I think so, ina tunanin haka.
I think those shoes are very good looking,, ina tunanin waɗancan takalman suna da matuƙar kyan gani.
I think you have too many clothes, ina tunanin kana da kaya masu yawa.
I thought the clothes were cheaper, na zaci kayan sun kasance masu sauƙi.
I trust you, na aminta da kai.
I need to change clothes, ina buƙatar canza kaya.
I need to go home,, ina buƙatar tafiya gida.
I need to go now, Ina buƙatar tafiya yanzu.
I only have 500 naira, naira ɗari biyar ce kawai dani.
I speak three language, ina ji/magana da yare uku.
I’m coming to pick you up, ina nan zuwa na ɗauke ka (a abin hawa).
I’m fine and you, ina lafiya kaifa?
I’m full/I’m full up, na ƙoshi.
I’m getting ready to go out, ina yin shirin fita waje.
I’m from kano, ni ɗan kano ne/daga kano nake.
I’m going to bed, zan tafi na kwanta.
She wants to know when you are coming, tana so ta san yaushe zaka zo.
She is going with me tomorrow, zata tafi tare dani gobe.
She is older than me, ta girme ni.
She’s pretty, kyakykyawa ce ita.
Should I wait? Ya kamata najira kuwa?
Everything went according to plan, Komai ya tafi kamar yadda aka tsara.
She will pass the exam in all likelihood, zataci jarrabawar bisa ga dukkan alamu.
He can’t barely write his name, da kyar zai iya rubuta sunan sa.
Don’t you dare come out in the rain, kar ka kuskura ka fito a cikin ruwa.
Da fatan an karu da kalmomin turanci da kuma jimlolin turanci tare da fassarar su!
{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}