Suwaye iyayen Ummi Rahab

Suwaye iyayen Ummi Rahab

Nidai nasan cewa babu wani ɗan-adam daya faɗo daga sama, anata maganar suwaye iyayen Ummi Rahab, yau dai munyi bincike mun samo bayani dai dai gwargwado.

Suwaye iyayen Ummi Rahab

Sakamakon dalilai da yawa al'umma suna ganin cewa Jarumin kannywood Adam A Zango shine mahaifin jaruma ummi, amma ganawarsa da gidajen talabijin da mujallu jarumin ya fito ya musanta wannan batu dake yawo a tsakanin mutane, sai dai kuma har izuwa yanzu babu wani rahoto da muka samu na ainahin iyayen jarumar.

Rahoton Neptune Prime ya ruwaito cewa, akto Adam A Zango bashi da wata dangantaka ta uba ko yan'uwantaka da ita, inda yace jarumin Adam ya dauko ta daga wajen wata sananniyar jarumar fina-finan kannywood wadda bai bayyana sunanta ba. 

Makallata fina-finan Hausa na kannywood dai sun cigaba da matsin lamba ga hukumar MOPPAN domin ta kira Adam a Zango da Ummi rahab domin su yiwa duniya bayanin ainahin abinda ke tsakaninsu. 

Sai dai kuma bayan mun zurfafa bincike, munyi nasarar samo wasu hotuna dake da alaƙa da ita jarumar wato ummi rahab, wannan tambaya, ta suwaye iyayen ummi rahab zamu iya amsata ne kawai da wannan hotuna dake ƙasa, wanda mai karatu zai fuskanci cewa na cikin hotunan larabawa ne, ko kuma muce mahaifiyarta kamar bakar fata amma mahaifin balarabe ne. To koma dai menene Allah yafi kowa sanin komai kuma shiya barwa kansa. A yanzu haka dai yarinya na rayuwa mijinta wato lilin baba, Allah ya basu zaman lafiya.

Suwaye iyayen Ummi Rahab

Wacece Ummi Rahab

An haifi jarumar shirya fina-finan hausa Ummi Rahab a ranar bakwai 7 ga watan Afrilun shekarar dubu biyu da uku 2003, a jihar Kadunan Najeriya. Tayi karatu a matakin Firamare harma dana Sakandare a jiharsu ta Kaduna.

Yadda Ummi Rahab ta shiga Kannywood

Saboda muhimmanacin shakuwa da kuma kauna da take tsakanin Ummi Rahab da wata fitacciyar jarumar shirya fina-finai, anan jarumin kannywood wato Adam A Zango, ya samo Ummi harta soma fitowa a fina-finai, shiyasa har ya zuwa yanzu da nake wannan batu wasu basu aminta cewa Ummi Rahab ba diyar Adam A Zango bace, tun bayan fitowarta a cikin shirin wasan kwaikwayo na “Ummi” tareda Jamila Nagudu tun lokacin Ummi Rahab tana ƙaramar yarinya.

Dawowar jaruma ummi rahab kannywood:

Wasan kwaikwayo na 'Ummi' na ɗaya daga cikin shirye-shiryen da jarumar ta fara fitowa, tun bayan shi kuma tayi sanyi, ba'a sake jin ɗuriyarta ba sai a yan kwanakin nan, wato lokacin da gama cika budurwa.

Adam a Zango ya sake dawowa da jarumar harkar wasan kwaikwayo, inda ya sanyata a cikin shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango na “Farin Wata Sha Kallo” wanda hakan ya sake daukakata a cikin masana’antar ta kannywood. 

Auren Ummi Rahab da Lilin Baba:

Lilin Baba fitaccen mawaƙi ne, kuma bama a masana'antar shirya finafinai ba, a'a mawaki dake waƙa ta salo daban daban kamar hip hop da dai sauransu, haka zalika ta fannin wakokin nanaye ba'a barshi a baya ba, domin nan ma ya taka rawar gani. Ƙulluwar soyayya ta shiga tsakanib Lilin baba da jaruma ummi rahab, har takai izuwa yanzu da nake maka wannan batu su ɗin ma'aurata ne. Da fatan wannan rubutu akan suwaye iyayen ummi rahab ya fitar da kai daga kokwanto akan jarumar, wato tanada iyayenta kuma ita mutuniyar kirki ce, tunda ba'a taɓa samun wani aibu nata daga masana'antar ta kannywood ba.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post