Shigar ciki nasa ciwon mara

Shin shigar ciki nasa ciwon mara ?

Yau gareka gobe ga ɗan uwanka, bayanin shin shigar ciki nasa ciwon mara ?. A yau shine abinda zamu tattauna a wannan dandali namu.

Shigar ciki nasa ciwon mara

Samun ciwon mara ga mace mai ciki abu ne wanda aka riga aka saba gani a mata masu juna biyu, kuma ba wani abun kai ruwa bane, sai dai kuma wasu lokutan yakan iya kasancewa da buƙatar a bincika, dalilin da yasa nace zaifi a bincika shine zai iya zama kuma ciwon marar mai juna biyun na rashin lafiya ne. Hajiya idan ke uwargida ce wato kinsha haihuwa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, to nasan kinsan meke faruwa dake idan kinada juna biyu, kinga kenan kinada sanin kanki fiye da kowa. Amma normally a likitance ana samun ciwon mara ga mace mai ciki, kuma ba wani abun matsala bane.

Amma idan har ya kasance ciwon marar ya ɗauki lokaci, wato kin daɗe kina yinsa misali kamar awa ɗaya kina yinsa kuma ke ba naƙuda ba, to a gaskiya akwai buƙatar aga likita nan take. Yayinda kike wannan ciwon mara abinda ya kamata kiyi shine ki canja yanda kike a kwance ko a zaune, idan zai yiwu ma ki ɗan taka a tsakar gidanki, sai kuma ki samu waje ki huta to in Allah ya yarda tusa zata iya zuwa miki wanda hakan zai baki sauƙi.

Jerin ciwon marar mai ciki wanda bana matsala bane.

1. Ɗan ƙaramin ciwon ciki ko ciwon ƙugu

2. Cushewar ciki 

1. Ɗan ƙaramin ciwon ciki ko ciwon ƙugu:

A matsayinki name ciki dama dole ne a sameki da yawan gajiya dama wasu abubuwa masu kama da haka, haka zalika ta ɓangaren yin ciwon ciki wanda bai taka kara ya karya ba, bashi da wata matsala ga lafiyarki da kuma da jaririnki.

2. Cushewar ciki:

Shima samun ciwon mara sakamakon rashin markaɗuwar abinci da wuri ga mai juna biyu ba matsala bace ta tayar da hankali, ɗan lokaci kawai za'a samu zaki samu sauƙi koda kuwa baki sha magani ba. Amma zaifi kyau idan da maganin kuma likita ya bada damar shan irin magani to sai kiyi amfani dashi.

A maza a tuntuɓi likita ko ungozoma idan aka samu ɗaya daga abubuwan da zamu lissafa a ƙasa:

1. Zubar jini

2. Fitar ko wane abu daga gaban mace wanda baki saba ganinsa ba

3. Ciwon ƙugu na lokaci mai tsayi kamar awa biyu ko sama da haka.

4. Jin zafi mai raɗaɗi yayinda kike fitsari

5. Jin ciwon jiki dana mara wanda ya haura mintuna sittin 60

Abubuwan da ka iya kawo mugun ciwon mara ga mai ciki:

1. Juna biyu a bayan mahaifa

2. Ɓarin ciki (Allah ya kiyaye)

3. Ciwon haƙarƙari

4. Haihuwar bakwaini 

5. Kasa renon ciki a mahaifa

6. Ciwon hanyar mafitsara

1. Juna biyu a bayan mahaifa:

Samun ciki a bayan yana ɗaya daga cikin abubuwan dake kawo ciwon mara mai matsala, hakan yana faruwa sakamakon rashin zaman tsokar halitta ta jariri a cikin mahaifar uwa, to idan har aka samu haka to da buƙatar ayi tiyata ko a samu magani daga wajen likita.

Alamominsa suna farawa tsakanin sati huɗu zuwa sati na sha biyu ga mai ciki. sune kamar:

            1. zubar jini

 2. jin zafi ko ciwo a kafaɗar mai ciki

            3. Zafi yayin yin fitsari

Cikakken bayani akan juna biyu a bayan mahaifa

2. Ɓarin ciki:

Ɓarin ciki shine zubar da ciki ba tareda ya kai lokacin aihuwa ba, hakan na faruwa kafin mako 24 da ɗaukar ga mahaifiya, alamominsa sun haɗa da:

             1. Zubar jini

             2. Ciwon mara mai zafi

3. Ciwon haƙarƙari:

Yawan jin ciwon haƙarƙari ga mace mai juna biyu ba sabon abu bane amma shima idan yayi yawa tofa akwai matsala, wannan ciwo na haƙarƙari na faruwa ne sakamakon girman da jariri keyi a jikinki. Haka zalika ciwon haƙarƙari na iya kawo rasa abinda ke cikin mahaifa wato zai iya zuwa babu rai. 

Manyan alamusa ciwon haƙarƙari mai matsala suna haka;

              1. Yawan ciwon kai

   2. Gani hazo-hazo (rashin gani sosai)

 3. Kumburin tafin ƙafa, hannu ko fuska

4. Haihuwar bakwaini:

Bakwaini kalma ce ta hausa dake nufin jaririn da aka haifa lokacin haihuwarsa baiyi ba, idan har kina mako kamar wanda bai kai talatin da bakwai da juna biyu kuma kina yawan samun ciwon mara mai zafi, to ki tuntuɓi likita ko ungozoma saboda nada nasaba da yiwuwar haihuwar bakwaini.

5. Kasa renon ciki:

Kasa riƙe juna biyu ga mahaifiya, hakan na faruwa sakamakon rashin ƙarfin bangon mahaifa wanda ke riƙe jariri har izuwa girmansa, wanda hakan zai iya kawo yawan fitar jini da ciwon mara mai zafi, idan kika ga wani abu mai kama da haka ki tuntuɓi likita.

6. Ciwon hanyar mafitsara:

Eh kwaraikuwa shigar ciki nasa ciwon mara, musamman sakamakon ciwon mara ga uwa zata iya fuskanta lokacin data ɗauki ciki, yanda zaki gane ciwon hanyar mafitsara shine yawan jin zafi lokacin da kike fitsari.


{getButton} $text={JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL} {getButton} $text={JOIN OUR WHATSAPP CHANNEL}


Recent Post Next Post