Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano ta ce ta fara karbar biyan kudin makaranta a cikin tsarin cryptocurrency

 Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano ta ce ta fara karbar biyan kudin makaranta a cikin tsarin cryptocurrency
Wata makaranta mai zaman kanta a jihar Kano, New Oxford Science Academy, Chiranchi, ta ce ta fara karbar biyan kudin makaranta a cikin tsarin cryptocurrency.


Shugaban makarantar, Sabi’u Musa-Haruna, ya shaida wa manema labarai haka a ranar Alhamis.


A cewarsa, an yanke shawarar ne bayan tuntubar iyaye da suka yi.


Mista Haruna ya kara da cewa an yanke shawarar ne domin a samu saukin biyan kudin makarantar.


“Mun yanke shawarar karɓar cryptocurrency a matsayin kuɗin makaranta saboda duniya a yau tana karkata zuwa ga tsarin.


"Mun yi imanin wata rana kuɗin dijital za su sami karɓuwa fiye da kuɗin takarda," in ji shi.


Mista Haruna ya kara da cewa kasashe kamar El-Salvador da Tanzaniya tuni suna karbar cryptocurrency a makarantunsu.


Don haka, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta rungumar tsarin tare da daidaita shi.

Post a Comment

0 Comments