Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan ikirarin Sheikh Ahmad Gumi

Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan ikirarin da Sheikh Ahmad GumiRundunar Sojin Najeriya ta mayar da martani kan ikirarin da Sheikh Ahmad Gumi ya yi cewa sojojin Najeriyar na hada baki da ‘yan fashi da suka aikata manyan laifuka da munanan ayyuka a fadin kasar.


Malamin addinin Islama ya yi zargin ne a lokacin da yake gabatar da shi a shirin safe na TV na ARISE ranar Laraba.


Zargin Gumi : Fashi da Makami Kasuwanci Da Hadin kan Jami'an Tsaro - Gumi

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, Daraktan hulda da jama’a na rundunar Soji a cikin wata sanarwa ya yi Allah wadai da zargin na Gumi.


Nwachukwu ya ce rundunar sojan ta gudanar da aikinta na kundin tsarin mulki a mafi kwarewar aiki daidai da kyawawan halaye na duniya na bin dokokin aiki da kuma kare hakkin dan adam. 


Post a Comment

0 Comments