Dakatar da Twitter: Idan Kayi Tunanin Kana cutar damu Ta hanyar Amfani da VPN, Kana cutar da kanka - Lai Mohammed

Dakatar da Twitter: Idan Kayi Tunanin Kana cutar damu Ta hanyar Amfani da VPN, Kana cutar da kanka - Lai MohammedDakatar da Twitter: Idan Kayi Tunanin Kana cutar damu Ta hanyar Amfani da VPN, Kana cutar da kanka - Lai Mohammed


Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bukaci wadanda ke amfani da VPN din da suka tsallake dokar da aka hana amfani da Twitter a kasar da su daina yin hakan, IgbereTV ta ruwaito.


Lai Mohammed wanda ya bayyana a gaban ‘yan majalisar yayin sauraren bincike kan hana ayyukan Twitter a kasar, ya ce amfani da VPN yana fallasa bayanan da suka hada da asusun bankin su.


Ministan ya kuma ce wadanda suke tunanin suna cutar da shi ta hanyar amfani da VPN, suna cutar kansu ne kawai.


Lai Mohammed ya kuma bayyana cewa haramcin ya samar da kyakkyawar dama ga "'yan Najeriya masu basira su kuma duba yadda za su iya samun manhajar da za ta maye gurbin Twitter da sauran dandalin sada zumunta

Post a Comment

0 Comments